Skip to content

Chapter 93

Chapter 93

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
Download Book

zata yafe muku abunda kukai mata kunga bata da hakki a kanku gashi da kanku kunzo kun tonawa kanku asiri,,, bayan kun nemi gafarar ta kuje kuyi ta istigafari domin Neman yardar Allah" Uwa! Tana kuka wurjajan ta matsa kusa da Balaraba tace"Ki yafe min abunda nai miki Wanda na sani da Wanda ban sani ba,, nasan na cutar da rayuwar ki nayi miki sharri da kazafi gashi duk abunda nake jifan ki dashi bai same ki ba sai alkairi abun sai ya koma kan "yayana nasan hakkin kine wallahi" Share hawaye tayi tace"Uwa! Ki daina kuka kinji ko har yanzu kinanan a matsayin uwata kuma na yafe miki duk abunda kikayi min Allah ya yafe mana baki d'aya" "Nagode-nagode nagode sosai Balaraba Allah ya baki zaman Lafiya da mujin ki" Mama tace"Amin haka ake son mumunin ya zama me ya fiya" Lantana ma ta matsa kusa da ita tana kuka sosai Sam ta kasa magana. Balaraba ta rike hannunta tana fad'in nasan abunda kike so kice"Na ya fe miki, dama tun tuni na ya fe miki kuma har yanzu kinanan a matsayin kakata naji mutukar dad'i da kuka gane gaskiya. 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿104* Mama ta kalli Shafa'atu tace"Ki d'auki wannan kayan tsubbu kije ki k'ona su can bayan gida, ubangiji Allah ka rabamu da sharrin zuciya" Jakadiya tayi bisimillah ta d'auki ledar dake aje gaban Mama ta futa daga d'akin domin taje ta aiwatar da aikin da aka sata. Madabo tayi musu wani kallon banza tace"Ya kamata Ku zo a mai daku gida domin zama daku annoba ne,wallahi Fulani ki barni da halina kawai amma na tsani mutum me asiri wallahi" Murmushi Fulani tayi tace"Na san halin ki ciki da bai don me yasa bakya shiri da Kulu ai saboda halin ta ne" Madobo tace"Wallahi kuwa ai Kulu tayi nisa sai addu'a" Mama tace"Ita kad'ai ce magani" Shiru falon yayi, kunyar duniya ta ishi su Lantana sun kasa d'ago kai su kalli mutane,,Balaraba ma kanta na k'asa tana sak'e-sak'e, k'amshin turaran sa ne ya gauraye falon,, da sallama ya shigo cikin yanayin tafiyar sa ya zauna kusa da mamansa. Kwarjinsa da haibar sa ya cika falon, Lantana duk dadewar ta a gidan bata tab'a ganin shi ba sai yanzu, bakinta na rawa tace"Ranka ya Dade ya barka da yamma" A nutse ya galli gefan da take ya amsa Cikin yanayin muryar shi. Mama tace"Kakar Balaraba ce nasan baka gane ko wacece ba" Mai da ganinsa yayi kan Lantana wacce tayi muzu-muzu a zaune tana tsoran kar Mama ta fada masa halin da ake ciki,, minti biyu yana kallonta yaji sam matar bata kwanta masa,, a hankali ya Dora idonsa kan Uwa! Ta zaune sai gumi take cikin zuciyarta take cewa dama wannan ne Sarki! Almansur din? Lallai Allah yayi hallita a gurin,, ina Shamsiyya ina shi,, a ya zama dole ta sanar da Shamsiyya cewar ta daina wahalar da kanta ko mutuwa zatayi ta san Sarki ya fi k'arfin ta,, Ya mutse fuska yayi ganin wata koriyar kwanta a idon Uwa! Abun k'yamk'yami yace"Ita kuma wannan fa"? A hankali Mama tace"Matar Kawun ta ce, sunanta Uwa!" Tunda yaji haka ya d'auke kansa zuciyarsa tana tashi tunda ya kalli fuskar Uwa! Babu kyawun gani,, gai sawa sukayi da Madabo cikin mutum ci da girmama juna,, ya gaida mahaifiyar shi a mutumce, falon yayi shiru kowa da abunda yake sak'awa a zuciyarsa Tunda ya zauna a gurin yake so su had'a ido da ita,, Allah bai bashi iko ba, itama gane hakan ne yasa taki d'ago kanta sai kara sunkuyar da kanta take. Mama ta kalle shi tana fad'in "Dama yanzu nake cewa a kira min kai zamu zauna da kai da iyalin ka" Shiru yayi yana d'an Sosa kai as'usuel. Gimbiya Halisa ta futo daga wani daki dake cikin falon tw cire alkyabar jikinta yanzu tana cikin wata muguwar shadda wacce akai mata mugun aiki mai bala'in kyau (sirfani) abunka da siririya sai dinki yak'i zama a jikinta sosai, duk cikin kayan lefansu take Balaraba na da irinta Azima ma haka. Mama ta kalli su Lantana da suka muzanta tace"Yanzu sai Ku shirya a mai daku gida ko" Lantana kamar ta kurma ihu shikkenan, taga samu taga dashi,inama ace Balaraba ta ce ta zauna mata Jakadiya Shafa'atu CE ta dawo ta zauna Cikin nutsuwa,, Mama tace"Jakadiya kar ki gaji a had'a musu tsaraba zasu wuce gida" Jakadiya ta mike tana fadin"An gama Uwar dakina" Balaraba ta mike a nutse ta nufi dakin da take, duk wani Abu da tasan nata ne naci da na sawa ta had'a su guri guda ta futi dasu da k'yar,, zama tayi kujerar da ta tashi tace"Gashinan Ku raba Wannan nawa ne babu yawa,, Ku gaishe min da Iya matar Kawu" Lantana godiya kawai take yau ta k'ara tabbatar da cewa Ubangiji mak'agin baiwa ne me yin yadda yake so da kowa wai tana raye a duniya Balaraba tayi aure kuma ta dauri Sarki! Lallai idan kace tukunyar wani baza ta tafasa ba to taka ma ko dumi baza tayi ba, tabbas taga ishara ta gane duniya ba komai bace, yanzu dole ta kwantar da kai suci su sha ta dalilin Balaraba.. ******* ******* ******* Shamsiyya tsugene a bakin kofar zauren Arrama ta buga-buga an ki budewa, wata zuciyar tace watak'ila yana ciki yana aiki shine ta tsuguna tana jiran ya gama,, wasa take da wani kara a hannunta taji zuciyarta tana wani irin tashi, da sauri ta mike taje bakin kwata ta dunga yunk'urin amai,, aikuwa kafin kice me sai ga wani amai Kore fatau tana kyalashi,, mutane suka fara taruwa a kanta suna tausayin ta,,wata mata tazo ta kamata ta mikar da ita suka samu dakali suka zauna, da k'yar ta dawo hayyacin ta sai haki take, matar tace"Yarinya daga ina kike haka ai gwara ki koma gida ki je ki huta" Shamsiyya ta ya mutse fuskarta har yanzu tana jin tashin zuciya tace"Nazo gurin Arrama ne, tun d'azu nake bugu bai bude ba nace ko aiki yake ne" Matar ta girgiza kai cikin takaici wato ire-ire "yan Matan da suke zuwa gurin Arrama ne, wannan wai duniya INA zaki damu bin malamai babu yara babu manya babu zawawara babu Matan aure da " yan mata, tace"Ai sai da kiyi hakuri jiya-jiyanan aka kama shi yanzu yana hannun hukuma saboda jiya wata buduwar yarinya tazo Ita da uwarta gurin nan cika yayi da d'an Adam tazo tana kuka yayi mata ciki wata uku shine sukaje suka d'auko "yan sanda a ka kamashi, to d'azu da safe labari ya same mu cewar ya kufce daga hannun " yan sandar ya gudu" Shamsiyya ta d'ora hannu aka tana fad'in"Na shiga uku na lalace, Arrama me yasa zakayi min haka,, kace Saura kad'an aikina ya kammala shine zaka gudu baka k'arasa mun ba" 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108