Chapter 84
Chapter 84
Azima ta zauna cikin kujera tana tab'e baki itakam ba zata iya Wannan bautar ba, duk yawan bayin gidan nan ace dole sai sune zasu had'a ruwan Wanka, wacce taga zata iya taje tayi. Balaraba kuwa gudun kar magana tayi tsayi yasa ta nufi hanyar sama cikin nutusawar ta, wata banzar harara Azima ta bita dashi. Shatima yace" Haka ake so Gimbiya kuma Amarya ta gaban goshin mijinta" Azima taji kamar ita yake fadawa magana, kawai sai ta fara shan kamshi tana amsa musu magana sama-sama. Yana zaune a gefan gado ta shigo dakin bakinta d'auke da sallama, had'a ido sukayi a karo na biyu, sai tayi saurin d'auke nata idon. Ganin yanayi da ta ganshi, a ciki, shikam ai kallo yake mata na mutukar kurrula ya kafe ta da ido gaskiya tayi masa kyau sosai da sosai, gyaran murya yayi cikin yanayi maganar sa yace"Ki shiga toilet ki had'a min ruwan ka amma kar yayi zafi sosai" Balaraba ta kama hanyar toilet cikin tsarguwa kafarta sai rawa take tasan idonsa ne a kanta, ta bud'e band'akin kenan zata shiga yace"Jimana" Tsayawa tayi ba tare da ta waiwayo ba, tana bal'in jin haushin Wannan sunan wai Jimana" Idonsa ya lumshe ya bud'e su sun fara sauyawa yace"Ki matsa min makilin a brush kinji ko" Haushi duk ya ishe ta, ta lura dashi d'an iko ne.Toilet d'in ta shiga ya fara had'a mishi ruwan kamar yadda ya buk'ata, ta matsa masa makilin d'in ta aje inda ake ajewa, tana k'okarin futowa ne shi kuma ya shigo ciki, sauri kaucewa tayi domin ta bashi hanya kanta a k'asa kwata-kwata batason had'a ido dashi, tsayawa yayi yana kallonta ,,, jikinta ya bata cewar kallonta yake cikin zuciyarta take cewa dama haka mutumin nan yake da kallo, d'ago kanta tayi tan gyara fuskarta gudun raini, suka had'a ido, sai tayi saurim d'auke nata idon ganin yadda nashi ya kad'a yayi jajazur, gashi sun wani k'ankance duk girman idonsa, jarumta da dauriya ta aro tace"Zo ka wuce ga hanya" "Zo ka wuce ga hanya? Ya maimata maganar da tayi masa tamkar wata uwarsa ce take bashi umarni yanda tayi maganar. Aikuwa sai ya tawo tayi k'asa da kanta tana jira ya wuce,, ya k'araso daf da ita taji gabanta na dukan uku-uku babu zato! Taji ya rungumeta sam! A jikinsa yana sauke wata zazzafar ajiyar zuciya, abun yazo mata a bazata! Shine yasa ta kusa fad'uwa k'asa sai yayi saurin tallafo ta jikinsa suka zube dandagaryar k'asan tayel, Balaraba ta shiga rudu ganinta kane-kane kan cinyarsa, shi kuma jikinsa na kyarma! Yake lalubar jikinta har sai da yayi nasarar cafko k'irjinta abunda yake mutukar muradi kenan ya gigice mata ya fara murza mata su duk da suna cikin Riga bai hanashi jin yaya taushin su yake ba a hannusa. 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿97* Wani irin yanayi ta shiga lokacin da taji abunda yake mata da k'irji, tsigar jikinta ta mik'e sosai,taji jikinta ya mutu murus ta kasa yin katab'us a jikinsa, ganin yadda jikinta ya shika ne yasa ya fara k'okarin cire mata rigar ko ta halin k'aka ne,,, nan ta dawo hayyacinta da sauri ta mike daga jikinsa,lokacin shi kuma jikinsa ya mace, saboda halin sha'awar da yake ciki, bakinta na rawa tace"Wato dama abunda zakayi kenan shine yasa ka kirani" Wani kallo ya watsa mata a kasalance yace"Laifi ne,Ku haram na aikata da har kike min wannan maganar" Kallo me kama da harara tayi masa ji take kamar tayi masa tsaki sai ta tuno kuma matsayinsa a gurinta,kama hanya tayi zata wuce Ya rik'e hannuta guda yana k'okarin mik'ewa tsaye ina k'arfin ba d'aya ba,ai kawai sai ta rikoto kansa,, tana nishi! riketa yayi sosai suka mik'e tare kallonsa take cikin jin haushi, ta kama hanya zata wuce a karo na biyu, had'e ta yayi da bangon d'akin yana fad'in "Idan baki rage min sha'awata ba, zaki shiga hakkina ina cikin halin taimako" Maganar ta girme ta,, yanzu ta fara jin tsoransa ganin yadda ya ware k'arfinsa a kanta duk ya tareta da gangar jikinsa,, Bakinsa na dab da nata hucin numfashinsa na duk fuskarta. Lumshe ido yayi gami da tallafo kanta ya had'e bakinsu guri guda kiss d'inta yake babu sauki, Sosai Balaraba ta shiga shauki tana mamakin yadda take jin wani mugun dad'i na ratsa mata kwakwalwa wato dama haka ake ji shiyasa turawa da indiyawa Larabawa suka nacewa kiss had'a baki saboda suna jin dadi. Sosai Sarki! Ya hargitsa ta da zafafan kiss d'in shi mai wahalar mantawa Sai da ya tabbatar da tayi laushi sannan ya sake ta da ido jajazur! Saura kad'an ta fad'i ta tsaya da k'afafunta, da sauri ta futa daga toilet din tayi niyar barin d'akin ba tare da tayi tunanin halin da take ciki ba. Shima abunda ya tuna kenan, tana gaf da futa ya k'araso da sauri ya cire key din ba tare da ya kalleta ba ya wuce toilet din domin yin abunda ya kaishi, amma fa daurewa kawai yakeyi yayi hakane domin ya ragewa kansa damuwa Ashe bai sani ba damuwar sai ta kara nunkuwa kan ta da. A daddafe yayi Wanka ya dauro towol dinshi ya futo yana goge jikinsa had'a ido sukayi da ita ta cikin mudubi, dukaninsu suka d'auke kai a tare,,, Murmushi ya saki Mara sauti cikin zuciyarsa yake cewa yarinyar nan fa bata da juriya da gani romance kawai ya labdatar da ita,, Lallai ya gano lagonta. Tana kallon shi yana shirya wa cikin kaya irin nasu na sarauta sai k'ak'ale yake turare kamar yayi magana ya fesa yafi kala bakwai a jikinsa d'akin Duk ya gauraye da kamshi,,, Cikin k'asaita ya nufo inda take tsaye yana k'araso wa ya rik'e hannuta ya bud'e k'ofar suka futa daga dakin, babu Wanda ya kula kowa a cikinsu har suka sauka k'asa. Shatima yace"Ai da mu muna cewa kawai mu tafi amarya ta rik'e maka wuya,, Shiru yayi musu yana kallon Azima da tayi kicin kicin da fuska kamar ta kurma ihu ganinshi rik'e da hannun Balaraba sai annuri suke futarwa. Shahid dariya kawai yake kunshewa ganin abokinsa yayi shar da shi yasan halin mutumin sa sai da ya d'ana abun,ganin Duk yanayin Balaraba da alama bata cikin nutsuwa domin Sam taki had'a ido dasu Zama yayi cikin kujera,, Har yanzu hankalinsa na kan Azima, ita kuma sai cunkushe fuska take. Ganin haka yasa Balaraba ta yi hanyar futa daga falon tanai wa su Shahid sallama. Domin tasan halin dabbacin su Azima yanzu sai ta hau hauka da surutai Wanda ita kuma tana ji tana gani baza tabari su zageta ba, Kallo ya bita dashi har ta futa,yw sauke ajiyar zuciya me zafi, duk suna kallonsa wata kibiyar kishi ce tazo ta tokarewa Azima makogwaro wai dame wannan yarinyar tafisu ne? Ta lura fa Sarki! yana sonta tunda gashi ya kasa b'oye son yana nunawa a zahiri. Yanayin fuskarta ta gyara domin bata so tayi masa magana cikin b'acin rai! taga alama dole sai ta had'a da kissa da shiyasa, tace"Yallab'ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108