Skip to content

Chapter 47

Chapter 47

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,240 words 0 views Progress saved
Download Book

shiga, ya mayar da murfin ya rufe, ya zagaya ya bud'e ya shiga shima, "Maddibo ya kalleta a nutse yace" wannan nik'ab d'in yayi miki kyau Gimbiyata" K'okarin cirewa take, tace"kaga ni ko ala dole nake sashi sabuda kallon da ake damuna dashi" "Nima kinyi min gata" yafad'a da murmushi a fuskarsa,ya cigaba da cewa"da zaki dinga sawa daga nan har lokacin auran mu" Kallonsa take cikin nutsuwa tace"Yusuf da gaske kana sona"? "Kwarai kuwa" yafad'a cikin shauk'i yau gashi ga ita Idanun ta ne ya fara tara ruwa tace"zaka iya aure na dani da k'anne na biyu wato Usuman da Sadiya"? Cikin tausayi yace"kwarai kuwa, duk abunda kike so ina so balle Usuman da Sadiya Gimbiya ki kwantar da hankali, in sha Allahu zan rik'e ko da amana" Hawaye ne ya fara zuba a fuskarta, taso ta danne kukan amma yak'i dannuwa, tace"Nagode sosai, inaji a rayuwata bani da mai k'aunata kamar ka, na auna ka sosai na lura tsakani da Allah kakeso na, ba wani abu nawa ne yake burgeka ba,shiyasa na yanke shawarar tsayar dakai a matsayin mijina kuma Uban "yayana, sabuda haka in ka shirya kawai ka futo muyi aure in huta da bala'in da nake ciki" Shima kamar zai yi kukan yake rarrashin Gimbyar tasa duk hankalinsa ya tashi, yace"kinyi magana a kan gab'a Gimibiya, dama ke kad'ai nake jira ki amunce min naj dad'i insha Allahu zaki futq daga halin da kike ciki zan aure ki domin kyawun halinki,ba dan kyau da wani abu naki ba, ni ina sonki tsakani da Allah" ya karasa maganar jikinsa na kyarma, ji yake kamar ya yaye mata damuwar dake damunta. Rarrashin ta yake har sai da ya ga damuwar da take ciki ta ragu, domin har dariya tai masa,sai suka cigaba da hirarsu cikin so da k'auna, yace"yau baza ki shiga kasuwa bane"? girgiza kao tayi tace"yau bazan shigaba,zan koma gida ne, domin a kwai sauran aiki da nabari, zan tare a sabon gidan da nakama haya" gabanshi ne ya fad'i yace"kamar yaya kin kama haya? haya wace iri"? Sunkuyar da kai tayi tace"har gida mana" Cikin mamaki yace" Gimbaya kin kama hayar gida, kikace min maganar babu dad'in ji, ke baki san yanzu sai ki zama abin kwantacce ba, ne, kamar ki budurwa kina zaman kanki,gaskiya ban amunce ba" ya k'arashe maganar da b'acin rai a fuskarsa. " Yanzu ya kakeso ayi ne" tafad'a da damuwa a ranta, domin bata son tona asirin gidansu" Sassauta murya yayi yace"ki bar maganar kama hayar gida kiyi hakuri ki koma gidanku ki cigaba da zama kamar yau ne komai zai huce" "Shikkenan, zan bi maganar ka" tafad'a cikin tausayawa kanta" " Yawwa nagode Gimbiyata, yafad'a fuskarsa d'auke da murmushi najin dad'i Wayarsa ce tayi k'ara yana dubawa yaga Sarki! ne, Balaraba ya kalla fuskarsa d'auke da murmushi yace"ga mutumin ki fa" "Wanene"? tafad'a cikin rashin sani " Sarki ne"! Shan kunu! tayi ta d'auke kanta, murmushi yayi kawai ya girgiza kai tana ji yana masa magana yana amsawa sama-sama, da alama wani abun yake tambayarsa, yana gama wayar ya kalleta yace" muje in kanki gida, yana can yana jirana yanzu" " A ya mutse tace"gashi ni kuma bangaji da ganin ka ba, sai yaya kenan"? Agogon hannunsa ya kalla da murmushi a fuskarsa yace"Kiyi hakuri in kin bani dama zan shigo da daddare mu k'ara gaisawa, yanzu muhimin abu ne yasa ya kirani" Tab'e baki tayi tace" wannam d'an rainin hankalin wallahi na tsane shi" Cikin mamaki yake kallon ta fuskarsa ta janza da yanayin damuwa yace"har kike rantsewa Gimbiya yanzu d'an uwan nawa kika tsana"? Tab'e baki tayi tace"ranin wayo ne dashi,wai shi d'an Sarki, nifa gaskiya ko aure mukai da kai bana buk'atarsa a gidanmu" Shiru Moddibo yayi yana jimanta al'amarin yace"ya kamata ki rage wannan tsanar da kike yi masa domin wata rana zata iya zama so, kamar yadda Annabi Muhammadu (Slw) yafad'a *Comeent Vote and Share* [22/07, 02:06] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿56* Shiru tayi masa kawai, yace"muje in kai ki gida ki huta don Allah kar ki sake futowa waje,domin bana son rana tana dokar miki fuskarki mai kyau da kwarjini" murmushi tayi kawai, yana "yar dariya ya kunna motar suka bar gurin, kafin suka k'arasa gidansu Balaraba kira ya shigo wayarsa, yana dubawa yaga mutuminsa ne, a fili yace" aiki ya had'ani da wanda baya son jira,Gimbiya d'auki wayar nan"yafad'a cike da bada umarni,aiko batare data duba wanene yake kira ba, kawai ta d'aga wayar gami da kara ta a kunne, tayi sallama cikin siririyar muryarta mai dad'in saurare, gabanshi ne ya fad'i jin muryarta, sai yayi d'iff, sallama ta k'ara yi tana duba fuskar wayar a karo na farko domin taga wanene, Magajin Sarki! sunan da tagani kenan, tasan ko waye, tsaki taja ta zata kashe wayar, yace"ke ina me wayar yake,ne ke dashi duk kun zama shashashai, dallah bashi wayar zamuyi magana, kuma ki kuka da kanki gurin yi min tsaki, kinyi min sau biyu kar ki kar ki sake kiyi na uku, wani tsakin ta k'ara ja a karo na biyu, ta mik'awa Moddibo wayar batare da tace komai ba, k'arba yayi da hannu d'aya, d'ayan kuma yana tuk'i dashi ya kara a kunnensa gami da fad'in " ya a kayi ne, ganinan fa a kan hanya" "Kar Allah yasa kazo d'in" Sarki! ya fad'a da rai a b'ace! ya cigaba da cewa "an d'ora min nauyi duk a kanka, tun safe na kiran wayarka dan wulak'anci,kana min hanya-hanya sabuda kana tare da wannan mara kunyar yarinyar da in kayi wasa sai ta lalata ka, kaja mata kunne da kyau duk ranar da ta kuskura ta kuma yimin tsaki, sai nasa an d'aure ta a na tsawon kwana uku, ba budurwar ka ba,ko mecece d'inka bai dame ni ba sai ta d'auki hukunci,tunda kai so ya rufe maka ido kana gani tana abu na rashin kamun kai ka kasa tsawatar mata" yana gama fad'in haka ya kashe wayar yana wani irin huci! ji yake kamar yaje ya samu yarinyar ya koya mata hankali, ranar da suka fara zuwa gidansu shida Moddibo tayi masa tsaki, jiya tayi masa yau ma tayi masa uku kenan, mutukar ta kara wani to sai ta fuskanci hukunci, Babu Abunda Moddibo yace, kawai aje wayar yayi gefansa, Balaraba ta kalleshi cikin bacin rai tace"na lura kana mutuk'ar tsoran mutumin nan dubi irin masifar da yake maka a waya tamkar wani mahaifin ka, kayi masa shiru, bakace komai ba, gaskiya ka canza tsari, domin ina gani ko aure ma mukayi duk abunda yace da kai shi zakayi" ta k'arashe maganar tana zumb'ura baki, Ajiyar zuciya ya sauke dai-dai lokacin da yake parking d'in motar a bakin hanya, yace"kin kasa gane, Sarki! Gimbiya, na fad'a miki halinshi ne haka, yana da saurin d'aukar zafi ga muskilanci a cikinsa in ban dani babu da wanda yake sakewa, nine shi shine ni, shiyasa nake so ku samu fahimtar juna ke dashi, amma ina neman alfarma a gurinki don Allah" Ya fad'i maganar yana kallon ta sosai, ya cigaba da cewa"in banda kina da

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108