Chapter 95
Chapter 95
jakkunkuna atamfofi masu d'auke da hotanshi da amaran sa , duk Wanda yazo gurin ya samu kuma yayi guziri. Bakwai shaura aka tashi saboda lokacin sallahr magariba ne. Kuma bayan sallah Isha'i Mama tace Ko wacce za'a kaita dakin ta. https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿106* Hannuwan ta ya zubawa ido kurr!! Sun sha uban Jan lalle wanda yayi jajazur har ya fara yin b'aki, sosai abun ya burge shi kuma ya bashi sha'awa,, nata duk ya fi tafiya da imaninsa, nasu Halisa bak'i ne, irin wanda ake zanawa shima yayi kyau babu laifi, kowa da kalar nashi,Cikin nutsuwa ta had'a plate uku kowa da nashi,, ta mik'a masa nashi tana fad'in "Bisimillah" Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe ido yace"Ke ina naki plate d'in, kin had'awa kowa nashi" babu yabo babu fallasa tace"Na ci abunci kafin na futo,, kai tsaye yace"Ko kinci dole kici na nan, ka'ida tace, wannan" Cikin mamaki ta kalle shi, ganin yanda ya b'ata fuska yasa ta fara zuba abuncin domin bata son ayi ta Jan magana,,Shiru gurin yayi, sai motsin cokola, satar kallonsa take yanda yake cin abunci kamar baya so,, ita kanta taunar sa ma abun kallo ne, Halisa kanta ya k'ara girma ganin yanda yake kula da ita domin shine ma ya tsiyaya mata ruwa,, ya mik'a mata lokacin da ta k'ware ganin, yana sanya Balaraba aiki yasa suka kara mike kafa suna ganin sun fita daraja a gurin shi kuma yasan su dama basu saba da aikin wahala ba,, shine ya fara mik'ewa daga gurin,, ganin ya tashi yasa ta mike da sauri ta gudu part d'inta... To Azima ma da ta kammala mik'ewa tayi ta wuce part din ta, aka bar Halisa tunda itace take da miji a hannu jiya da yau. ******************** ******************** Tsito da Waziri ne zaune cikin duhu,, Aljani Mak'asudu ya hauro kan Tsito nan suka fara magana da Waziri,, yana fad'a masa buk'atun sa, Mak'asudu yace"Akwai alkwarina a kanka na k'afa biyu kar kace na manta da wannan alk'awarin ina sane dashi, kuma sai na bi jinina,, wannan buk'ata kuma da kawo mana, zata biya amma da sharad'i idan ka kuskura ka kauce sharad'in da muka gindaya maka to sharrin zai koma kanka kaji!!!!!!! Ko"!!!!!!!? Waziri yace"Arne ya dafa maka ai duk sharad'in da kuka gindaya min ina me tabbatar maka da cewar zan bishi bazan kauce ba" Mak'asudu yasa dariya yana fad'in"Shikkenan ni zan jirge!! Yanzu amma zan Sanar da Tsito duk sharad'inmu sai ya fad'a maka" Waziri yace"A sauka lafiya Mak'asudu me mukulin mulki mak'asudu d'an gidan K'azaza gaba salamun baya salamun Ubana"" Tsito ya dunga wata irin katantanwa a tsakiyar d'akin yana wani irin ihu!!!!!! D'if dakin yayi shiru kamar anyi ruwa an d'auke. Wajan minti goma Tsito ya dawo dai-dai cikin duhu ya kalli Waziri yace"Da alama d'azu muna magana da kai Mak'asudu ya hauro ko"? Waziri ya gyad'a kai yace"Akwai sak'on da yace zai fada maka ka fada min" Shiru Tsito yayi yana sauraron Mak'usudu sai gyad'a kai yake alamun yana sauroro,, bayan ya gama sauraron Mak'asud'u ya kalli Waziri yana fad'in"Yace"Mu nemo bak'ar kulb'a da bak'ar kunama sai bak'in b'era dunka sai tsohon kadan gare Wanda ya soma sab'a saboda tsufa, duk a yanka su a cire musu fatar jikinsu,, a shanya ta bushe, sai ka kafa kusa a d'akin ka, duk ka kafe fatocin bango d'aya ka samu Jan yanki kasa a tsakiya, bayan nan kuma hanjin su,, a had'a shi guri guda a sanya su su bushe a dake lukwi sai a zuba masa a abunci, da iziinsa sai ya mutu idan bai mutu ba to zai rasa wani b'angare na jikinsa, sannan in ka kuskura mutum ko guda ne, ya shiga dakin Da ka kafe fatocin nan to abun zai dawo kanka,,sai magana ta k'arshe yace"Ka tafi bakin kogi da k'aton rago me tozali ka yanka masa zai shanye jinin" Waziri yace"Duk za'ayi da izininsa mutukar bukatar zata biya, yanzu yanda za'ayi na samu wad'annan dabbobin shine abun dubawa" Tsito yace"Wannan babu matsala gobe sai ka futa dani a mota ni zan samo maka,, sai dai ka ware min lada na" Waziri yace"Duk kar ka damu zan maka kyauta ta ban mamaki in zaka tafi" Nan sukayi sallama Waziri ya futa yana godiya ga Mak'asudu. ************************* ************************* Kwanan Sallau Uku a asibiti yace ga garin ku nan, Lantana ta dunga kuka kamar ranta zai futa,, Uwa! Ma duk da ya sake ta ta koko da mutuwar Sallau,, Shamsiyya kuwa tun sanda ta dawo daga gidan Arrama ta kwanta ciwo kariris,, Amai da zazzab'i duk ta rame ta jeme sai uban zubar da miyau da takeyi,, jama'a 'yan zaman makoki dayawa duk San fahimci ciki ne da ita Uwa! Ta gane da sauran mutan gidan rudanin mutuwa ya hanasu nuna b'acin ransu domin hausawa nacewa wani tashin hankalin yafi wani,,, Lokacin da Balaraba taji mutuwar Sallau kuka ta dungayi sosai, Mama tai ta rarrashin ta, tare suka tafi Da ita da du Halisa Madabo ma taje,, Sarki kuwa dashi akayi jana'izar Sallau, unguwar ta d'auka wanda ma bai yi niyyar zama gurin mutuwar ba dalilin zaman Sarki! A gurin ya zauna,, ya sa aka kafa rumfuna sosai mutane suka zo suna kwasar girgi harda wadanda suka futa kasuwa, sai su dawo domin su kwashi abuncin gidan mutuwa, kullum sai sun zo har a kayi sadakar uku,, Balaraba suka dawo gida cikin jamami,, tayi mamaki da har aka share zaman makoki bata ga Iro da Mabaruka ba, har dai ta gaza hakuri ta tambayi Iya ina suke, sai tace"Mabaruka dai tafi sati hudu rabon ta da gida, shi ko Iro tun kafin ki bar gidanan aka neme shi aka rasa, tace"Shamsiyya fa"? Iya ta girgiza kai tana goge kwalla tace"Tana cikin daki ta d'auko abun kunya shiyasa take buyarwa jama'a" Balaraba ta dunga share hawaye tana tausayawa rayuwar su,, Shamsiyya kuwa tana jin ance ga Balaraba tazo zata dunga lekowa tana taga tana kallonta tana fad'in ina ma itace. ************************* ************************* Duk abubuwan da Mak'asudu ya ce a nemo sun nemo kuma sun aiwatar da aikin kamar yarda yace d'in abunda ya rage wa Waziri shine zuwa bakin ruwa ya yanka rago shima ya sa d'amba gobe da Asuba zai futo domin an samo ragon irin wanda Mak'asudu ya buk'ata... Yau ne girki Balaraba ya kama,, duk dama wancan kwanakin ya na Cikon na Halisa ne, sai Azima da yayiwa kwana uku, wannan mutuwar da akayi yasa Balaraba taga kamar kwanakin sunyi sauri, ita fa bata lissafin komai yanzu duk bata cikin hayyacin ta domin mutuwar Sallau sai ta dawo mata da ta iyayen ta sabuwa,, jiki a sanyaye take yin komai, k'arfe shida ta kammala girki mai rai da lafiya tayi Wankanta gami da fesa turare ko ina a jikinta, tana sanye da wani material sky blue yayi mata masifar kyau, inda tayi amfani da k'aramin mayafi tayi rolling dashi,, anyi mata kitso ta tattare shi a tsaki ta sanya manya-manya ribom sai ya zama kamar a cuci tayi kyau sosai d'inkin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108