Chapter 78
Chapter 78
fa yayi Wanka ya sanya k'ananun kaya,yazo ya ware AC har suna rigima da Shatima saboda k'arfin AC d'in yayi yawa,shi kuma yace ya rabu dashi haka yake so. Hira suke irin ta abokai Sarki! Yana daga kishin gid'e yake sa musu baki, zumbur! Ya mik'e da sauri ya nufi tv memory ya zura jikin DVD ya kuna sai gasu shida Maddibo sun bayyana jikin faskekiyar TV plasma dake manne jikin bango, suna zaune cikin makaranta a can america new york, can sukai karatunsu, wani abokinsu ne me yawan yi musu photo da vidio, ranar dai Sarki! Ya samu memori ya bashi yace duk sanda suke zaune shida Moddibo suna karatu ko suna wani abun Ku suna hurawa to kawai ya dunga d'aukar su a hota ko yayi musu video aiko Ashir baya gajiya mutuk'ar yana kusa idan yagansu sun keb'e kawai sai ya ciro memori a zura a wayarsa yayi tai musu hotuna had'e da video. Shahid da Shatima duk sun rud'e ganin Moddibo jikin tv kamar kayi masa magana ya amsa,kai wannan duniyar abar tsoro ce. Balaraba na shigowa idanunta suka sauka akan fuskar tv Moddibo tayi tozali dashi yanai wa Sarki! Magana yana dariya Kwandon da yake hannuta ta saki ta k'wala k'ara jikinta ya fara k'arkarwa, "Inallahi wa'ina ilahi raji'un" Jin gina tayi da bango tana sauke a jiyar zuciya bakinta sai motsi yake. Dukaninsu kallon ta suke sosai saboda ba suji lokacin da ta shigo ba, sai ihunta da sukaji Shahid ya zubawa fuskarta ido yana tunanin a ina yasan fuskar tabbas yasan me wannan fuskar Shatima kuwa gulma yake son yayiwa Sarki! Sai ya lura babu fuska yaja bakinsa yayi shiru,amma fa bakinsa da akwai magana, domin yana kokwanton anya ba wannan ce,Balaraba da yaji Mama tana yawan ambatar sunanta ba. Tv take kallo babu k'iftawa wasu hawaye masu zafi suna biyo kumatunta. Maddibo ne yake magana tamkar ta kirashi ya amsa mata. In banda sautin kukan Balaraba babu abunda yake tashi a falon, Tsura mata ido yayi babu k'iftawa, wato har yanzu yarinyar nan bata far kukan mutuwar Moddibo ba kenan,a ganinsa ta shigo musu babu sallama kuma tazo tanai musu kuka babu gaira babu dalili. Shatima ne da ya fuskanci kukan me take ya tashi da sauri yaje ya kashe tv d'in ya dawo ya zauna yana mamakin ta. Shahid ne ya mik'e ya k'arasa inda take tsaya ya fara rarrashinta da kalmomi masu sanyaya zuciya, ya jima yana tausar zuciyarta sannan tayi shiru tana share hawayen ta, k'okarin futa take ba tare da tace musu komai ba. Shahid yace"Ranki ya dad'e ai baki bamu abuncin ba, zaki futa kuma bamu gaisa ba, ya kamata kizo ki duba mutumin naki kafun ki futa" Shahid yana da k'ima da mutumci a idonta, ta lura yasan abunda yake, kallonsa tayi babu yabo babu fallasa ta gaishe ya amsa fuskarsa a sake, tare suka jera suna tafiya har cikin falon. D'auke kansa yayi daga kansu, yarinyar yau tayi masa kyau sosai tamkar wata balarabiyar k'asar saudia shigar tayi mata kyau, yana so ya ga mace na suturce jikinta. Hannuta rik'e da kwandon abuncin ta nufi gurin cin abunci,shi kuma Shahid ya zauna kusa da Sarki! Suna magana k'asa-k'asa. Mik'ewa yayi yana mik'e duk jikinsa ciwo yake masa, Tashi sukayi suka bi bayan sa. Tsaf! Ta had'a musu kowa da plate d'insa, ta kalli Shatima da yake satar kallonta sosai yarinyar tayi masa kwarjini da yawa. A nutse tace"Ina wuni"? Shatima ya amsa da sauri sai murmushi yake yace"Lafiya lau amaryar mu, yo ke haka ake daga shigowa sai ki fara kuka uhum"? Shiru tayi tana satar kallon Sarki! Da yake juya abunci da alama yunwa yake ji, tunda yake Neman abunci da kansa, tarasa wani irin mutum ne shi da baka gane gabansa da bayansa fuskarsa a sake take amma ko da wasa yak'i kallon inda take, abuncin sa yake ci kawai, su Shatima sun rik'eta da suturutu ita kuma tana ta k'okarin yaya za'ayi ta gudu domin mutuminta da yayi mata wani mugun kwarjini gashi tana so ta gaidashi amma babu fuska. Da k'yar dai tace" Barka da yamma"? Shiru gurin yayi su Shahid suna kallonsa sun san da shi ake" Lumshe idonsa yayi ya cigaba da cin abuncin sa, bai amsa ba. Shatima yace"Ana magana fa" Da gefen ido ya kalleta ya d'an tab'e bakinsa yace" Naji ai bazan amsa ba, tunda duk sai da ta gama wulak'ancin ta sannan" Shatima yace"Amarya ce fa kasan amarya bata laifi komai tayi dai-dai ne" Wani irin kallo yayi mata me d'auke da ma'anoni daban-daban yayi wani murmushi irin na gefan baki,yace"Ai ba ita kad'ai gare ni ba, Anjima kad'an nasan Halisa nan tafe,kaga kuwa ai bazan damu ba" Balaraba sarkin d'aukar zafi! Fuska ta turb'une duk idanta ya rufe,wani kallo ta watsa masa,suka had'a ido dashi, tsaya wa yayi yana mamakinta, wani irin Abu tayi da idonta ta kalli su Shatima muryar ta a cunkushe tace"Ni zan wuce ku tashi lafiya" Sauka tayi daga kan step d'in ta fara tafiya a nutse zuciyarta duk babu dad'i ta lura Sarki! Zuma ne shi ga zak'i ga harbi,dubi yadda kwana ki ya dunga lallab'ata har tana yi masa d'aukar mutum me saukin hali a she ba haka bane,wannan halin nasa nan, halin wulaknci da raina mutum,yo ita ina ruwanta ko mata dubo zai aura a rana d'aya ba damuwar ta b'ace,shine bai sani ba ita tafi sha'awar zamanta a haka tunda tayi rashin babban masoyinta Modiibo. Shatima yace"Allah ya huci zuciyar gimbiyar mata, ai dukaninsu kin sha gaban su, kar ki manta ke fa amanrmu muce,bayan haka kuma kina da babban matsayi a zuciyarmu ki kwantar da hankalin ki. Ko waigo wa batayi ba, ta bud'e Kofa tai fucewarta Rahila na tsaye na jiran futuwar ta sai ta take mata baya. Shahid yace"Lallai addu'a ta ta karb'u, wannan yarinyar ba itace wannan yarinyar da sukayi saukar alk'urni shekaru biyu da suka wuce ba"? D'aga kansa yayi kawai. Shahid yace"Allah sarki Moddibo Lallai na yarda zuciyoyinku d'aya duk abunda kuke so iri d'aya ne,Allah bai hukunta zai aure ta,ba sai ya kawo maka ita har gida" Shatima yace"Ni wallahi abunda kayi mata ne ya bani haushi da alama yarinyar tana da hankali da nutsuwa,kawai sai ka ci mata fuska, kasan dole taji babu dad'i a zuciyarta. 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿91* Balaraba tayi k'asa da idanunta domin baza ta iya jurar had'a ido dashi saboda kwarjini da Allah yayi masa. Niyar koma dakin take, yayi gyaran murya tsayuwa tayi. Ta d'an waiwayo suka had'a ido lumshe nasa yayi ya bud'e baki a hankali yace"Jimana" Sak tayi jin abunda yace wai jimana! Sai kace Wanda bai san sunanta ba. Ahankali ta taka ta k'arasa inda yake zaune, mik'ewa yayi yana gyara zaman sa,idanunsa a kanta, ita kuma tana tsaye gefansa duk jin ta take a takure, sai gyara fuskarta take. "Zauna zamuyi magana dake" Cikin k'asaita gami da jan'aji ta zaune kujerar gefansa. Cikin bada umarni yace"Ki dawo wannan domin maganar da zamuyi dake tanada muhimanci" Kujerar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108