Skip to content

Chapter 80

Chapter 80

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,229 words 0 views Progress saved
Download Book

ake nau'i -nau'i tsakar gidan ya cika, sai suka fara d'orawa akai. Sallau ya rarrafo ya futo duk ya rame ya susuce, ganin uban himilin kayan dake jibge a tsakar gidan yasa ya kusa fad'uwa ya kalli Lantana yana wani irin murmushi yace" Hak'ika Haihuwar Maburuka tayi min rana, yanzu wannan mutsiyaciyar matar zata San ni bak'ashin yar wa bane, ni mutum ne Wanda ya cancan ci a had'a jini dashi" Aikuwa Uwa! Tayi kansa da masifa sai kuza masa ashar take tana fad'in k'arya yake ya zage ta ko yace ita ba me kashin arziki bace, Fad'a suke sosai suna fad'a ma junansu bak'aken maganganu, da tada tsohon Abu da ya faru a tare dasu. Gidan ya cika da matasa da yara "yan unguwa kai harda matan aure wasu sun futo daga gidajansu domin su bawa idanunsu hakkinsu. Abokin Walidi ne yace" Don Allah kuyi shiru mana arzki yana Neman Ku kuna kokarsa, wannan da kuka gani a zube to ake ne daga gidan me Martaba Almutafah Allah ya gafarta masa. Shamsiyya najin abunda abokin Walidi ke fad'a sai kawai ta zabga wani ihu!!! da gudu ta shige d'akinsu tana ihu tana tsalle fad'i yake "An yanka ta tashi, dama ni nasan tunda Arrama yace" In saurara komai zai zo da sauk'i nasan lokacina yayi, tabbas aikinka kamar yankan wuka ne a gurina, Mabarukan banza ina taga arzikin da zata kawo wannan kayan" Gudar dubu d'aya ta futo da ita a hannuta,bakinta kamar gonar auduga ta mik'awa Abokin Walidi tana fad'in "Karb'i tukwuci ai dole ne In biya ka, irin wannan alkairi haka" Karb'a yayi yasa a aljuhunsa yana godiya ya kalli Lantana yana fad'in wasu Samari biyu sunaso su shigo Ku gaisa don haka sai Ku gyara guri" Yana gama fada r maganar sa ya juya ya futa sauran abokansa da yaran suka rufa masa baya, d'aya bayan d'aya mutane suka futa suna ta gulmar su. [9/8, 5:19 PM] Akwai Citta💵💵: Sallau da Uwa! Cigaba da fad'an sukai Lantana tace"Sakarkaru kawai a gaban "yayan Ku kun zauna kuna fad'a ai sai kuje kuyi tayi" Ta k'arshe maganar tana marmatsar da tarkacen takalman dake bakin k'ofa. Sam! Baka jin sallamarsu saboda Hayaniyar Sallau da Uwa! Sai da abokin Walidi ya buga musu tsawa sannan suka dawo nutsuwar su,, suka hau washe baki sunawa su Shatima barka da zuwa. Amsa sukeyi cikin mutum ci da karrama d'an Adam, Lantana ce tayi musu iso har rumfar ta, ta shimfida musu tabarma, bakinta kamar ya tsage dan fara'a sai wani sunkuya musu take tamkar wacce za'ayi musu sujjada, shi kanshi Shahid din ya fuskanci abun take yayi yawa, yace"Baba ya isa,ki nutsu kinji zauna sosai magana me muhimanci muke tafe da ita" Lantana ta gyara zamanta har da tankwashe kafafu tana fad'in "To Allah ya jisshemu alkairi, ko da yake ai alamar karfi tana ga me k'iba, ina sauraron Ku" Shahid ya zuba mata ido yana nazarinta daga busani yace"Ina mahaifin Balaraba? Gurin shi muka zo" Wata irin faduwar gaba ce ta rikitowa Lantana bata shirya ba, baki na rawa tace"Wac...wace Balaraba..kuke tambaya? Ashe duk abunda yake faruwa a kunnen Sallau da Uwa! Jan jiki yake domin ya k'arasa rumfar domin yajiyewa kansa tabbas,a sukwane Uwa! Ta tsallake shi,har tana take masa cinye, ta bankad'a labule ta afka cikin rumfar babu, Sallama fad'i take"Wace Balaraba kuke tambaya"? Shatima ransa ya b'aci sosai ganin rashin mutumcin da Uwa! Take tazo ta tsaya musu aka, tunda ta shigo dakin ya d'ume da tsamin hammata,, sauri yake su tashi. Shahid ya daure zuciyarsa domin ya fara fuskantar akwai babbar Matsala a tartare a gidan. Yace"Balaraba Ayuba Tanko" Lantana tace"Ayuba ya mutu shekara da shekaru Balaraba bata da uba kamar wannan Wanda yake zaune"tafada tana nuna Sallau dake rawar jiki. Shahid ya kalleshi yana fad'in "Kaine Waliyyin ta" Kamar wani k'aramin yaro Sallau ya d'aga kansa, yana sauraron abunda zai biyo baya Shahid yace"Ga kaya can daga gurin Mama Fulani tace akawo muku a matsayin Ku na iyayen Balaraba mata ga Sarki! Me jiran gado wato Sarki! Almansur insha Allahu gobe za'a d'aura mata aure dashi" Ihu!! Shamsiyya ta kurma ta afko cikin dakin tana fad'in "K'arya kukeyi Wallahi baku isa, ni za'a yaudara da muna furci billahillazi bazan lamunta, wannan kayan nawa ne, kuma gobe dani za'a d'aura auran ba da wancan shegiyar ba" Cikin ihu da tashin hankali Shamsiyya take maganganun sai dara take tana tsalle, Uwa! Ta dunga zabga zagi tana habaice habaice Sallau da Lantana kuwa Shiru sukayi suna mamakin wannan al'amari Ganin sun gama abunda ya kawo su yasa suka mike cike da mamakin dabi'ar mutanan gidan tsallake Sallau sukayi Wanda yayi rashe-rashe a bakin Kofa suka futa cikin tashin hankali domin Sam Shatima baya San hayaniya da yawa yanzu kansa zai fara ciwo. Ganin sun futa yasa Lantana mik'ewa da sauri ta bi bayan su, sai kuma ta dawo da sauri ta koma cikin d'akinta ta d'auko wani Abu tana boyewa cikin hijab, rad'a tayiwa Uwa a kunneta ta futa a sukwane! Lokacin Buba Direba har ya kunna mota ta karasu gurin tamkar sabuwar mahaukaciya tana fad'in Ku tsaya kutsaya" Shahid yace da Buba ya tsaya Lantana ta iso gurin tana haki!! Tace"Inaso in biku gidan sarautar domin a gudanar da harkokin buki dani, a matsayina kamar Balaraba. Shatima yace"Bud'e mata Kofa ta shigo, aikuwa Buba ya bud'e kofar mota Lantana ta shiga ta zauna tana k'ara damk'e abun da yake hannuta. [9/8, 9:34 PM] Akwai Citta💵💵: ********** ********** ********** Wata irin fad'uwar gaba taji lokacin da taji abunda yake cewa, kar dai wannan mutumin zarginta yake. Take fad'ar haka cikin zuciyarta. Tamkar wacce aka aikowa da mala'ikan d'aukar rai! Haka ta kicin-kicin da fuskarta, cikin yanayi irin na b'acin rai tace"Wannan ba hurumin ka ba, cewar maza nawa na kula ko nayi mu'amula dasu lokacin ina sana'ata, kai bari kaji wani abu da baka sani ba, yau kasan dashi, na Dade da sanin dama kanai min kallon "yar tasha me sai da abunci cikin kasuwa, babu irin maganganun da baka fad'uwa Moddibo ba,kan kar ya aure ni, kushe da hassada basa hana gamji toho nida Moddibo soyyaya ce ta tsakani da Allah, ina mutukar alfahari da sana'ata,kuma duk inda na shiga na futa naji ana zagin masu irin Sana'a ta sai inda karfina ya tsaya, saboda haka tun kafin magana tayi nisa mutukar kasan da wani k'uli a ranka a game da aure na, sai ka janye kawai babu Lallai babu dole a ciki" Ta k'arashe maganar tana sauke ajiyar zuciya. Fuzgo hannuta yayi tafad'a kansa, ya rungume ta tsam! K'irjinta ya dunga fat-fat! Shima nashi haka, muryar shi a tsark'e yace"Ni kike k'okarin zagi ko saboda kawai na tambaya ki, abunda nake da hakki akansa" Da sauri ta fuzge jikinta tanai masa kallo na wani irin mutum mai baud'adan ra'ayi yasan yayi Abu ya nuna bai yi ba, babban abunda yake bata haushi dashi shine son ya tab'a mata jikinta. "Sama-sama tace" Babu maganar zargi a magana ta,ai gaskiya ce tun yanzu naga take-taken ka, kayi hakuri idan na b'ata maka rai,da kalaimai na" Tana gama maganar ta shige d'akin da suke kwana. Kallonta yake babu k'iftawa har sai da ta shige dakin sannan ya d'auke kansa, yana

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108