Skip to content

Chapter 77

Chapter 77

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,224 words 0 views Progress saved
Download Book

duk abunda ta tacewa Sarki! Ya aikata sai ya aikata shi,domin baya tsallakewa umarnin ta. ****** Yau saura kwana uku d'aurin auran Sarki! shine dalilin da yasa gidan ya hautsine da shirye-shirye b'angaran Mama Fulani ma haka bayi sai shige da fuce sukeyi, Mama Fulani taso Sarki! Ya d'aga lokacin d'aurin auran sai bayan futarta daga takaba. Yace tayi hakuri kawai a d'aura yanzu burinsa kawai a d'aura auran ya wuce gurin domin sunyi magana da governor maganar zama a fada yace sai bayan auransa wannan zai fara zama domin shine cikar mutum, wannan magana da Sarki! Yayi itace ta kashe masa jiki, yasa ya hak'ura kawai,amma sam baya kaunar ganin Waziri kan kujerar mulki domin sam bata dace dashi ba. Halisa na keb'e a wani guri, a cikin gidan dai, Madabo da sauran " yan uwansu suna kula da ita tare da gyara mata jikinta sosai domin Madabo tace "yar baza tayi boranci ba,dole sai tafi sauran matan da zai aura shiyasa tasa ake had'a ta sosai To itama Azima tunda aka fara hidamar bukin ta tafi garinsu domin ta shirya tsaf, duk da yake ita kullum cikin shiri take Mamanta ma ba a zaune take ba. Su Shahid da Shatima ne suke fad'i tashi tare da shige da fuce, ganin ko wacce a bata hakkinta a kwatuna iri d'aya suka siyo irin me sha biyu nan, duk a bubuwan dake cikin d'aya a kwai a cikin d'aya,Kai dai-dai da kayan bacci iri d'aya suka zuba musu, takalma mayafai gasu nan birjik,gaskiya sun had'a musu kaya kamar hauka. Mama taji dad'in k'okarin dasu Shahid sukeyi domin in ta Sarki! Ne sai dai a d'aura auran babu lefe sam taga bashi ne a gabansa ba. " Yan uwa da abokan arzik'i Mama ta kira suka mik'awa ko wacce nata Balaraba dai nata suna gaban Mama,inda tayi-tayi da ita tazo ta duba kuma ta d'ibi wanda take so a d'inka mata Balaraba kunya duk ta hanata, haka Mama ta hak'ura ta kira Jakadiya Shafa'atu ta d'ibar mata atamfofi da lesuka masu kyau da tsada a ka kaiwa masu d'inki. Yanzu Balaraba bata futowa falo sosai, kullum tana d'aki a kulle indai ba Mama CE take kiranta ba bata futowa saboda wata irin kunyar ta da take ji,Su Sadiya kuwa ai sun zama "yan gari sun saba da Mama sosai hakanan Jakadiya Shafa'atu in zata wani guri sai ta tafi dasu domin suga gari. Shi kansa Sarki! Ya kwana biyu bai sanya ta a idonsa ba, daurewa kawai yake amma kwanakin nan yana yawan jin fad'uwar gaba idan ya tuna da ita,kasancewar shi mutum ne Wanda baka ganin damuwarsa sai ta kai ta kawo shiyasa lokaci guda baza ka fahimci halin da yake ciki ba. ********* Misalin hud'u da rabi na yamma Balaraba na zaune gefan gado tana duba wani k'aramin littafi irin na addu'oi, tana sanye da wata doguwar riga mai uban kyau da tsada rigar taji stone masu shek'i wuyanta da hannuta tayi amfani da k'aramin hijab irin me hulan nan fari k'al dashi, dai-dai kafad'arta ya tsaya, fuskarta tayi fayau sai annuri ne yake sauka, dama can ita wannan kwaliye-kwaliyen bai dame ta ba,ko Wanka tayi k'ark'ari ta shafa mai sai hoda,da kwalli sun ishe ta, amma fa akwai son k'amshi jidin jikinta na k'amshin turare. Sadiya ce ta shigo da saurinta tana fad'in "Yayarmu kizo inji Mama,wai zaki kaiwa Magajin Sarki! Abunci yana zazzab'i" Balaraba gabanta ya fad'i jin abunda Sadiya tace, tace"Wai ke ba na hanaki rashin kamun kai ba, don Allah dube ki sai wani rawar jiki kike yi" Sadiya ta sunkuyar da kanta tana jin tsoran fad'an yayar tata. "Karki k'ara shigowa babu sallama kuma ki daina wannan gudun da kikeyi" Sadiya tace "To" Ajiye littafin tayi kan gadon ta mike tsaye tana gyara zaman hijab din nata,tace"Yana ina ne Magajin Sarkin"? "Yana shashensa tare da abokansa,muma bamu dad'e da dawowa ba ni da Usuman tun d'azu muna can" Ita fa bata son zuwa shashensa gudun abunda ka iya zuwa ya dawo ta lura wani irin mutum ne shi, me saurin tab'a jikin mace ko haka yakewa sauran matan oho shi dai ya sani, amma dole zata kiyaye ta daina sakar masa jikinta. _Niko nace Balaraba kenan maganar sakin jiki ta k'are tunda an kusa d'aura aure_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ ______________________ *Tsokaci* ______________________ *_Tun farkon farawa na fad'a cewa ban rubuta littafin Gimbiya Balaraba domin in ci zarafin wani ko wata ba, ku wani jinsi mutum me k'iba ko siriri, wannan labarin k'agaggene daga ni, Binta banga dalilin da zaisa kawai in ci mutum cin wani jinsi ba,kamar yadda wata "yar uwa ta fad'a min, Asali ma, wannan jinsin mutane da take magana akan su ina cikinsu to kun gani idan naci musu fuska har dani a cikinsu, Allah da kan shi ya hallici d'an Adam kuma ya karrama shi, duk a cikin hallitunsa ni Wacece da zanyi ciwa hallitar Allah fuska,, labari ne kawai saboda haka don Allah mu San abunda zamu dunga fad'a akan " yan uwanmu_* *🅿89* Mama Fulani na zaune a falo ita da Jakadiya Shafa'atu suna hirarsu cikin mutun ta juna.Balaraba ta futo a nutse ta k'araso inda suke ta tsuguna tana gaishe da Fulani. Cikin "yar fara'a Mama Fulani ta amsa, tace" Dama nace Sadiya ta kira ki kaima Mutumin ki abunci yana can shashensa tare da abokansa su Shahid,watak'ila ya fi maida hankali yaci abuncin, tunda bashi kad'ai bane" Cikin jin nauyi gami da kunya Balaraba tace"Mama Sadiya tace bashi da lafiya yana zazzab'i"? "Ba wai bane, da gaske ne, yau ya tashi da zazzab'i amma dai yanzu nasan jikin da sauk'i tunda d'azu ma ya shigo mungaisa" Balaraba ta mik'e tana fad'in Allah ya sawak'e, Mama ina abuncin yake"? Can wani katafaran gurin cin abunci ta nuna mata tace "Kije ki had'a masa,amma yace nacin mutum uku za'a had'o in yaso in kika gama sai ki kira d'aya daga cikin " yan matan dake aiki a waje ta d'aukar miki' Balaraba tace"To ta mik'e ta nufi gurin cin abincin. A nutse ta had'a masa komai yadda yace d'in, Mama tasa Sadiya ta kira wata baiwa me suna Lahira ita tazo ta d'auki kwandon abincin suka futa tare da Balaraba. Tun washe garin rasuwar Maddibo rabonta da b'angaransa shiyasa yanzu da ta shigo taji gabanta yana fad'uwa tunowa da tayi da rayuwarsu da Moddibo wasu hawaye ne masu zafi suke k'okarin zubo mata, ta fara k'okarin mai dasu,,. Wasu k'yatattun takalma ta gani a bakin k'ofar shiga falon, kuma tana d'an jin magana a ciki, sai ta gyara yanayin ta,ta koma Balaraban ta ta asali, cike da jarumta tayi sallama ta shiga falon, Rahila na biye da bayanta. Yana kishin gid'e cikin wata shirgegiyar kujera,me kamar k'aramin gado da wasu k'ananun fililluka a kai, daga shi sai boxar da k'aramar shart me k'aramin hannu,abunda yasa yayi wannan shigar saboda jin jikinsa ya d'auko zafi gumi sai zuba yake,dalili yasha maganin zazzab'i shikkenan gumi sai karyo masa yake ko ta ina,shine

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108