Chapter 34
Chapter 34
karyar zakiyi min kenan, in da gaske kike ki matsa in shiga cikin dakin naki in duba kaji ni da ja'irar yarinya ko" Ya karashe maganar yana gyara babbar rigar shi "Haba Baba, wannan ba yi bane, kai yanzu a kace ka shiga dakin sai ka shiga,gaskiya kai Lusari ne wallahi" Hahahahaha Walidi ya karashe maganar yana kyalkyala dariya, ya zira hannu cikin aljihun wandon dake jikinshi wanda yayi dau'da sosai duk jirwaye, gudar dubu daya ya futo da ita ya mika masa yana cigaba da dariya kamar wani mahaukaci, ganin Walidi ya futo da Dubu daya sabuwa dal! ya bawa Sallau yasa jikin Lantana kyarma, washe baki tayi ta matso kusa da Walidi, tace"Ashe da gaske ka keyi yaron nan, ai nace dama jarina yayi kasa, kaga yau sai in shiga kasuwa in siyo kuli-kuli, Allah dai yayi maka albarka d'an nan Walidi yasa dariya yana nuna Lantana da hannunshi yace"ke dai Lantana in kika ga kudi duk sai ki shiririce, dube ki don Allah" yafada yana dariya, ya cigaba da cewa"wannan kudin sun futo daga gurin mijin Balaraba insha'Allah in kin kwantar da kai,kullum zan dinga baki dari biyu, yanzu dai ga dubu daya ke ma sai kira jari kamar yadda kika fada, Warce wa tayi daga hannusa, tana washe baki tace"da gaske kake dan nan"? "Da gaske nake mana,ke dai ki dai na takurawa Balaraba a gidan nan" "Yo ni dama ai bana takura mata,sai kaje ka nemi masu takura mata, to kaj! in kaji ina mata fada to fadan gaskiya ne, ko ba haka bane Balaraba" tafada tana kallonta Girgiza kai kawai Balaraba tayi tana kokarin komawa daki Jin hayaniya tayi yawa a tsakar gida yasa Uwa! futowa daga dakinta, yau ta makara bata tashi da wuri ba dalili jiya sun dade ita dasu Shamsiyya,da Maburuka suna lissafin kudi, har Sallau ya dawo daga mahadarsu ya taddasu suna lissafi,yayi-yayi su bashi dari biyu Uwa! ta hana shi "yayan nashi kuwa sai dariya suke masa, Shamsiyya ce me cewa" Baba zuciyar ka ta mutu, wallahi Allah ya wadaran Halinka" nan ya mike ya barsu ya shige daki yana ta zaginsu,su kuma sai dariya suke masa. Ganin kudi tayi hannun mijinta cikin mamaki, ta bi bayanshi ganin yana kokarin futa daga gidan, yasa ta kwala masa kira"Sallau" Da sauri ya juyo yana hararar ta, ta karaso gurin kanta babu dankwali daga ita sai daurin kirji tace"me nake gani a hannun ka kamar gudar dubu daya" Da sauri ya zira ta a aljuhu yace"Kwarai kuwa menene"? "Kamar yaya menene, a gidan ubanwa ka samu kudi,haka kuma kake kokarin futa batare da ka bamu kudin karin kummalo ba,tunda Allah yasa ka samu" Banza yayi mata kawai ya kama hanya zai futa a karo na biyu, da sauri ta je ta tari gabanshi, tana hura hanci tace"karya kake wallahi, ka bani ko yanzu in tara maka mutane,domin na gaji da muguntar ka, wato sai da kasamu kudin kaje kaci banza kaci wofi,to baza ta sabuba,wai bunda a ruwa" Tafada tana dukan cinyar ta Sanin halin jarabar Uwa!yasa Sallau kallo inda Walidi yake tsaye yace"Zo kara bani da wannan mutsiyaciyar Uwar taka, mayyar kudi" Dariya Walidi yake sosai ya karaso gurin yana wata irin tafiya yace"ai duk halinku daya da ita Baba, dubu daya ya ciro ya mika mata yace"kema gashinan kici albarkacin Balaraba" Da sauri Uwa ta karbi kudin daga hannun Walidi tace"karya kake inci albarkacin wata banza yarinya, wallahi" "Ke dai kika sani, zaki iya yaga kudin yanzu, ai tunda kince karya ne" Tafiyar ta tayi tana surutai gami da fadar bakaken magan-ganu ga Balaraba, Sallau ma fucewa yayi ya bar gidan, Lokacin Balaraba ta samu ta futo ta shiga bandaki, domin tayi wanka ganin rana tafara yi, jan ruwa take a rijiya, Maburuka ta futo hannuta rike da bokiti, da kutto wande ke dauke da sabulu da soso, daga ita sai daurin kirji,wani irin kallo ta watsawa Balaraba, taja tsaki, yaje ta dangwarar da bokitin saura kadan ya fada kafar Balaraba, tayi saurin kaucewa, kawai bata saurare ta ba, ta dauki ruwan da taja cikin wani bokiti irin na roba ta shiga bandaki, nan ta jiyo Mabaruka na cewa, banza kawai, kina dauke da najasa kina shigarwa mutane,ban daki dole ne ma in kin futo in wanke bandakin domin bazan je in kwashi cuta ba" Ranta ya ba'ci sosai jin abunda Marubuka take cewa a kanta, sauri-sauri take ta futo daga bandakin taci Uwarta, ta lura idan bata, tasar musu tsaye ba,zasu hanata shan ruwa a gidan, Mabaruka na zaune a kan rijiya tana wake-wake cikin rashin kamun kai, Balaraba ta futo daga bandakin, tayi kamar zata wuce, sai tai sauri ta dawo da baya,ta damki! wuyan Maburuka ta rike tamau, ta jawota sosai suka matsa daga jikin rijiyar, had'a ta da bango tayi ta makure ta sosai tace"wa kike zagi ne, mara kunya" Kakari! Mabaruka take sosai tana son tayi magana takasa, idanunta sunyi jajazir, Wani wawan mari Balaraba ta tsinka mata,wanda yasa jinta da ganin ta suka dauke na wucin gadi, tace"Ke baki kira kanki da najasa ba, zaki kira wani, bari kiji dan uwarki, duk irin iskancin da kikeyi a unguwar nan nasani, shegiya me bakin uwa, duk sharrin ku sai ya koma kanku,ni nafi karfin ku wallahi" Hawaye ne, kawai yake zuba a idanun Mabaruka, jikinta sai kyarma! yake yau ta tsorata da Balaraba sosai,ashe haka take da karfi,sai kace me aljanu, Cikin ikon Allah har yanzu babu wanda ya futo daga daki cikin mutan gida, Kasa da muryar ta tayi tace"bani hakuri dan Uwarki ko in cire miki makogwaro yanzu-yanzu Bakinta na rawa tace"Allah ya baki hakuri" Sakinta tayi tana hararar ta tace"karyar rashin kunya kike yi yarinya,wallahi kika duk ranar da kika kara zagina sai naci miki uwa"! Shiru Mabaruka tayi tana kallonta Har ta shige dakinta, Cikin sauri-sauri take shiryawa ta tashi su Sadiya da Shamsu ta shiryasu cikin uniporm kamar kullum, ruwan tea ta dafa musu,dake tanada kayan shayi a dakinta nan ta hada musu suka karya,suka futo a tare,a gurguje ta leka dakin Iya suka gaisa, tace"yau baki futo ba" "Wallahi na tashi da zazzabi ne, tun dazu nake jin hayaniya a gidan, lafiya in ce ko"? "Lafiya kalau" Balaraba tafada ta cigaba da cewa" amma kin sha magani ko"? "Ai cikin dare zazzabin ya rufe ni" Iya tafada tana kara rufe jikinta, "Insha Allahu zandawo da wuri sai muje chamis a duba ki" "To sai kin dawo,kinji Allah yayi miki albarka" "Ameen Iya nagode, in su Sadiya sundawo su zauna a gurin ki tunda babu isilamiyya yau" "To shikkenan sai kin dawo" Balaraba na futa taci karo da Walidi shida abokansa, da sauri ya taso ya zo ya karbi jakar hannunta, sai washe baki yakeyi, suka jera,har inda me Napep dinta yake, tsayuwa in yazo daukar ta Tunda ta futo matasan dake unguwar suke kallonta wasu su fadi alkairi,wasu su fadi sharri a kanta, babu abunda ya dame ta, ta shiga Napep, Walidi ya mika mata jakar ta, yana mata adawo lafiya Suna futa daga unguwar ta kunna wayarta, ko minti biyu ba ai ba kira ya shigo, sai da ta kusa katsewa sannan ta daga, Ajiyar zuciya ya sauke, muryar shi kasa-kasa yace"Allah ya taimaki Gimbiya ta" Shiru
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108