Skip to content

Chapter 32

Chapter 32

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,261 words 0 views Progress saved
Download Book

irin kallo, a ya mutse yace"Karya nake kenen" Murmushi Maddibo yayi yace"mai da wukar malam, ni zani gurin Gimbiya in ci abunci, ko injiraka ne" A hasale yace"wallahi zamuyi fada dakai, kar ka kara sakoni cikin maganar ka da wannan yarinyar in kana son kanka da arziki, kai daka ga zaka iya kaje kayi, amma ni, kasan nafi karfin inci kazantar ta" Daga kafada Maddibo yayi alamun abunda ya fada bai dame shi ba,yace"Ni kam zanci har da side kwano, sai na dawo" Banza yayi masa har ya fuce daga dakin. Maddibo na futa wasu bayi suka shigo Maza biyu mata biyu Wani irin kallo ya watsa musu cikin tsawa yace"wane shegen ne yace ku shigo min daki,"? Kasa sukayi da kansu dukkaninsu Cikin tsawa ya cigaba da cewa"ni kuturo ne da komai sai kuce sai kunyi min, nace bana so, nace bana so, amma sabuda tsabar naci! kullum sai kunshigo min daki da sassafe! kufuce ku bani guri" yafada cikin tsawa! Zubewa sukai gabansa, kamar wasu masu neman gafara, wannan abun ya kara tunzura masa zuciya, a zafafe! yace"me kuma zanyi muku,, bakuji abunda nace ba? Mariya ita ce baiwar shi wacce take kula da gyaran bangaran shi da da kai masa abunci da daukewa in ya kammala goge-goge da share-share, ita ce tace "Ranka ya dade don Allah kayi hakuri ka bari munai maka hidima a shashen ka, domin aikin mu ne,hakan ka gafarce mu, ranka ya dade, zamu maka gyare-gyare ne" Wani kallo ya watsa mata, wanda yasa ta sunkuyar da kai kasa, babu shiri,domin idanunsa duka ya ware mata,tunda take dashi ba ta taba ganin ya bude idonshi haka ba, kullum a lumshe suke, ko kallon ka yake, baya budewa sosai kasa-kasa yake kallo. Yace"kece Sarkin iyayi ko, wacce tafi kowa iyawa, kowa yayi shiru zaki damu mutane da magiya,Ok ku fuce min a daki, tukkuna inyi abunda zanyi in futa,sai kuyi abunda zakuyi" Ya karashe maganar yana hararasu,sai kace su sukai masa laifi Daya bayan daya suka fuce daga dakin, suka tsaitsaya a falo suna gulmarsa, kasa-kasa Mariya tace"yau da alama a kwai abunda yake damun Yallabai wannan masifa haka" Wacce take kusa da ita tace"kuma hakan ba halinsa bane,shi dai kyaleshi da muskilanci gami da shariya" Mariya tace"gaskiya akwai wani abu dake damunshi" Haka dai sukayi cirko-cirko a falo suna magana kasa-kasa, gefe kuma suna jiram fitowarsa,domin su fara aikinsu Yana kokarin mikewa ne daya daga cikin wayoyinshi ta hau gyara, ko kallonta bai yi ba balle ya dauka, toilet ya nufa, cikin zuciyarsa sai mita yake, ya tsani kamarshi azo ace sai an masa komai, yana da lafiya da kuzari Allah ya hore masa sai ya tsaya an masa bauta, shi sai yake ganin wannan cutar kai ne, a rayuwar shi ya tsani yaga ana wani jin tsoransa,kamar ayi masa sujjada, kamar dai yadda suke masa, shiyasa kullum cikin yi musu tsawa!yake, baya son wannan rawar jikin da suke masa, Sarki!bayason raini ko kadan, shiyasa abunda Balaraba tayi masa ya kasa bacewa a zuciyarsa,dalili kuwa shine tunda yake a rayuwarsa babu mahalukin da ya taba yi mishi abunda tayi Toilet dinshi abun kallo ne, sosai in ka shiga baza kayi sha'awar futowa ba,domin har wani sanyi-sanyi yake,duk abunda mutum yake bukata a kwai a ciki Jaccuzi kuwa har biyu ne a ciki, sabuda girman toilet din, a nutse ya shiga ya hada sabulai na mussaman yayi wanka, ya futo ya nannade jikinshi da towol ya dauki karami yana goge kanshi, Kai tsaye dressing mirrow dinshi ya nufa, ya tsaya jikinshi a fara shafa mayukanshi masu kyau da tsada, ya taje sumarshi sai kyalli take,itama ya sanya mata mayuka, Kwantaccan gashin dake fuskarshi yake gyarawa sosai ya gyara Sajanshi ya tsaida gemunshi iya inda yake so, sai fuskar tafito tayi wani mugun kyau da haske,kalar fatarshi ta fito sosai,annuri ne kawai yake futa a fuskarshi, Wayarshi ce take kara alamun kira,bai saurare ta ba,sai da ya futo da kayan da zai sanya,sannan ya zauna gefan gadon ya dauki wayar yana dubawa a nutse. Khalifa sunan da ya gani yana yawo kan fuskar wayar, Khalifa dai yaron Waziri ne, kani ga Maddibo, kenan yaron bashi da kunya ko kadan shiyasa basa shiri da Sarki! ko kadan yanzu ma yayi mamakin ganin kiranshi, sai da yagama yangarshi sannan ya dauko, "Assalamu alaikum" Daga daya bangaran Khalifa yace"Yallabai barka da asubah" "Barka kadai, Khalifa ya kake"? " Lafiya yallabai, dama Baba Waziri ne yace kazo yana neman ka" Shiru yayi na tsawon minti uku,kana yace"Ok ya fita fada ko yana gida"? "Yana gida" "Ganinan zuwa" Yafada yana kokarin kashe wayar, Mamaki yake kiran me Waziri yake masa Allah yasa alkairi ne, Tsaf ya shirya cikin wani uban yadin filtex me ruwan sararin samaniya, an mishi dinki irin na sarauta sosai yayi masa kyau, kafarshi saye da takalmi irin nasu shima kalar kayan jikinshi, wayoyin shi ya diba ya futa daga dakin, suna tsaye sukaji futowarsa, da sauri sukayi kasa da kansu, ko kallonsu bai yi ba ya fuce daga falo, Wasu bayi maza su biyu suna tsaye bakin kofa,suka zube suna kwasar gaisuwa, yana tafiya yake amsawa, suka mike da sauri suka rufa masa baya Duk wasu bayin dake kaiwa da kawowa a filin gurin tsayawa sukai suna gaidashi, har sai da ya wuce sannan kowa ya koma bakin aikinsa, *Ikon Allah Sarauta da mulki sai mai shi*😇 *Comment* *Vote and Share* [10/07, 05:14] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®REAL BINTU BATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*Zamani Writes Association*_🤝🏻 _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` *🅿44* ```Bisimillahir-rahamanir-rahim``` Waziri na zaune a falo tare da uwar gidanshi, Hajiya Rahamatu, wato mahaifiyar su Modibbo, wacce suke kira da Mama, macace mai mutukar kirki da maida dan wani nata, tana da kara da kawaici,da kauda kai a kan abunda babu ruwanta, shiyasa kullum cikin tsawatar da "yayanta take, a kan su lura da duniya mussaman in taga suna jiji da kai da nuna su " yayan sarauta ne, kullum takance musu,babu wanda Allah ya ware tsakanin tsakin bayinsa,me mulki ko mara mulki talaka ko me kudi,sai wanda yafi bauta masa. Wani lokacin idan Waziri yana wani abun na son zuciya takan iya bakin kokarinta gurin ganin ta hanashi, haka zasuyi ta rigima dashi, Amaryar shi ce,halinsu yazo daya,duk wasu abubuwan da yake yi ita take ingizashi,yake da girmanshi da komai,bashi da gaskiya kullum cikin shirya manakisa yake. A nutse Sarki! yayi sallama cikin falo,Mama ta amsa masa cikin sakin fuska, tana gyara masa gurin zama, fuskar sa ya saki sosai ya je ya zauna kasan kafafun ta kanshi a kasa yace"barka da asubah Mama" Kanshi ta shafa tace"barka kadai, Almansor,yau sharabon da in sanya ka a idona" Sosa kansa yayi irin na sabo yace"Yace Mama Ayi hakuri, a gafarce ni" Dariya tayi kawai tace"ai nasan hali baka son mutane dama" "Mama a dane wannan" yafada yana sosa kansa Wani irin kallo Waziri yayi masa yace"kema ai da neman magana kike wannan yaron da baya son jama'a ko kin manta da halinshi, wai kuma a haka akeso a bashi mulki" Shiru Mama tayi jin abunda mijin nata yace, tasan yanzu zai kauce hanya Girgiza kai kawai Sarki! yayi ya dago kanshi fuskarshi

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108