Skip to content

Chapter 59

Chapter 59

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,247 words 0 views Progress saved
Download Book

Yace"Magajin Sarki ya labarin bunkicen da nasa kayi min kan wannan yarinyar dake zaune kusa da kai" Cikin yanayin maganar sa ya ce"Allah ya baka nasara, a gafarce ni, nayi laifi saboda banzo na fad'a maka komai ba yau tsawon kwana biyu kenan, dama yau nakeso inzo in fad'a maka sai ga shi ka aiko,tuba nake ranka ya dad'e" Galadima yace"me Martaba ya karb'i uzirin ka" Moddibo ne ya kalleshi yana masa magiya da ido,dama kafin su futo sai da ya dunga lallab'ashi Sarki! yayi gyaran murya a nutse yace"Allah ya taimake ka nayi bunkice sosai nagano wannan yarinyar bata da wani aibu yarinya ce me ladabi da biyayya da bin nagaba da ita,nayi bunkice sosai duk wani sharace-sharace da ake mata basu da tushe,anayi ne domin ganin tana futa kullum gurin sana'arta,wannan shine abunda na sani a game da ita, Ya karasa maganar cikin nutsuwa. Shiru na minti biyu me Martaba yayi gyaran murya hankali kwance yace" Nayi farin cikin jin wannan abu, wannan yarinyar tun kafin in ganta hankali na ya kwanta da ita,in sha Allahu tana tare damu ita da "yan uwanta, ni ne zan shige mata gaba,kan lamarinta, a yanzu yanzu zan d'aura mata aure da Yusuf Moddibo, saboda na yaba da nagartarsa gami da jajircewar sa kan lamarin ta, wannan shine hukuncin da na yanke" "Alhamdulilahi-Alhamdulilahi, Abunda Moddibo yake ta fad'a kenan cikin zuciyarsa, Balaraba ma taji dad'in yadda abubuwa suka zo da sauk'i haka, duk wanda yake zaune a fadar yayi murna da wannan abu,in ka cire mutum biyu wato Sallau da Waziri Zayyanu, Nan me Martaba ya umarci maga takarda da ya futa ya sanar a cikin gida,sannan ya tawo da goro da Alawa domin, cika al'k'awarin da ya d'auka. Shiru fada tayi bayan futar maga takarda,kowa da abunda yake sak'awa cikin zuciyarsa,kawai sai sukaji muryar Waziri Zayyanu cikin fushi!yace" wannan hukunci da me Martaba ya yanke bai yi ba, domin ni ne nake da hakki a kan yaronan don haka ban amunce ya auri wannan yarinyar ba,in ko ya aureta zai had'u sa fushina! *Tofaaaaaa!* *Fans kuna ina ne wa ya dace Balaraba ta aura, shin me zai biyo baya in me Martaba ya d'aura auran Moddibo da Balaraba, shin wane irin rikici ne zai faru kan hakan, yaya su Lantana zasuji jin cewar Balaraba tayi aure gidan sarauta, shine wanene mijin Balaraba???* *SARKI! NE KO MODDIBO?* [05/08, 00:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` _BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_ *🅿67* Shiru fada tayi ana kallon kallo abunda Waziri ya fad'a ya girgiza jama'ar dake gurin. me Martaba bai tab'a yanke hukunci ba, a samu wani wanda zai ce be yi dai-dai ba, kowa yana jiran yaji abunda me Martaba zai ce, shiru yayi kawai yana jin damuwa da b'acin rai a zuciyarsa yau Waziri ya nuna masa cewar d'anshi Moddibo bashi da iko a kansa aure tunda ya riga ya yi niyyar d'aura shi a yanzu sai ya d'aura shi, saboda haka duk abunda Waziri yaga zaiyi yayi, yanzu yana sauraron dawowar maga takarda ne. Mik'ewa Waziri yayi ya futa, ba tare da ya yiwa kowa sallama ba, me Martaba yaji ciwon abunda d'an uwansa yayi masa,amma sai yayi shiru kawai. Mintuna goma da futar Waziri sai ga maga takarda nan ya dawo, yana tare da wani bawa a bayan shi, yana d'auke da d'aurin goro da kwalin alawa, Galadima ne ya matso ya kwance d'aurin goron da alawa, kansa a kasa yace"Allah ya taimake ka, Waziri tuba yake yayi abisa kuskure a gafarce shi" Murmushi kawai me Martaba yayi ya kalli Sarki! dake zaune kanshi a k'asa yana jini b'acin rain abunda Waziri yayi wa mahaifin sa. Kafin me Martaba yace wani abu Sarki! Ya fahimci abunda yake nufi, kamar ya sani kawai ya zura hannu cikin rigarsa ta ciki ya futo da kud'i zasu kai duba talatin ko sama da haka, mik'ewa Moddibo yayi ya rik'e a hannusa, kasa-kasa yace"ka rik'e a hannuka ana d'aurawa sai ka bata sadakin ta" Moddibo ya k'arba fuskar sa d'auke da murmushi kana ganinsa kasan na farin ciki ne. Kafin kace kwabo fada ta cika da mutane, nan me Martaba ya Umarci babban limami a fara d'aura aure. Alhamdulilahi-Alhamdulilahi an d'aura auran Moddibo da Balaraba kan sadaki dubu arb'ain da biyu, nan maga takarda ya fara rabon alawa da goro me Martaba ya Umarci Moddibo ya d'auke Balaraba su futa, haka kuwa a kayi, suka futa,suka bar Sarki! suna ta gaishe-gaishe da mutane Jiki a sanyaye Balaraba ta dunga tafiya har suka isa shashen Sarki! gabanta sai fad'uwa yake tana jin kamar a kwai wani abu da zai faru. Can fada kuwa komai yana tafiya dai-dai kana kallon Sallau kasan yana cikin wani mugun hali na d'imuwa yayi yunk'urin mik'ewa ya kasa saboda yadda yake jin jikinsa na rawa ji yake kamar kafarsa ba a jikin jikinsa take ba, nan me Martaba ya sallami kowa, mutanan da suka rage a ciki sune makusantan sa, sai Sallau da me gari Halilu da Walidi, kyautar ban girma me Martaba yayi wa Walidi, wanda tasa shi kusan sumewa a gurin ya dunga godiya, me Martaba yaja kunnen Sallau sosai, da sosai, sannan ya gargad'i me gari Halilu kan kar ya kuma aikata abu maka mancin haka, me gari Halilu ya bada hakuri kuma ya nemi afuwa, shi ko Sallau bud'ar bakinsa,sai yace"ranka ya dad'e maganar sauran yaran wato Sadiya da Usuman ina so abani su mu koma gida" Sarki!! Ya d'ago da kansa cikin fushi! yace"Sadiya da Usuman zasu zauna gurin "yar uwarsu,kai ka tafi ka kad'ai" Wani bafade ya kalli Sallau da jajayen idonsa yace"gyara kintsi dai!!! kayi na d'aya kayi na biyu kar ka sake kayi na uku,anan zan tub'e ka in zane maka jiki,ko zaka nunawa me Martaba abunda ya dace ne." Girgiza kai Sallau yayi jikinsa na kyarma! cikin tsawa wannan bafade yace"ka nemi afuwar gurin me Martaba" Jiki na rawa Sallau yace"Allah shi gafarta maka ina neman afuwa" Saura kad'an Walidi ya saki dariya saboda yadda ya ga jikin mahaifin nasa yana rawa, murmushi me Martaba yayi yace"Allah yayi mana afuwa baki d'aya, wato malam Sallau maganar wad'annan yaran naka Sadiya da Usuman kayi hakuri kabar su gurin "yar uwarsu kaji ko, duk lokacin da kukayi sha'awar ganinsu za'a kawo muku su har gida,idan kuna sha'awar zuwa gurin su k'ofa a bud'e take muna maraba da ku baki d'aya" me gari Halilu yace"godiya yake ranka ya dad'e" Ganin babu yadda zai yi ne yasa ya fara yak'en dole yana godiya ga me Martaba, amma in zaka tona zuciyarsa a lokacin tafi garwashi zafi da turiri. Nan me Martaba ya bada Umarni a kaisu gida tare da kayayyakin abinci buhu-buhu mota guda a ka had'a musu na kayan masa rufi,Walidi kuwa in ya tuno da kyautarsa da akayi masa sai yaji kamar babu wanda ya fishi sa'a a rayuwa,gobe i yanzu yana cikin kasuwar sha tambaya yafara gudanar da kasuwancin sa. Cikin tsananin b'acin rai! Waziri Zayyanu ya shiga b'angaran sa,sai a kayi sa'a duk "yayan shi maza na zaune a falo suna

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108