Skip to content

Chapter 52

Chapter 52

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

rarrashin ta, in bata zauna wa ka kyaleta kawai malam taje duk inda zata je, dama ta saba" Moddibo ya d'an harare shi,bai ce masa komai ba ya mayar da hankalinshi kanta yana rarrashi, Wa d'annan yaran fa? a sharad'in mu dama a zata zo min da yara ne"? yafad'a yana binsu Sadiya da kallo. Moddibo yace" Yan uwanta ne,itace uwarsu itace ubansu,zata zauna tare dasu insha Allah ko aure mukai muna tare dasu. Tab'e baki yayi ya mayar da kansa k'asa yana duba littafin hannunsa. Da k'yar Moddibo ya rarrashe ta,tare ta bishi sama, tare da sharad'in gobe zai canza mata gurin zama, sai da ya tabbatar da ya kwantar mata da hankali sannan ya sauko k'asa cikin sauri ya nufi k'ofar futa, ko kallon Sarki! baiyi ba, saboda ya bashi haushi d'azu abunda yayiwa Gimbiyarsa bai dace ba, Tab'e baki yayi kawai ya cigaba da abunda yake, yananan zaune Moddibo ya dawo hannusa nik'i-nik'i da manya-manyan ledoji, kamar yadda ya futa bai kulashi ba, haka da ya dawo kai tsaye sama ya nufa, inda Balaraba take. Wajan minti ashirin ya sakko, yazo ya zauna kusa dashi ya dafe kansa da hannu guda yana sauke ajiyar zuciya, Shareshi yayi shima tsawon minti goma babu wanda yace da d'an uwansa k'ala, Cikin jan nuffashi Moddibo yace"wallahi narasa wane irin hali ne da kai, kafin in kawo yarinyar nan sai da nafad'a maka kuma ka amunce, kan me yasa zaka ci mata mutumci, kowa ai da koyo ya iya,gaskiya banji dad'in abunda kayi mata ba" Kamar da dotse yake magana yana jinsa yayi shiru. K'wafa yayi kawai yana duba agogon hannusa yace"yanzu dai gata can babu abunda zata nema,komai na siyo mata in tsautsayi yasa ta sakko don Allah babu ruwanka da ita" Hankalinsa na kan littafin hannunsa yace"sai ka fad'a mata nima babu ruwanta dani, haka kawai ni da gidana anzo ana kafa min doka" " In dan ta ita ne sai ku shekara bata shiga harkar ka ba, nasan halin kowa a cikinku" Aje littafin yayi yana wani murmushi mai d'auke da ma'anoni daban-daban ya fuskaci Moddibon sosai yace"wai dakata malam har tsawon wane lokaci ka d'auka zatayi anan, inaji fa kayi mata alk'awarin gobe zaka canza mata guri, kazama me baki biyu kenan"? " Wannan kuma kai za'a tambaya tunda wuk'a da nama na hannunka, dole ne in kadamu kaje ka k'arasa bunkice a kanta idan kuma ka gama shikkenan sai kaje kasanar da me Martaba halin da ake ciki" " Ni tuntuni nagama bunkice na a kanta kuma nafad'a maka, amma tunda kace haka insha Allahu gobe zan sanar masa da halin da ake ciki" yafad'a yana d'an jan numfashi sannan ya cigaba da cewa" Yanzu wane amsa zaka bawa me Martaba in ya aika gidansu yarinyar nema maka auranta, a kaji cewar tana hannunka ka b'oye kana da amsar da zaka kare kanka"? "Duk wannan me sauk'i nr tunda kafin in d'auko su sai da naje na sanar da me gari, yasan halin da ake ciki, kuma a ranar yace zai aika a kira masa shi me unguwar da aka had'a baki dashi da wan mahaifin nata Sallau, wata k'ila kana iya ganinsu gobe a fadar Sarki" "Shikkenan Allah yasa haka shi yafi alkari, Allah ya baku zaman lafiya" "Ameen ameen" Moddibo yace cikin jin dad'in addu'ar da d'an uwan nasa yayi masa, hira suke sosai irin tasu, Sarki! yace"gobe da misalin k'arfe hud'u na yamma Gimbiya Azima zata kawo min ziyara" Murmushi Moddibo yayi yace"kace muna da manyan bak'i" Ya mutse fuska yayi kawai bai ce komai ba. Moddibo yace"wai Halisa tasan halin da ake ciki kuwa? ma'ana tasan su biyu zaka aura lokaci guda" Wani murmushi ya saki cikin k'asaita yace d'azunan muka gama rigima da ita anan,sai da nayi mata fata-fata sannan ta shiga hankalin ta kasan halina sarai bana son shirme" Cikin dariya Moddibo yace"gaskiya ne, rigimar Halisa babu mai iyawa da ita sai kai, wai don Allah yanzu ka fara sonta kuwa, na lura kai sam ba'a gane cikinka ko kana son abu baka nunawa wai saboda me"? Cikin yanayin maganar shi yace"kowa an fad'a maka irinka ne, da kake haukacewa kan mace, duba don Allah shiriritar da kake kan wannan kidahumar yarinyar wacce ko hankalin ki kirki bata dashi, ka zubar da girman ka ta gani, d'azu dakana bata hak'uri ji nayi kamar in tsinka maka mari dan haushi wallahi" Dariya kawai Moddibo yake kyak'yatawa yace"malam bakasan dad'in soyyaya bane shiya kake wannan maganar, ina ganin in kane kuka ma sai kayi da dai ban san halinka bane shiyasa nake tambayar ka yaya kakejin Halisa a zuciyarka, dan gaskiya ni ina mutukar son Gimbiya ina tunanim zan iya rayuwa da ita ita kad'ai" Sarki! yayi masa wani kallo a d'age yace"wannan tsarin ka ne, malam ni babu wata "ya mace da zanyi wa kuka a kan me, me zata bani? wallahi kuna bani mamaki, wai me kukeji ne in kuna rawar jiki akan mata, soyyayar banza duk shirme ce ni aganina" Girgiza kai Moddibo yayi yace"gwara da kace kai a ganin ka, amma ina nan ina addu'ar Allah ya nuna min lokacin da zan ganka kanai wa mace "yar murya ni nasan komai daran dad'ewa wannan lokaci sai yazo *Turka!Turka* ```WAI SARKI!! NE?``` *KO* ```MODDIBO NE?``` *Muje zuwa* *Comment Vote anda Share* [25/07, 16:36] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿60* "Lallai kuwa ashe zaka sha zama in har zaka tsaya jiran wannan lokacin da kake, fad'a, aini ko ina son mace bata isa in nuna mata ba, zahiri sai dai ta gani a ai kace, kai dai da kaga zaga iya kaje kayi" Moddibo ya mik'e tsaye da niyyar tafiya, da murmushi a fuskar sa yace"wannan ciki bakin naka yana bani mamaki, amma dai zamu gani ai" Hannu ya bashi sukayi sallama, ya futa. Shi kuma kusan rabin kwana yayi a farlon nasa yana karance karance sai wajan uku shaura ya mik'e ya haura sama, toilet ya nufa ya d'auro alwala yayi nafila kamar yadda ya saba, yayi addu'oin sa, sai jingina jikin bed d'insa yana jsn carbi, bacci ya soma fuzgarsa, cikin bacci ya dinga jin motsi, kad'an-kad'an a bardar saman sa, mik'ewa yayi a nutse ya bud'e window yana duba gurin, Sadiya ce a takure a k'ofar d'akin da suke ciki ta bud'e ta futo ta tsuguna ta takure kanta cikin gwiwa jikinta sai rawa yake. A nutse ya bud'e k'ofar d'akin nasa ya futo yazo ya tsaya kan yarinyar, sam bata san ma yazo gurin ba, kallon cikin d'akin yayi haske tarr! da yake basu kashe futila ba, can ya hango Balaraba kan bed tana ta bacci abunta, gashin kanta duk ya hargitse, ga sharab'ar ta duk a waje, kasancewar riga da wando ne a jikinta irin cotton d'in nan rigar me dogon hannu ce tana da botora shi kuna wandon iya gwiwa ne, shiya duk wasu sassan jikin nata suke waje, sauri d'auke kansa yayi yana d'an ya mutse fuskarsa, ya mayar da idonsa kan Sadiya, cikin murya mai sanyi yace "Kee" Da sauri yarinyar ta d'ago kanta tana kallonsa

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108