Chapter 104
Chapter 104
love ne, bude mata hannuwan sa yayi wai ta zo. A hankali ta k'arasa amma me makon ta shiga jikinsa kamar yadda ya buk'ata sai ta zauna gefan gadon tana ya mutse fuska, Ka fad'ar ta ya kamo ya Dan matsa kad'an k'asa-k'asa yace." Menene hummm."? Lumshe ido tayi tace." Bana jin dadin. Jikina yanzu na fara zargin kaina saboda banga period d'in ba, wannan lokacin nake yi shiru bai zo ba." 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿113* Hannunsa ya sanya ya rungumo k'ugunta fuskarsa d'auke da wani kyakykyawan murmushi yace." Lallai Allah ya amsa min addu'a ta da wuri Ubangiji Allah yasa ciki ne dake, idan hakane zan yi farin ciki sosai da sosai." Sunkuyar da kanta tayi tana jin kunyar sa a hankali tace." Gaskiya ina zargin haka domin ban tab'a batan wata ba,ko lokaci nayi nake amma wannan kwana hud'u akai gaskiya da akwai alamun tambaya." Cikin farin ciki yace." Yanzu nan zan auna ki domin in tabbatar da hakan." Towol din yake k'okarin cirewa ta rike hannunsa cike da tsoro! Kallon ta yayi yana lumshe ido,tace." Wai kai baka gajiya ne."? Kanne mata idonsa yayi yace." Kece ai kamar zuma kike sam bakya gimsa ta." Nauyin maganar sa taji yasa ya juya baya tana girgiza kai. Ya rungume ta k'am! Yana sakin ajiyar zuciya yace." Ki barni in gaisa da babyna." Shiru tayi, sai ya zura hannunsa yana shafo cikin tamkar Wanda yake mata tafiyar tsutsa ya dinga shafa mata mara lumshe idonta tayi tana sauke ajiyar zuciya, ni dai nan na futo na barsu. ******* Hajiya Kattime ce zaune a falo tana jiran futowar mijinta, sai gashi ya futo cikin shirin zaman fada, tace."Allah ya taimake ka ina da magana da kai." A k'asaince yace." Ina sauraron ki,zan shiga fada ne." Zama ta gyara tana fuskantar sa sosai tace." Dama tambaya nake so in maka." Yace." Ina sauraron ki." "Me yasa da yaran ka suka a mutu baka nuna damuwar ka ba? Kuma me yasa baka so a shiga wancan dakin na kulle."? A hasale! Yace." Ke saurara min da maganar banza haka." Shiru Kattime tayi ya cigaba da cewa." Idan mala'ikan d'aukar rai yazo kan 'yayana sai in hanashi kan wane dalili zan tashi hankalina zaki mutu zan mutu zamuje inda sukaje,saboda haka babu dalili da zai sa in tada hankalina, bayan wannan kuma kina maganar wancan dakin dake kulle dakin sirri na ne,ko da wasa kar ki kuskura ki kai kanki gurin zan iya sakin ki a kan hakan." Kattime ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki. Futa yayi ya bar ta da tunani. ********* Mabaruka ne da saurin ta cikin mota zasu dawo gida, duk suna cikin maye, Alhaji Ashiru sai fafara gudu yake, ba tare da bin ka'idar tuki ba, wata k'atuwar mota ta buge su,suka gangara cikin daji,ihu!! Mabaruka take kurmawa tana k'okarin futowa ta fado kasa motar ta bi ta kan kafafunta, ta cillata can gefe, motar ta cigaba da katantanwa a gurin, tayi raga-raga Alhaji Saminu kansa ya fashe take ya amsa kiran ubangiji ita kuma Mabaruka ta suma. ******** Hajiya Kattime na zaune a inda take tun bayan futar mijin nata take tunani kan yadda zata yaudare shi har ta samu nasarar shiga dakin sirrin shi, murmushi tayi lokacin da ta tuno abunda zatayi masa, gyad'a kai tayi a fili tace." Insha Allah sai asirin ka ya tuno mutukar ba abun kirki kake shukawa ba." 'Yan a gaji ne suka kawo dauki gurin, ba tare da b'ata lokaci ba,a ka dauki Mabaruka a kaita asibiti ,shi kuma Alhaji Saminu cikin motar suka duba suka ga katin sa da shaidar garin da yake, nan suka saka gawar sa a mota domin su kaishi dangin sa. ******* Ranar Sarki! Da Balaraba sun sha soyayya sosai ji suke tamkar su kadai suke rayuwa a duniyar Balaraba har fargaba take su koma gida, in ta tuno da masifaffan kishiyoyinta wanda ko anan ma sun dunga damunsa da kiran waya babu dare babu rana. Sai k'arfe shida shu Shahid suka shigo gidan,dama me girma governor ya koma lokacin da yayi kwana uku, nan sukayi sallahr magariba, suka zauna suna cin abunci suna hira, Shatima ya futo da magunguna ya mik'a masa, b'ata fuska yayi yak'i karb'a.Balaraba na kallonsa, ta kalli Shatima a hankali tace." Ka bari zan bashi in anjima har na shafarwar ma." Shahid yace." Hakan yayi ke in kika bashi sai yafi karb'a mu kam kullum sai ya bamu wahala." Murmushi tayi kawai. Gyaran murya yayi yace. " Na fa gaji da zaman gidan nan, Dole gobe nima na futa in kusanta kaina ga Allah don haka sai Ku shirya futa dani." Shahid yace." Allah ya kaimu goben muna fatan a sanya mu cikin addu'a." Yace." Jikina na bani insha Allahu da k'afafu na zan koma gida." Shatima yace." Idan Allah ya yarda kuwa haka muke so." Nan suka cigaba da hira suna kallo, sai k'arfe goma da rabi sannan sukayi sallama kowa ya shige makwancin sa. Balaraba ce ta tura shi bedrom ta d'auko masa kayan bacci, ta taimaka masa ya sa, ta sanya nata sukayi kwanciyar su, cikin so da kaunar junan su. 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿114* To bayan likitoci sun gama binkicen su a kan Mabaruka nan suka yanke shawarar yanke mata k'afafu domin babu wani sauran dubara da ta rage k'afafun Mabaruka duk sun karye karaya mafi muni! Wanda ko dori akayi baza su k'ara amfani ba, Mabaruka tana ji tana gani aka yanke mata k'afafu, ta futa daga cikin hayyacin ta saboda azaba fatan mutuwar ta kawai take. *********** Ranar Juma'a da misalin k'arfe d'aya shaura na rana, Waziri ya shigo cikin gidan, cikin sauri ya bude dakin sirrin shi ya shiga tare da kullewa, Hajiya Kattime na zaune a falo tana kallonsa, ya shiga ya fi minti goma a ciki sai gashi ya futo da sauri, yaja kofar tare da murza mata mukulli ya cire ya futa ba tare da ya kalli inda take ba. Kamar wacce
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108