Skip to content

Chapter 103

Chapter 103

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
Download Book

fadin"Kai wai ya kabarin wancan gurgun ne,? Wallahi naso ma mutuwa yayi shege Dan asara,wato shi da yana zaune yana jiran mulki, kakansa yayi ubansa yayi Dan rashin imani,shine yake so yayi shima, ko an fada masa muma ba 'yan sarautar bane oho,ai yanzu kuma mulki ya dawo hannunmu Dan uwarsa sai dai yaga anayi sai mun kashe shi da bakin cikin mu." Ansar yace." Kaii manta da wannan, sai muga da wace k'afar zai hau kujerar mulki ballantana ya zauna." Hahahahahaha!!suka kwashe da dariya, kamar da wasa sai Khalifa ya k'ware ya fara tari!! Ansar ya mik'a masa ruwa ya kurb'a tarin yak'i tsayawa idonsa yayi jajazur har yana k'okarin fad'uwa daga kujerar ya damk'e k'irjinsa sosai yana ta tari idanunsa duk sun futo waje, Hajiya Kattime ta futo daga dakin taga abunda yake faruwa da sauri ta k'arasa gurin tana salati, har ya fado daga kan kujerar ya kifa sosai ya galabaita, Ansar duk ya gigice' yan uwansa dasu kenan sunyi tsaye a kanshi, ji sukayi kamar anyi ruwa an d'auke, da saurin Al'amin ya d'ago shi, sai yaga wuyansa ya karye ya tafi luuuuuu ya fad'i kasa, salati suka saka, Hajiya Kattine tace." Innalillahi, waina'ilahi raji'un.! Khalifana babana ka mutu ka barni babana kabi Dan uwan ka Moddibo, ya Allah ya jikanka Khalifa na." Tana share hawaye take fadin Wannan maganar, aikuwa gida ya rude da kuka sosai, mutuwar ta girgiza su mussaman dai Ansar da suke, hira dashi, da sauri Al'amin ya nufi fada domin ya sanar da mahaifin su halin da ake ciki. 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿116* Waziri na zaune a fada sai bada umarni yake cike da izza! magana ma da k'yar yake yin ta,wai shi dole ga Sarki, Al'amin ya shigo cikin tashin hankali ya zube gaban mahaifinsa ya fara Sanar dashi halin da ake ciki. Hankali a tashe ya mik'e fadawansa suka rufa masa baya,kwata-kwata ya manta da alkwarinsu da Mak'asudu, yana isa ya Tarar dasu hankali a tashe mussaman Hajiya Kattime da ta kusa zautuwa domin. Bayan tafiyar Al'amin shima Ansar d'in fad'uwa kawai suka ga yayi yana rike cikin sa kafin su ankara sukaga jini na b'ulb'ulowa ta bakinsa da hancin sa,gaba ki daya sun rasa wanda taimako zasuyi masa, Khalifa kuwa tuni Allah yayi masa rasuwa kafin Waziri ya k'araso mutuwar Ansar din ta afuku a gabansa, zaman dirshan yayi a gaban gawawwakin 'yayansa ya sunkuyar da kansa kasa yana kukan zuci,kamar daga sama yaji wata murya kamar ta Mak'asudu yana fad'in." Kar ka manta da alk'awari mu dakai,yau na cika shi shiyasa ma na shanye jinin 'yayan ka saka fi so da kauna."!!! Zumbur!!! Ya mik'e tsaye idonsa yayi jazur ya kalli sauran 'yayan nasa yace." A shirya yi musu suttura." Yana gama fad'in haka ya shige asirtaccan d'akinsa, Hajiya Kattime ta bishi da kallo cikin mamaki ganin bai damu ba, yanzu tafara zargin sa, Sosai take zargin wannan dakin da ya kulle ya hana kowa shiga,dole tafara bunkice a kansa. Kafin kace kwabo mutuwar su Khalifa ta watsu a gida da waje, su Sarki! Ma labari ya same su,sunyi mamaki sosai daga bisani Sarki yace." Ba'a mamaki da ikon Allah, Galadima da me girma governor ne suka dunga tur da halayyan Waziri domin su sun San abunda yake faruwa saboda mulki babu abunda Waziri bazai yi ba. Mama ce ta dinga d'ebe wa Kattime kewa har akayi sadakar uku kowa ya watse Hajiya Kattime ta kudiri aniyar bibbiyar mijinta da abunda yake aikatawa tana fatan asirinsa ya tuno a duniya shine sanadin mutuwar 'yayan ta uku, tayi da tasani data aure shi. Saboda mugun bakin halinsa. Waziri kuwa yana shiga d'akin sirrinsa ya kulle da mukulli ya zube bakin kofar yana warware nadin dake kansa, gumi na tashin hankali kawai takeyi wasu zafaffan hawaye ne suka fara zubo masa, lokaci guda yayi rashin 'ya'yan shi biyu lallai Mak'asudu ya shammace shi, kuka yayi sosai daga bisani ya miki ya maida rawaninsa ya futa daga dakin, yanzu yasan kuma Mak'asudu baya binsa wani bashi tunda ya biya shi. *Niko nace haka kake gani Waziri aljan ba'a iya masa sai Allah* ********* Uwa! na zaune tsakar gida ta zabga uban tagumi tunanin rayuwa kawai take, duk ta rame ta ko jale,Shamsiyya ce ta futo daga ban daki hannunta rike da buta cikin ta ya tsofa sosai duk ta kumbura, Sadiya matar Kawu na hangota tace." Ki dinga tafiya a a hankali da gurin nan kar ki fad'i saboda santsi." Shamsiyya ta d'aga kanta cikin tausayin kanta taje kusa da uwarta ta zauna da k'yar.Uwa! Ta sauke ajiyar zuciya tace." Shikkenan yanzu kamar yanda na fidda rai da Iro haka zan hak'ura da Mabaruka, anyi neman duniya ba'aganta ba." Shamsiyya tace." Jiya fa Walidi yake ce miki ya samu labari gurin wani abokin kasuwanci sa wai ya ganta cab portarcouht ita da saurayin ta." Uwa! ta share hawaye tana fadin ." Allah ya dawo da ita gida ubangiji Allah ka shirye ta kasa ta gane duniya ba mattabata bace." Cikin sanyi murya Shamsiyya tace." Ameen" Lantana ta futo daga d'akinta ta zauna suna Tisa maganar,Lantana Duk tayi sanyi,kusan kullum tana daki tana Jan carbi sallar walha bata wuce ta, ta koma ga Allah sosai domin mutuwar Sallau ta gigirgaza ta, yanzu basa cikin k'angin rashi Walidi na tsaye a Kansu basu da yunwa,kuma daga gidan Sarauta Mama nayi musu aike duk wata. ********** Alhmdullahi yau satin su guda A k'asa me tsarki, sauk'i ya soma zuwa da izinin ubangiji duk Wannan kumburi da k'afafun sukayi ya sab'e kwanan su biyu da zuwa aka fara yi masa amfani da magunguna na islaminc masu d'auke da ayoyin Allah a ciki, yasha a shafa k'afafun nasa, dasu yanzu yana iya motsa su, amma bai iya taka su,yayi wata kib'a sosai saboda samun kulawa daga my life d'in shi Balaraba soyayyar sa yake sha sosai idan yaga babu idonsu su Shatima, dake su in Safiya tayi suna tafiya harami su yini sai yamma suke dawo wa, wannan damar da ya samu ya dinga more amarcin sa, Balaraba ta saki jiki dashi sosai tana bashi kulawa, shi kuma sai yayi tayi mata shagwaba yana lanjarewa, da dare yayi zata ga ya watsake yana Mata kallon love, tun bata gane wayon sa ba har ta gane shi, sai dai kawai tayi masa dariya, suna samun waya sosai daga gurin Mama, taji dad'i da taji jiki yayi kyau, Balaraba ta sha addu'a a gurina. Daga Wanka ta futo daure da towol cinyoyinta duk a waje ga kanta sai d'igar ruwa yake, yana zaune gefen gado daga shi sai k'aramin wando, da alama angama

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108