Skip to content

Chapter 106

Chapter 106

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

a yarin gidan sarauta tare da ayarin me girma governor suna jiran saukar jirgin su, Sha biyu dai-dai jirgi ya sauka Shahid da Shatima ne a gaba, sai Sarki! Da BALARABA a bayansu ya rungomo ta jikinsa, tuni gadawan gurin suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa, cike da kunya take k'okarin kwace jikinta ya ki s'akinta,cikin walwala suke gaisa da jama'arshi su Governor da Galadima da sauransu mota ta mussaman aka bude masa ya shiga ya zauna Balaraba ta shiga direba ya shiga domin su Kansu su Shahid wata motar daban suka shiga, direba yaja su suka nufi gida ***** Tsabar hayaniya jama'a tasa kansa ya fara ciwo nan take yace. da Babu direba su huce can shashen Maman shi, amma duk da haka jama'a bin motar suke suna banbadan ci tare da roko da kid'a kowa na fadin albarka cin bakinsa, Sarki ya futo cikin walwala ya dinga daga musu hannu ya rike hannun matar shi tamm!!fadawa suka dunga sanya duka da bulala da k'yar dai ya samu ya tattatka suka shige gurin Maman shi, wacce take tsaye gurin wani k'aton window tana ganin abunda yake faruwa, ganin yaron ta yayi kiba da lafiya gashi kamar ba Wanda ya tafi jinya ba,yasa ta godewa Allah sosai yana shigowa ya rungume ta, Balaraba ta koma gefe tana murmushi, Mama ta rik'o hannunta tana fadin"Zonan yarinyar ta hak'ika ke alkairi ce a tare damu kin zama Wani jigo na rayuwar mu, Balaraba ina jinki a cikin jinana tamkar nice na haifeki ubangiji Allah ya sauke ki lafiya." Balaraba tayi saurin sunkuyar da kanta cike da kunya, lallaima ashe sai da ya fadawa Mama halin da take ciki" Mama ta cigaba da cewa." Duk irin dawainiyar da kikayi da mijinki ina da labari, babu abunda zan iya saka miki dashi sai dai addu'a ladan ki na gurin Allah domin kinyi ibada kin bautatawa mijinki ubangiji Allah ya jikan iyayaenki yayi miki albarka a rayuwar ki." Balaraba ta sunkuyar da kai kasa tana amsawa da amin kwalla duk ta cika mata ido. Sadiya da Usuman ne tsaye can gefe suna kallonsu Mama ta kirasu tace." Kuzo ga aunty ta dawo,. " BALARABA ta daga Kai tana kallon yaran sunyi kyau sosai sun murje sun kara girma Sosai Mama take kula dasu, makaranta suke zuwa me tsada su saka suttura masu tsada babu. Shakka babu abunda zatace da Mama Fulani bisa alkairin ta a garesu. Nan b'angaran Mama suka biyo shi Halisa da Azima kowacce tana wace wannan gurin ado gwal sai walwali yake a jikinsu, Balaraba ta basu gurin ganin yadda sukeyi I junansu tamkar su bangaji juna,duk wannan k'awancan babu shi, kowacce ta kwaci kanta, Halisa duk ta kanainaye shi, a cewar ta ai girkin ta ne yau don haka duk su matsa gefe, shidai kawai kallonsu yake, yana tunanin halin da zai shiga zai kwana ba tare da gimbiyar sa ba, ya Riga ya saba da dumin jikinta da shagwaba shi da take sosai da soayyarsu duk dare, to itama b'angaran ta hakan take duk tayi sanyi tana tunanin ta yaya zatayi bacci bataji kanta a kirjinsa ba yana mata wassanin kamar yanda suka saba a saud'ia. *Daga wannan pege din sai na k'arshe Ku zauna cikin shiri*❤❤❤❤ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 *🅿115* Da k'yar ya samu ya kufce daga hannun Halisa ya gudu part d'insa inda su Shahid suke zaman jiransa,nan kama kafin ya tafi sai ya gargade su kar wacce ta bishi, saboda hutawa zaiyi Balaraba cikin zuciyarta tace." Dama ni ko ka neme ni ba zuwa zanyi ba, zama zanyi inyi jinyar zuciyata da zatayi kwana hudu ba tare da Kai ba. Nan gurin Mama suka zauna dukaninsu, kallon Balaraba sukeyi a fakaice ganin yanda tayi Wani mugun kyau, tayar ta kamar ka tab'a jini ya futo ta kara cika da kwarjini, wani kyashi da bakin ciki ya damu zuciyarsu babu abunda ya kara daga musu hankali sai yanda Mama take kula da ita, tana kaf-kaf da ita da tayi motsi zatace "Ya akayi in dai akwai abunda kike sha'awar ci kiyi magana akawo miki." Girgikai kai kurum take cike da kunyar Maman, Halisa ta kalli Mama da jiki a sanyaye tace." Bata da lafiya ne."? Murmushi tayi tace." Cutar ta arziki ce ai insha Allahu kun kusa samun baby." Ita da Azima ban San wanda yafi wani shiga rud'u da tashin hankali ba, neman miyau tayi ta rasa abakin ta, idonta ya ciko da ruwan hawaye, Balaraba na da ciki,cikin kuma na masoyinta Wanda taci burin ita zata fara Haifa masa 'yaya, to wai abun tambaya anan, shine mutumin da ya tafi Neman lafiya ta yaya har ya iya kwanciyar aure babban abun tambaya yaya akai shi da bashi da kafa ya sarrafa kansa. *Dariya nayi nace lallai Halisa kin cika hamaguwa😄* To tunani da take shi Azima take duk sun shiga tashin hankali Lallai BALARABA tayi musu fintinkau tayi musu zarra,yanzu meye abunyi? Halisa take tambayar zuciyar ta, wani b'angare na zuciyar tata Yace mata,kawai yau kema ki matsa masa yayi miki ciki ki haihu, aikuwa ta yarda da wannan shawarar ta zuciyar tata. ******* Walidi ne ya siyowa Shamsiyya atamfa guda biyu dinkakkau ya siyo rago ranar suna yaro yaci sunan mahaifin su,wato Sallau, Salihu kenan, a ranar ne kuma labarin Mabaruka ya same su, ta hanyar k'afafun yada labarai, an nuno ta kwance gadon asibiti babu k'afafu, ana cigiyar danginta harda Lamar waya aka kawo wa Walidi aikuwa atake ya kira wayar yayi musu kwantan inda suke, ba tare da bata lokaci ba aka sako Mabaruka a mota tare da keken guragunta tana kuka tana da tasani abunda tayi, Ranar kwana sukai kuka Iya da Sadiya matar Maman suna ta tausar zuciyar su. ****** Ana kiran idar da sallahr Isha'i Halisa ta dura a part din Sarki! Cikin shirin ko ta kwana, tayi kwalliya iya kwalliya, sama ta hau domin baya farlo,shima tunda su Shahid suka tafi ya hau sama domin ya huta, bude kofar tayi ta shiga bakinta d'auke da sallama ya amsa babu yabo babu fallasa, zama tayi kusa dashi, tana sak'e-sak'en maganar da zata yi masa, yace." Halisa mun same Ku lafiya ko."? Cikin dauriya tace." Lafiya lau Yallab'ai." Shiru yana sauraron ta yasan da akwai magana a bakinta, yace." Wane tanadi kikayi min."? Yake tayi kawai tace." Ni wane tanadi zanyi maka,nice ma Nazo kayi min tanada kamar yanda kayiwa Balaraba." Bai gane hausarta ba yace." Wane tanadi nayi Mata." Inda-inda ta fara yace." Ke nake saurare." Tace.'Nima ciki nake so kamun.' Cikin mamaki yake kallonta. Yace." Ciki Allah ne ke ba dashi ba mutum ba,

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108