Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,249 words 0 views Progress saved
Download Book

sha shida, bakwai mata sauran duk maza ne, matanshi hudu ko wacce tana da " yaya dashi, Waziri mutum ne shi mai bala'in san mulki sosai domin ji yakeyi tamkar ya kwace sarautar daga hannun dan uwanshi,kullum burinshi da kokarinshi yaya za'ayi taga sarautar ta dawo hannunshi, shida iyalinshi,shiyasa da yaga Maimartaba bai haifi da namiji ba,sai hankalinshi ya kwanta, yana jiran ranar da Maimartaba zai kwanta dama,ya gaje sarautar tunda shine namiji,cikin hukunci ubangiji Allah ya azurta Maimartaba da haihuwar Sarki!Almansor, in da ya zamo daya daya kwal cikin "yaya mata goma sha bakwai shi ya zama cikin na sha takwas, lokacin waziri kusan zaunce wa yayi,ya dinga shige sa fuce gurin ganin ya ga bayan Sarki!Almansor, Allah bai bashi iko ba,dan duk wani kulunboto da yake shiryawa sai ya koma kanshi ko kan iyalinshi,duk rabi" yayanshi maza sun zama "yan shaye-shaye in ka cire, Yusuf(Maddibo) duk ciki shine nutsatstse a cikinsu,shiyasa suka fi shiri da Sarki!Almansor kusan a tare suka yi makaranta komai iri daya suke sawa, duk inda daya yake dayan ma ba gurin, halayyarsu ce kawai bata zo daya ba,inda Sarki Almansor ya kasance mugun muskili wanda magana take masa wahala,sai ya kwana ya yini bai kula kowa ba har in dai ba kamawa tayi ba,shi kuwa Maddibo mugun saukin kai ne dashi gami da wasa da dariya, in ka ganshi sam baza kace yana da alaka da gidan sarauta ba,sabuda da kowa mu'amala yakeyi,babba da yaro, Tsakaninsu basa boyewa juna sirri duk abunda ya dami daya daga cikinsu, tsakaninsu suke warware matsalar basa taba yadda maganar ta futa waje, shiyasa kai tsaye Maddibo shi ya fara kawowa maganar Balaraba, Kiranshi da suna Sarki! da mutane keyi na gida da jama'ar gari ya samo a sali ne daga gurin mahaifinshi,shine take kiranshi da sunan tun yana yaro in yaga yana wata irin tafiya cike da kasaita, ko cin abuncin sa abin kallo ne,balle yadda yake magana, Yadda Maimartaba ya fuskanta abin a jininsa yake, shi kanshi yaron ya san ya fishi kasaita, shine dalilin da yasa yake kiranshi da sunan, mutanan gida suka kama hade da jama'ar gari Halisa kuwa " yar kanwarsu ce wacce ta kasan ce autarsu wato Fulani Mariya maca ce mai mutukar kirki da sanin ya kamata sam bata kin talaka kullum cikin jawo jama'a take gidanta, tana can tana auran sarkin garin Wani gari jaja Amare, tun Halisa tana yarinya rikonta ya dawo hannun, me babban daki, wato Uwargidan Sarki, ta hada da "yayan ta ta rike kamar gaske, tun ta so warta take mutuwar son Sarki!Almansor, tun tanayi a boye har abu ya fito fili kowa ya fahimta,har maimartaba, nan kuwa Me babban daki ta tsaya kai da fata tace lallai dole ne a kulla wannan al'amarin domin dorewar zumunci, Maimarta ba ma ya nuna yaddarsa, a kan al'amarin, Shi kuma wanda ake domishi ya nuna bayaso da kyar dai mahaifiyarshi ta lallabashi ya dadda gudun bakin mutanan gari *Wannan shine kadan daga cikin tarihin abunda ya faru a baya* *Cigaban Labari* Da asubah Maddibo yasa drevar ya futa dashi suka shiga kasuwar sha tambaya,can gefan titi yasa drevar yayi parking din motar, yana kwance cikin motar yana kallon masu shigowa cikin kasuwar duk da cewa safiya ce, Wajan karfe takwas da rabi ya hangi Napep din Ashiru Balaraba na kokarin fitowa daga ciki yau tana cikin wata irin doguwar riga baka " yar saudia rigar taji adon duwatsu sosai da sosai tayi nan nade kanta da veil kafarta sanye da wani takalmi mai tsayi mai igiyoyi,sai ta kara tsayi sosai takalmin shima baki ne sosai kafarta tayi kyau a cikin talakmin hannuta rike da wayarta da wata "yar karamar pose ta tsaya suna magana da Ashiru Maddibo kuwa suma ne kawai bai yi ba lokacin da ya hangi fitowar ta sai ajiyar zuciya yake saukewa, yana wa Allah tasbihi cikin zuciyarsa yace" tabbas Allah ya aje baiwarsa gaskiya yarinyar ta hadu sosai, dole maza su rika rikice wa a kanta, in da take burgeshi , kamun kai da rashin kwadayi gami da dogaro da kai shiyasa duk abunda a ka fada masa a kan ta yake kauda kai,sabuda yana ganin babu mahalukin da ya isa ya hanashi auranta, Ya na can yana tunani Ashiru yaja Napep dinshi ya na kokarin hawa titi,can ya hangoshi, da sauri ya bawa drevar Umarnin bin bayanshi duk in da ya nufa. *Muje zuwa* [30/06, 04:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ† _*GIMBIYA BALARABA*_ βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ† πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» _*Na*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani Writes Association🀝🏻 ```Bisimillahir rahamanir rahim``` *πŸ…Ώ34* Sosai Ashiru yake gudu a kan kwalta,kasancewar babu cinkoso sosai na ababan hawa, sauri yake shima ya isa gurin aikinsu, kawai sai yaga katuwar mota ta tari gabanshi, sai ya rage gudu, ya fara tafiya a hankali gabanshi yana faduwa! Cikin sauri drevar dake jan Maddibo ya yi parking din motar gefan titi ya fito,yana dagawa Ashiru hannu. Ashiru ya tsayar da Napep dinshi ya fito daga ciki duk hankalinshi a tashe,ganin mutum sanye da wasu manyan kaya ja da baki kanshi nade da wani katon abu,yana gani ya fahimci daga gidan sarauta ne, Hannu ya bashi suka gaisa yace"Yallabai ne yake son yin magana da kai" Jiki na rawa Ashiru ya bi bayan dravar suka karasa inda yayi parking din motar, Maddibo ya mika masa hannu fuskarsa a sake yace"barka da asubah" Cikin dari-dari Ashiru ya mika masa hannu sukayi musabaha da juna,kana yace"barka dai yallabai,fatan katashi lafiya" "Lafiya kalau Abokina" Maddibo yafada fuskarshi dauke da murmushi ya cigaba da cewa"in baza ka damu ba inaso in nemi alfarma a gurinka" Jiki na kyarma Ashiru yace"babu damuwa Yallabai" "Masha Allah, Menene alakar ka da Balaraba"? Cikin rawar baki yace" babu wata alaka a tsakaninmu kawai ina kaita bakin kasuwa kullum" "Ok shiga muje ka nuna min gidan su" Maddibo yafada babu wata damuwa a tare dashi. Ashiru duk ya rude yace"Yallabai Allah dai yasa ba wani abun tayi muku ba,sabuda na fahimci bata kaunar Sarki!Almansor, in wani abu tayi muku, ku gafarce ta dan Allah, Balaraba marainiya ce bata da uwa babu uba,kusan itace take daukar nauyin gidansu" Ajiyar zuciya Maddibo ya sauke, wani irin tausayin Balaraba yana ratsa zuciyarsa. Yace"Babu laifin da tayi mana, alkairi ne zai kai ni gidansu,ka kwantar da hankalin ka" Da kyar Ashiru ya je ya gyara parking a gefan titi kana ya sanya key ya kulle Napep din nasa, ya shiga motar suka kama hanya har unguwarsu Balaraba. Sosai Maddibo yayi mamakin irin unguwar da Balaraban shi take rayuwa, wani irin lukuna masu dauke da dagwalan katoci ku ina kwata tabi hanya abun babu kyawun gani, hankalinshi bai kara tashi ba ma sai da yaga lokwan su Balaraba,mai tattare da tarkacan, kayan gwan-gwan ko ina gasu nan wasu a daure a buhun-huna wasu kuma a washe a hanya, in ban da wari babu abunda yake tashi a gurin, Kasa shiga ciki yayi sosai ya tsaya daga baya, Ashiru yace"Yallabai ga gidan can, in da waccan budurwar take soya a wara to nan ne gidansu" Yara ne suka fara taruwa a gurin suna kallon Maddibo,wasu na rugawa gida da gudu suna fada cewa ga Sarki yazo, ai tuni Yara suka cika gurin,kasancewar Safiya ce wasu

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108