Chapter 45
Chapter 45
tana yi yace"lafiya lou alhamdulilahi" "Salihu yace " wai kana neman babanmu" "Eh hakane"? yafad'a ba tare da ya kalleta ba. " Bayanan amma bari in sanya yaro ya kira maka shi yanzu" tafad'a tana kokarin tafiya, sai wani murgud'a mazaunai take,wai dole sai ta burgeshi, Tare suka jera da Salihu domin futa bakin lungu ko zata ga Walidi ta tura shi ya kira baban nasu domin tana ganin wannan bak'on nasa na alkairi ne. Kanshi a kasa yayin da ya zuba hannuwansa duk biyun cikin aljihun jins d'in dake jikinshi,yana jimanta labarin da Salihu ya bashi a kan Balaraba, lallai in ko hakane yarinyar ba matar aure bace. kanshi a kasa ya fara jiyo wani mugun k'amshin turare mai dad'in gaske, d'ago kansa yayi, karaf! suka had'a ido ta cikin gilashin dake idonshi yake kare mata kallo, a kwai hasken fitala tunda da wuta lokacin, d'auke kanta tayi cikin izza! da tak'ama take tafiya, tana sanye da wasu riga da wando pakistan ta masu kalar blue da pink da adon wasu manya-manyan stons masu shek'i ta yane kanta da wani mayafi wanda ya sakko kad'an ya rufe mata k'irjin ta amma duk da haka ana ganin tudunsu, wandon ma duk da burgujeje ne,amma bai hana bayyanuwar sharp dinta ba, masu gigita lafiyayyan namiji kai har wanda ma bai cika lafiya ba, in ya kalli duri da k'irar Balaraba sai yayi sha'awa, shima da sauri ya kauda kai, ya d'an sosa kansa kamar yadda ya saba, yace"Jimana "yan mata" Tsayawa tayi tana shan k'amshi, gefe guda kuma tana tunanin a ina tasan wannan muryar. Cikin Yanayin tafiyar shi ya karasa inda take tsaye tana masa wani kallo sama sa k'asa,tana tab'e baki, har ya k'araso ya tsaya dab da ita, tayi saurin matsawa baya, tace"Lafiya Malama"? Gyara murya yayi ya k'ara yin k'asa da ita yace"amm" ina neman maigidan nan ne wanda kika futo daga ciki" D'auke kai tayi ta d'an turo baki gaba, tace"bayanan" tana fad'a tayi gaba,tana d'aga kai sama, as,usul "Ok yanzu a ina zan same shi a kwai abunda ya kawo ni, gurin shi" yafad'a yana d'an daga muryar shi sabuda tayi masa nisa kad'an. Tsayawa tayi tace"in zaka iya tsayuwa nan ka tsaya ka jira shi,yanzu zai dawo tunda tara tayi"ta k'arasa maganar tana k'okarin tafiya a karo na biyu, da sauri yace"d'an tsaya mana, "yan mata ai ban gama tambayar ba" Wani irin kallo ta watsa masa,wanda yasa shi saurin dauke kai, "wai me zan maka ne, uhum? ka tambaye ni na baka amsa,sai me kaga ina da uziri ni,yi sauri kafad'i abunda zaka fad'a in wuce abuna" Ranshi ne ya b'aci sosai! jin yadda take masa tsawa sai kace wani sa'an ta, lallai yarinyar nan baza ta canza ba, kanshi ya sosa kad'an yace"naji kince tara na dare tayi, ke ina zaki a matsayinki na "ya mace me kamun kai, babban abun mamaki ma kin ci uwar kwaliyya gami da turare mai dad'i me zai hana ki tsaya ki tayani hira kafin Baban yazo" Wanini irin kallo take masa,wanda kana kallonsa kasan ta shirya wulak'anci, a ya tsine tace"baka da hurumi a kan abunda kake tambaya ta,haka kawai daka ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i, aikin banza kawai ni natsani munafurci wallahi, ka tambaya an baka amsa ka tsaya neman magana" Wani irin d'aci-d'aci ya fara ji a bakinshi,tsigar jikinshi ta fara tashi, tunda yake a rayuwar shi babu "ya macan da ta tab'a ci masa mutumci irin wannan sai wannan yarinyar, Daure zuciyar sa yayi kawai yana bin ta da kallo, tabbas ya gazgata abunda Salihu ya fad'a masa yanzu a kanta Tun daga Nesa Shamsiyya ta hango Balaraba da Sarki! a tsaye, tamkar zata tashi sama haka ta k'araso gurin zuciyat ta tana tafarfasa, tace" ke dabbar Araf! mayyar maza, wato ke duk inda ki kaga namiji sai kin nuna masa ke karuwa ce ko, to bari kiji wannan da kike gani yafi k'arfin wallahi sai dai ki gani ki kyale, domin shi dai ba d'an iska bane irin ki" Shamsiyya ta karashe maganar tamkat zata tsone mata ido Abun mamaki sai yaga kawai Balaraba ta girgiza kai zata wuce ba tare da tacewa Shamsiyya komai ba, a zuciyarsa yace"wato wannan yarinyar rashin kunyar ta da rashin mutuncin ta akan mu yake" kallasa Shamsiyya tayi tana wani fari da ido ta jawo mayafin da Balaraba ta nannad'e kanta dashi Balaraba tayi saurin dafewa sanadin haka har sai da wayarta ta fad'i k'asa had'e da pose d'ita sabuda in ta cika, Shamsiyya zata iya cirr mata kuma babu hula zai ga gashin ta, Shamsiyya tace"kaga wannan wallahi kar ka yadda da ita,sai ta lalata ka, dan muguwar makira ce ta iya kissa da kisisina duk da haka takewa maza irin ku masu kud'i" A dake! yace"to ke wanene yace miki ni mai k'udi ne, sakar mata mayafi ta tafi" yafad'a a cunkushe, dan yaji haushin abunda tayi Balaraba ko meye dalili oho Sakar mata mayafin tayi tace"gayyar tsiya gayyar datti da najasa sai an dawo" Wuce Balaraba tayi bata kallon gabanta, sabuda tsanani b'acin rai, karo sukaci da Sallau ya shigo lungun yana baza babbar riga sai kace wani limami ya kalleta, a banza ce yace"wallahi in baki dawo da wuri ba zaki zo ki tadda mun kulle k'ofarmu domin baza mu tsaya jiran ki ba" yana gama maganar sho ya shige bagaz-bagan, Duk wad'annan maganganun da Sallau yayi kamar a gaban Sarki! yayi su dan yaji komai, haka Shamsiyya. *Muje zuwa* *Comeent vote and Share* [19/07, 22:49] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿54* Sai surutu Shamsiyya take masa, kanshi a k'asa sam baya k'aunar ya kalli fuskar ta, haka Sallau ya same su, jiki na rawa yace"barka da zuwa" D'ago kansa yayi a nutse ya kalli Sallau hannu ya mik'a masa yace"barka kadai Baba" Washe baki Sallau yayi yace"yan samari nayi mamaki jin cewar nayi bak'o,gashi bangane fuskar ka ba" Shamsiyya tana tsaye tana dariya tace"aikuwa nima nace bangane shi ba" Shiru yayi na minti biyu ya kalli Shamsiyya a ya mutse yace"d'an bamu guri, zamuyi magana ne" Yak'e tayi tana "yar dariya takama hanya zata huce Sallau yace" ai "yata ce in taji babu komai" bana buk'atar taji" yafad'a babu walawala a fuskar shi, wani kwarjini yayi wa Sallau sabuda haka sai ya kalli Shamsiyya yace ki shiga gida" Ko kunya babu ta shiga gida, sai ta mak'ale a soron gidan ta kasa kunne tana so taji, abunda ya kawo wannan guy addu'a take Allah yasa cewa zaiyi yana sonta, A nutse Sarki! yace"wani abokina ne yaga "yar gidan nan shine muke bukince a kanta, ance mana kaine mahaifinta" Washe hak'ura Sallau yayi yace"Eh duk "yayana ne, wacce kakw nufi a cikinsu"? " Balaraba" yafad'a kai tsaye Murtuke fuska Sallau yayi yace"wannan lalatacciyar yarinyar kake nufi, yanzu nan ta futa yawon bariki, ai inaji ma ka ganta wata gansamemiyar mara kunya" "Eh naga wata yarinya yanzu ta futa ko ita ce"? " Babu shakka itace, shawarar da zan baka shine kaje ka fad'awa abokinka ya janye maganar auran ta domin ba d'iyar arzik'i
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108