Skip to content

Chapter 68

Chapter 68

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,251 words 0 views Progress saved
Download Book

kamar ta dena aiki,sai haki!tsabar d'imuwa da tashin hankali sunyi masa katutu a k'ahon zuciya. Duk suna zazzaune a tsakar gida suna jiran shigowar Sallau hankalinsu duk a tashe, kowa da abunda yake fad'a, akan Balaraba wai ita ta kai kararsa gurin Sarki! A rirrik'e a ka shigo dashi Lantana ta tashi tana sallalami gami da salati dad'i take shikkenan,wannan "ya tasa anyi masa wannan bulala ta gidan sarki!Allah ya tsine miki Balaraba" Ihu!Su Shamsiyya suke sukayi kan ubansu suka kakkamashi suka shiga d'aki dashi suna duba jikinsa sukaga babu wani k'warzane ko d'aya babu alamun duka a jikinsa. Uwa!tace"Wai meye kake haka sai kace Wanda zai tada aljanu,tun safe munanan muna fargaba,gaka ka dawo kuma me makon kayi mana bayani kuma kazo kana wani nishi!sai kace kuturo" Lantana tace"Ke rufe min baki shashasha kawai,bakya ganin halin da yake ciki,Allah yasa dai ba guba suka bashi yasha ko ya Ciba" Walidi dake tsaye bakin k'ofa yasa dariya yana nuna Lantana da hannu yace"Babu wata guba da yaci,guba d'aya itace bak'ar zuciyarsa ya kusa had'iyewa saboda tsabar bakin ciki, Hahahahahaha" Walidi ya shek'e da dariya babu abunda ya dame shi. _*TSANTSAR BUTULCI*_ *_NA_* _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA*πŸ‘„ _littafin me cike da sark'akiya gami da cin amana, kar Ku bari a baku labarin_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» 。。。。。。。。。。。。。。。 _*GIMBIYA BALARABA*_ πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULAπŸ‘„* _MARUBUCIAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* _*Zamani writers Association*_ ________________________ *We are her to educate motivate and entertain aur Reades* _________________________ *DIDEGATED* *to* RAHAMA ALIYU BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM *πŸ…Ώ78* Wata k'atuwar harara Lantana ta makawa Walidi bakinta na kumfa tace" Walidi kayi asara wallahi ban san inda kaje ka samo wannan b'akar zuciyar taka ba, yanzu ubanka na halin rai da rayuwa shine kake masa dariya" ta karashe maganar tata tana rik'e hab'a cikin mamaki! Wata mahaukaciyar dariyar Walidi ya kara saki yace" Kaji Lantana da wani magana kuma, hahahahaha, ai bak'ar zuciyarki na gado, amma naji kina zancan ina na gado bakar zuciya, to ai kece kika gada mana ita, hahaha" Ya k'arashe maganar da mahauaciyar dariyarsa, barin gurin yayi yana fad'in ni kam nayi nawa guri domin yau ina cikin farin ciki da annushwa sanadin Balaraba yau na "yantu na zama cikkaken mutum ehe duk d'an bak'in ciki sai dai ya mutu! fucewarsa yayi ya barsu da baki a sake Sallau kuwa tuni ya sharb'e a gurin bakinsa ya karkace miyau na dulala, da kyar ya d'aga hannusa guda yana kiran Lantana ta matsa kusa dashi tana salati, baki a mugud'e yace" Lantana muna cikin wani yanayi wannan yarinya da mukai wa rikon sakainar kashi, Allah ya rufa mata asiri tana gidan sarki za'a d'aura mata aure da d'an wazirin gar..... kafin y k'arasa maganarsa Lantana ta fahimci abunda yake nufi, wani uban ashar! ta kurma tamkar ba tsohuwa ba fad'i take, "Me nake shirin ji ni Lantana, Balaraba d'iyar Tanko itace zatayi aure gidan sarauta ni nawa jikokin na nan a zaune lallai da sake! tafad'a wata irin kumfa na futa daga bakinta tsabar tashin hankalin da take ciki sam yanzu rashin lafiyar Sallau din bata gabanba, tunanin ta ya koma gurin ganin yaya zatayi ta futo da Balaraba daga wannan gida ko ta halin k'aka ne. Shamsiyya ce ta futo daga uwar dakinsu daga ita sai daurin kirji nonuwanta sun cika sun tun batsa sai kace wata matar gida goshinta sai kyalli yake. Lantana ta dube ta sama da kasa tace"Dube ki cikkakiyar mace wacce ta amsa sunanta na mace kina zaune a gida kina tsotsor tsamiyya waccan mutsiyciyar yarinyar ta shallake ki, ai ko ta halin k'aka sai kin zauna gidan sarauta kema" Lantana ta karashe maganar kmar zautacciya Shamsiyya tace"Wai hayaniyar me nake ji ne tun dazu ina bacci" Nan Lantana ta kwashe duk abunda yake faruwa ta fada mata" Wani irin k'yashi da bakin ciki da hassada ne suka dura a zuciyar Shamsiyya ,rashin abunyi ne yasa ta fashewa da kuka wurjanjan! ta kalli inda mahaifiyarta take zaune kamar mutum mutumi,sai kace wata gunki tace"Uwa! kina raye a duniya haka tafaru damu k'askantacciya ta fimu komai kullum.kina cewa zaki sabautata mata rayuwa, gashinan kina zaune taje ta auri dan gidan sarauta mu muna zaune" "Wayyo na shiga uku na lalace"! Sosai Shamsiyya take kurma ihi! Wata wawar ajiyar zuciya Uwa! ta sauke zuciyarta cike da bakin ciki gami da hassada, a halin da ake ciki yanzu batasan yadda zata fara ba,amma ya zama dole ta bazama k'auyuka gurin malamai da bokaye, domin samawa kanta mafuta lallai maganar hauwa ta tabbata inda suke cewa dan hakin da ka raina shike tsone maka ido, a halin yanzu duk hankalin ya karkarta gurin ganin yaya za'ayi su sabauta Bawa Balaraba rayuwa ko ta mutu ko tai rai ko ta haukace cikin uku za ayi daya https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» 。。。。。。。。。。。。。。。 _*GIMBIYA BALARABA*_ πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULAπŸ‘„* _MARUBUCIAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* _*Zamani writers Association*_ ________________________ *We are her to educate motivate and entertain aur Reades* _________________________ *DIDEGATED* *to* RAHAMA ALIYU BISIMILLAHIR_RAHAMANIR RAHIM ``` Tunanin ka kamanin ka d'an uwa ka tsare kanka, Allah yai maka albarka, sai ka gyara makomar ka``` _*Wannan magana taka haka take fasihin mawak'i Musbahu m Ahamad*_ *Allah kasa mu dace* *πŸ…Ώ79* Da sauri Uwa!ta mik'e har zanin dake d'aure a jikinta yana k'okarin fad'uwa k'asa, tayi saurin rikeshi ta tsallake Sallau da kwance magashiyan a dandaryar k'asa,sai nishi yake,d'akinta ta afka kamar mahaukaciya,taje ta zura rigarta ta yafo mayafi ta futo, tana kallon Shamsiyya tace"Maza jeki sako riga mu baza ma,domin zama bai gan mu ba" Da sauri Shamsiyya ta shiga dakin domin sako riga. Lantana ta kalli Uwa!dake tsaye tana zazzage kud'i a cikin banki irin na gwangwani,tana lissafawa, tace"Uwa!yanzu, waye zai kula da Sallau gashi a kwance, kin san nima futa zanyi,yau na tashi bani da ko kwabo" Hararta Uwa!tayi tace"Ai yau dole ki hak'ura da zuwa ko ina ki tsaya ki kula da d'anki daga nan har zuwa lokacin da zan dawo, domin kema zaman jiyya ya kama ki" Lantana ta karyar da kai gwanin tausayi tace"To tunda kince haka shikkenan zan zauna, nasan dai zaki sammin abunci da zansa a baki na" Uwa!tace"Idan Shamsiyya ta dawo daga talla ta ciri dari biyu tayi cefa ne,ina da sauran garin kwaki,sai ta tuk'a muku teba,daga nan har dare,in kun ga bamu dawo ba to ku rufe Gida kawai domin in na futa yanzu sai inda mai ya tsaya" Lantana tace"To to shikkenan ai,Allah dai ya bada sa'a, a samo nasara" Uwa!tace"Ameen, ai in kana da kudinka komai me sauk'i ne, dama Dan me nake neman kud'in duk dan "yayana,saboda haka yau ranar sune" Tafad'a tana lissafa kudinta sun kai kusan dubu goma sha bakwai.haka ta zufa basu cikin wata karamar jaka, ta rataya ta a kafad'a Shamsiyya ta futo daga daki. Suna futa tsakar gida suka ci karo da Sadiya matar Kawu Mamman tana tsaye bakin k'ofar ta duk abunda yake faruwa a kunnenta. Kallonsu tayi tana me tausaya musu,ganin suna nema su jefa kansu cikin halaka,tace"Uwa!kiji tsoron Allah, ki tuna akwai ranar tsayuwa, me Balaraba tayi miki kike nema ki jefa rayuwarta cikin musiba,ki sani da shi sharri d'an aike ne, zuwa yake ya dawo saboda haka Ina mai tunasar dake cewar

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108