Skip to content

Chapter 72

Chapter 72

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,271 words 0 views Progress saved
Download Book

sak'i ya d'aura a k'ugunsa,jikinsa duk layu da tarkacen kayan tsafi, wani k'ok'o ne a gabansa me k'urzunu-k'urzunu da wasu takarce a ciki, wasu ciyaye shi da jajayen yankuna,an suka musu allurai" Da baya-da baya ya basu umarnin shiga d'akin,suna zama ya fara furje-furje wata kumfa na futowa daga bakinsa,sai ya mik'e tsaye yana wani irin tsalle yana zagaye su, bakajin komai sai sautin kayan aikin dake jikin k'afafunsa da hannayensa da wuyansa, kacacar-kacacar, wasu zan tuka yakeyi yana tumami a gurin, ya zayi zaman bori a gansu,duk kamaninsa sun sauya,kana ganinsa kasan bashi bane, Hajiya Kulu ta tsure tana had'iye yawu da k'yar,shi kuwa Waziri farin ciki yake yasan k'arshan wahalarsa ta k'are. "Nine Aljani Mak'asudu, dan gidan sarki K'azaza,jikan Sarki Jajubu" Nine na gaji sarauta,sama da k'asa, Nine nake da Muk'ulin mulki a hannu na, nasan abunda yake zuciyoinku, duk biyun,saboda haka kun kawo kukanku inda za'a share muku hawaye. Abunda sukaji d'an bori Tsito yana fad'a kenan. Waziri yace"Allah ya ja zamanin ka, tabbas kaine ka gaji mulki gaba da baya, ko a cikin jinsun Ku,ma zuriarku daban take,da kowa muna fata wahalarmu tazo k'arshe" "Ihuhuhuhuhu! Aljani Mak'asudu yayi,ya kyalkyale da dariya,yana Fad'in " Kasamu mulki ka gama, gobe ka kwana da shirin hawa kujerar sarauta,domin zan b'atar da d'an uwanka a duniya jininsa zan shanye tass!! Wannan mataki na farko, bayan na shanye jinin d'an uwanka, zaka bani jini bil'adamu k'afa shida bakwai kenan,,,wannan shine sakamako na" Waziri yace"Duk za'ayi maka daga yau zuwa gobe zan kawo maka,bil'adamu kasa jini ka k'oshi. Gyad'a kai Aljani Mak'asudu yayi, ya kalli Hajiya Kulu yace"Ke ma kije buk'atar ki ta biya, zamu sa, a tsugunar miki dashi wannan yaron da ya tsaya miki a zuciya, zakiyi yadda kike so ke da yaran ki, itama Uwar tasa duk wani abu da take ji dashi, zamu sauke mata shi,amma dole mubi a sannu saboda tsarin da yake jikinta,a shekarun baya mahaifinta ya bamu wahala sosai, dan haka dole mu d'auki fansa a kan jininsa" Hajiya Kulu tace"Kar kaji komai Ubana, ka fad'i bukatar ka ni kuma zan baka abunda kake nema" Aljani Mak'asudu yace"Ke ma zaki bani K'afa Uku shine muradi na" Hajiya Kulu tace"Angama Ubana, duk Wanda. Kaga yayi maka cikin gidan nan mace ko namiji ko a cikin "yayana ne,kana iya shanye masa jini na baka" Waziri shima yace"Wannan haka yake, nima ka zab'i Wanda kakeso cikin "yayana da bayina na baka, kasha jini yadda kake so" Aljani Mak'asudu yace"Ku tashi ku tafi buk'atarku ta biya ta duniya" Tashi sukayi suka futa da baya-baya. Tun a daran Aljani Mak'asudu ya fara gudanar da kinsa, takan me Martaba ya fara, jininsa ya shanye tas,a ka wayi gari babu shi,a duniya. *Innalillahi wainnailaiyi raji'un* Gida ya kacame da ihu da tashin hankali na mutuwar me Martaba sarki Almustafa mutuwar ka tsaham, yayi sallama da kowa lafiya lou ya shiga turakarsa, Liman na jira ya futo sallah asubah, shiru abunda bai tab'a faruwa ba, Sarki! Ne ya shiga shashen Mamansa, domin nan me Martaba yake, suka had'u da ita a babban falo itama ta futo, cikin wasi wasi da damuwa suka nufi d'akin da yake. Kwance suka ganshi kamar me bacci, idonsa a rufe, Sarki! Ya zauna gefansa yana tattab'a jikinsa, sanyi k'alau d'aga hannunsa yayi yaga ya koma ya kwanta yaraf!! Shi ba yaro bane yasan mecece mutuwa, Mama Fulani ta zube gurin a sume. https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿84* Cikin damuwa da tashin hankali Sarki! Ya futa daga d'akin, Jakadiya Shafa'atu na tsaye a falon tana gyare-gyare taga futowarsa,a gigice, tace"Allah ya taimake ka lafiya"? Sarki! Yace"Babu lafiya Jakadija, Allah yayi wa me Martaba rasuwa, Mama ta suma a d'aki,innalallahi wa'ina ilahi raji'un" Futa yayi bai san Inda yake saka k'afar sa, lokacin gari ya soma haske, kai tsaye masalaci ya nufa domin ya shaidawa liman abunda yake faruwa. Jakadiya Shafa'atu kuwa kasa shiga d'akin tayi, saboda tsoro da sauri ta nufi b'angaran Waziri domin ta kirawo Hajiya Kattime. Lokacin da liman ya sanar da rasuwar me Martaba mutane da dama sai suka dunga k'aryatawa kafin kace kwabo kowa ya futo daga shashinsa,har Waziri,,, ya nufi shashen Mama Fulani domin ya tabbatar. Babu Wanda ya hanashi shiga,saboda me Martaba bashi da wani d'an uwa shak'ik'i kamarsa,duk da sun san cewar babu jituwa a tsakaninsu kwana biyu. Tsallake Mama Fulani yayi ya nufi gawar me Martaba,yana dubawa, hamdala yayi a fili yace"Taka ta k'are Mustafah sai mun had'u, acan, Lillab'e gawar yayi ya futo yana share hawaye kamar gaske,nan ya k'ara tabbatar wa da jama'a cewar me Martaba ya amsa kiran ubangijinsa. Da k'yar Mama Fulani ta farfad'o ana tai mata fiffita, duk bata cikin hayyacin ta, Hajiya Kattime ta rungume ta a jikinta. Balaraba a gefenta tana share mata hawaye Mama takasa cewa komai, tunda ta farfad'o bakinta sai motsi yake,babu abunda take fad'a sai Kalmar innalillahi wa'inna ilahi raji'un" Balaraba hawaye kawai yake sharewa tana addu'a Allah ya yaye musu wannan masifa da ta tun karo su,gani take kamar k'arya ne me Martaba bai mutu ba, sai data an futo dashi cikin suttura za'a kaishi makomarsa sannan ta gasgata,fad'uwa tayi a gurin ta suma,Mama Fulani kuwa rirrik'eta akayi domin itama saura kad'an ta fad'i da k'yar! ta samu tayi masa addu'a wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, Waziri ya tasa gawar a gaba yana kuka kamar wani k'aramin yaro. Sarki! Kuwa wani mugun haushinsa yake ji,ganin yadda ya babba ke gaban gawar, ya hana mutane suyi masa addu'a, sai da aka sauke alk'urini me girma sannan aka sallaci gawar me Martaba ya samu jama'a sama da k'asa ko ina,haka aka d'auke shi aka kaishi makwancinsa na gaskiya. *** B'angaran Hajiya Kulu da yaranta kuwa duniya sabuwa suka bud'e sun cika suna ciye-ciye da kalle-kalle tamkar ba mahaifinsu ne ya rasu ba, babu abunda ya dame su,Naja'atu ce me cewa,lokacin su yayi,za tayi facaka da kud'i, son ranta Sarki! Kuwa wani irin zazzab'i ne yake damunsa tun bayan dawowarsu daga mak'abarta,daurewa kawai yakeyi ya zauna yana karb'ar gaisuwa gurin "yan uwa da mutan gari,suna kokawa da rashin da akayi, kowa sha'awa yakeyi Almansor ya maye gurbin mahaifinsa,hatta da su Galadima ma burinsu kenan,Governor da yazo gurin gaisuwar a bunda ya fad'a kenan,Waziri yayi tsagal yace" Ba haka al'adar sarautarmu yake ba,nine k'anin me mutuwa nine zan gaje shi,kafin "Yayanmu saboda haka tunda ina raye,ban mutuba ni zan zauna kan kujerar mulki" Governor yace"Wannan ba sarin mulkin k'asa bane, nine shugaba,dole nine zan zab'i sarkin gari na, saboda haka baza mubi tsarinka ba,Dan kar kace ba'ayi maka adalci ba,za muyi k'uri'a bayan sadakar uku wanda ya fi jama'a shine zai zauna kujerar mulki" Waziri ya baza babbar rigarsa cikin bak'in ciki da b'acin rai yace"Lallai kam kun jawo masifa,domin rashin zaman lafiya zai tabbatar a masarautar nan, tunda iyayenmu da kakanimu suke mulki basu tab'a wata k'uri'a ba sai yanzu, mu baza'a rusa mana tsarinmu ba" Yana gama fad'in maganganunsa ya mik'e ya futa daga fadar,ranshi a b'ace, yana ganin wannan Governor zai

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108