Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,239 words 0 views Progress saved
Download Book

suka fito suna rokarsu suyi hakuri ,Amma Ina!! Sam sun ki hakura sai dukanshi suke Suna Tambayar inda ya kai Wayar Mutane, Amma Yaki Magana Sabida tsabar Taurin Kai!! Makota cike da gidan suna Kallon ikon Allah ,dayawa daga cikinsu cewa suke Alhakin Hafsatu ne ya fara kama Uwa! Uwa! Ko Na can tana zagi Sallau Cikin Rashin kunya tace"So lubiyo Namijin hotiho ,kana tsaye a shigo har gida ana dukan Dan ka ka kasa tabuka komai, kai dai kayi Asara Wallahi *Balaraba* ce ta shi go gidan Jikinta Sanye da kayan Makarantar Isilamiyya Riga da wando da Hijabi ,Kafadar ta sakale da jakar buhu ,Wacce ta sanya Alkur'ani hade da Sauran Littatafan Addini. Da kyar! Ta samu ta Ku tsa cikin Mutane ta isa gurinsu,Hsnkalinta Nakan su Umaruru ,Ganin suna dukan Iro babu Imani gashi kowa yayi shiru, Lantana Ta kalleta ta Watsar Tace"Kunga barauniya nan ita zaku doka Ba iro ba domin ita ke min satar "Yan kudade na idan naje Tallah Na dawo ko tausayi Na,bata ji Sabida tsabar Rashin Imani" Ta karashe Maganar tana mikewa Tsaye Dukan ninsu suka joyo suna Kallon *Balaraba* jin Abinda Lantana take fada a kan ta, Hakan yaba Iro da mar tserewa da gudu yayi Waje hanci a fashe yana jini ,ga jikinshi yayi budu budu Rigar da yake sanye da ita ma ta yage! Tsabar Wahala Umaruru Yace" *Balaraba* kin dawo daga Makarantar"? "Eh Umaruru Balaraba ta fada cikin Nutsuwa Umaruru ya Kalli Lantana ,yace" Wallahi kuji tsoran Allah da ranar Lahira tsohuwa ,Ku dinga fadin Alkairi a kan Dan Wani *Balaraba* yarinyar kirki ce,Domin ba 'a taba kamata da kayan Sata b..... Uwa ta katse shi ta hanyar Cewa"Dole kafadi haka mana Munafiki Allah ta Allah ,sabida kana kama ta ka latse a lungu da sako ,Ai mun San duk Abinda yake Faruwa ,Babu Abinda bamu Sani ba" Ehee!! Kuka Mai cin Rai Hafsatu ta fashe dashi ,ta shige dakin ta da gudu,ita ko *Balaraba* Tana tsaye Babu Cikin dakiya idon ta tar! Duk da a lokacin tana da kananun Shekaru ta Gama gane Bata Da babbar Makiyya kamar Uwa! _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* 08089965176 [04/05, 03:15] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? 🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀ *🐾GIMBIYA BALARABA*🐾 🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀🧝🏻‍♀ *by* _BINTA UMAR_ *MAMAN ABDUL WAHABU* _ZAMANI WRITES ASSOCIATION_ *🅿22* Uwa! ta cigaba da cewa "dama duk wannan yawon da take yi da sunan zuwa makaranta ,mun san iskanci take tafiya tunda dama "yar nagada ce ,sabida haka kufadi kudin wayar ku a biya ku domin ana da abin da za'a biya, Ta karashe maganar cikin kuri! da cika baki,sabida tasan bata da wasu kudi idan ba jarin a wararta ba, Umaruru mamaki ya cika shi jin abinda uwa take fada,sai ya girgiza kai kawai yana mamakin sharrin wasu matan ,shiyasa a kace ko shedan yana gudun sharrin mace, Balaraba kuwa tana tsaye babu damuwa a tare da ita domin in da sabo yaci ace tasaba da irin kiyyar da suke nuna ma ita da iyayenta, shiyasa abin baya damunta da yake yarinya ce mai taurin zuciya ,sai dai abin yai ta damun mahaifiyar ta,itama babu abinda take iya yi idan ba kuka ba. Umaruru ya kalli uwa! dake tsaye tana hura hanci! yace"kudin wayar nan dubu bakwai da dari biyar ne ,sabida haka tilas a biya ,hakan kuma ba ya na nufin cewar in muga iro baza mu damka shi ga hukuma ba,tundadai kowa ya shaida da hakan. Sallau yayi saurin tarar sa yana kwantar da kai yace"umaruru kuyi hakuri a kashe magana anan don Allah za muyi masa fada ,in sha Allah bazai kara ba. Uwa Kuwa da taji maganar dubu bakwai gabanta ya yanke ya fadi sabida tasan dudu-du jarin a wararta bai kai na dubu uku ba,kuma dashi take joyawa suna cin abinci sai tafara sake-saken yadda zatayi, "Tun yaushe kake fadar haka,cewar zaka ja kunnesa naji labari cewar ai kai yake kawowa kudin kuke rabawa shiyasa kake daure masa gindi Sallau ya gigice sai rantse rantsa yake yace"ni ko kwabo baya bani ban sani ba ko uwarsa yake kawowa gatanan a gabanku ni babu ruwana" Dama umaruru ya fadi maganar ne domin ya tsoratar da shi. Cikin uwa! ya duri ruwa sabida tasan idan suka gane tana karbar wani abu daga hannun iro itama ba kyaleta zasuyi ba, Tayi sauri ta katse sallau dake basu hakuri,cikin rashin kunya tace"dallah malam matsa kabawa mutane guri solobiyo kawai,kai umaruru nawa kace ma kudin wayar,? tafadi maganar sai kace wacce zata iya biya "Dubu bakwai dari biyar ne" Ta kalli Lantana wacce tunda zu ta kasa furta ko a sabida taji ana maganar biyan kudin waya, ita kam bata da ko kwabo ba zata bayar ba. "Lantana ki fito da kudin nan danaga kina lissafawa a biyasu kudinsu ,tunda dai kema iro yana mora miki kullum da daddare sai kin ce ya siyo miki balangu ko kifi" Lantana tayi tsuru-tsuru tana motsa baki ,da kyar! tace "mai nake dashi "yannan ! da zan bayar so kike na rusa jarina" Cikin rashin mutumchi Uwa tace "Lantana dole fa kifito da kudin jikinki ko kinqi ko kinso wallahi domin bazan bari su kashemin da ba,ehee"!! Da kyar! Lantana ta kwance zaninta tana daga zaune ,sai surutai take tafito da "yan ashirin ashirin da "yan goma goma ,kwata kwata a kudin babu hamsin ko daya Uwa tazo ta kwashi kudin da sauri ,tafara lissafawa, *Balaraba ko na tsaye cikinta kamar ya kulle dan dariya sai boye dariyar take dan kar ta fito amma INA! sai da ta subuce mata ta zauna kasan gurin tana yi tana kallon Lantana dake faman share gumi! Sai tsine-tsine take,wai sam bata yadda ba kalawa Iro sata a kayi ,Aiko Lantana ta dauki wata sanda da suke tone kwatarsu idan ta toshe ta kaiwa Balaraba duka da ita tana faman zaginta ta uwa ta uba. Balaraba ta mike da sauri ta shige dakinsu tana jiyo Lantana kamar mahaukaciya tana ta dura mata ashar tamkar ba tsohuwa ba. To da kyar! dai Uwa ta samu ta hada dubu uku da dari biyu,domin kudin gun Lantana ko dari biyar basu kai ba,ta mikawa Umaruru gami da cewa"gashinan Abinda ya samu kenan,Shamsiyya bata dawo daga tallaba,kuje kubawa mai wayar hakuri idan an kwana biyu za'a cika masa kudinsa,domin Allah ya hore abin da za'a biya Umaruru ya karbi kudin yana lissafawa tsaf! Yace "kifadi ranar da zaki ciko kudin kawai bama son jeka ka dawo" Tabe baki tayi tace"ku dawo rana ita yau zan Baku kudinku" "To Allah ya kaimu kar muzo kice wani abu fa" "Mtssss nifa nace kudawo Ku karba ,akin banza akin wofi,Uwa! tafada a zafafe ,bakin cikinta yadda ta rusa jarinta yanzu kafin ya tashi ma aiki ne Umaruru yaja ta wagarshi suka fice daga gidan,suna fita Uwa tace dawa Allah ya hada ta duk wanda ya kwana ya tashi a gidan sai taci masa mutumchi kar dai Sallau yaji labari, Simi-Simi ya kama hanya zai shige daki ,tayi saurin janyo masa riga gar wuyanta ya yage ,tace"kama hanya ka fita ka nemo mana abinda zamu ci ehe! wallahi baza ka shigarmin daki ka zauna min ka kashe min katifa babu abinda kake min sai dai in nema ,in ci da

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108