Skip to content

Chapter 60

Chapter 60

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,250 words 0 views Progress saved
Download Book

hira, nan suka ga shigowar mahaifin su hankalin sa a tashe, Khalifa ne yace" Allah yasa lafiya dai na ganka kana faman gumi! Zama yayi cikin kujera yana cire rawanin dake nannad'e a kansa,yace"je ka kira min mahaifiyar ka" Tafiya yayi kiranta, ya kalli sauran yaransa da kumfar baki yace" in dai nine na haife ku daga yau na rabaku da Moddibo har abada babu ni babu shi hakanan kuma babu ku babu shi" Cikin rashin fahimta Ishak yace"ban fahimci me kake nufi ba Baba" Zuwan mahaifiyar tasu ne ya dakatar da maganar da yake tazo ta zauna kusa da mijin nata,tana kallon fuskarsa tasan lallai yau an tab'oshi" "Lafiya ranka ya dad'e"? Ta fad'a cikin sigar tambaya. Waziri yace" zaki ce min baki san abunda yake faruwa bane? kun had'a kai da d'anki kun munafurce ni, yaje ya d'auko yarinya da suka gama lalacewa da ita a waje ya kawo wa wannan mak'iyin nawa ya d'aura masa aure da ita" "Duk maganar da kakeyi ban fahimce ka ba,domin kuwa ni ban San abunda yake faruwa ba" Girgiza kai yayi kawai ya umarci d'aya daga cikin yaran dake zaune a gurin yaje ya kira Moddibo. Hankalin kowa ya tashi a gurin saboda sun san halin mahaifin nasu bai iya b'acin rai ba. Mintuna goma tsakani Moddibo suka shigo tare da Ishak d'an uwansa Ko zama Waziri Zayyanu bai bari yayi ba,yace"Umarni na ne ni ne nasa a kira ka, saboda dalilai masu k'arfi,yanzu-yanzu nake so ka furta cewar ka saki wannan yarinyar da kasa aka d'aura maka aure da ita,idan kuma kak'i ni yanzu zan saki taka Uwar,saboda haka zab'i ya rage naka." *Muje zuwa* *Comment Vote and Share* [05/08, 20:08] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` _BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_ *🅿68* Dukaninsu sun furgita da jin furucin da mahaifin nasu yayi, ita kanta mahaifiyar tasu ta girgiza da furucin da mijin nata yayi,kuma tafi kowa sanin halinsa zai iya aikata duk abunda ya fad'a. Modibbo ya shiga, tsaka me wuya bai tab'a tsammanin hukuncin da mahaifin nasa zai yanke ba kenan,iya tunanin sa yana ganin zaiyi fushi dashi daga baya ya sakko shi kuma sai ya nemi afuwar sa, tabbas Uwa-Uwa ce, babu ta yadda za'ayi ta sanadiyar sa ya rushe auran da aka d'aurashi sama da shekara talatin da wani abu,dole duk son da yake wa Balaraba ya rabu da ita ko da hakan zai yi sanadiyar rasa rayuwarsa, a kan mahaifiyar sa babu abunda ba zai iya ba. Khalifa ne mara kunya sosai ya cikinsu yace"Mu baza ka jawo mana b'acin rai!ba a cikin gida saboda haka kabi umarnin da a ka baka, idan ba haka ba zamu b'ata maka rai kuma zamu hana matar taka daka aura jin dad'in duniya,a kan mahaifiyar mu,babu abunda baza muyi ba" Jin furcin da Khalifa yayi yasa Waziri umartar sa da yaje ya d'auko takarda sa biro, aikuwa da sauri ya tafi, ita kuwa Hajiya Kattime tana zaune tana kallon ikon Allah bakinta ya mutu, takasa fahimtar komai, a wannan badak'alar da take faruwa. Khalifa ya dawo hannusa rik'e da farar takarda da biro ya zo ya mik'awa Moddibo, guda d'aya, d'ayar kuma yaje ya kai wa mahaifin nasu ganin Waziri ya d'ora biro jikin takkada yasa Moddibo saurin dakatar dashi, da hannu jikinshi na kyarma! yayin da gumi yake zuba a jikinsa, ya d'ora biyu jikin farar takarda yayi rubutu kayi biyu,kamar haka. _Ni Yusuf Moddibo na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki d'aya kacal, kan wani dalili guda d'aya, ina fatan Allah ya had'amu da ita a aljanar Firdausi_ Yana gama rubutuwa ya ninke takadar, zuciyarsa tana wani bugawa fatt!!fatt!fatt! Waziri Zaiyyanu ya mik'a masa hannu yana nufin ya bashi takardar, a hankali ya karasa inda yake zaune ya mik'a masa, bud'e takardar yayi ya karanta ya mayar ya ninke ta ya aje ta gefe,wani takarda ya kara cirowa ya mik'awa Moddibo cikin bada Umarni yace"Saki uku zaka rubuta mata,saboda nasan halin wancan mutsiyacin zai iya turasasa ka ka mayar da ita,don haka ban yarda da saki d'aya ba" Cikin tsantsar b'acin rai Hajiya Kattime tace"Wannan abunda kake tsantsar jahilci ne da son kai, Allah da kansa shi ya hallici saki,kuma ya umarci da ayi shi,amma kuma baya son ayi din,saboda haka tunda ka tursashi ya rubuta saki d'aya saboda son zuciyar ka to ka kyaleshi haka, ba lallai sai an saki mace saki uku ba take sakuwa,saki d'aya ma ya hallata" Cikin tsawa Waziri yace"Zakayi abunda na saka ko sai ka gama jin hudubar da mahaifiyar taka take maka" Ganin Moddibo ya tsaya yayi shiru da takarda a hannu yasa Waziri ya d'ora biron dake hannusa a jikin takarda ya fara rubutu. Moddibo ya rik'e hannunsa jikinsa zafi rad'au! muryasa a shak'e yace"Baba Waziri ka gafarce ni, idan nayi maka,laifi, ni Yusuf Moddibo na saki Matata Balaraba saki uku" "Innalilahi wa inna ilaihi rajiun" Shine abunda Kattime take fad'a zuciyarta kamar tayi bunduga tarasa wane irin bakar zuciya ne da mijin nata. Mik'a masa takardar yayi a karo na uku yace"rubuta min da hannun ka" Ganin babu abunda yayi saura yasa Moddibo ya rubuta ya mik'a masa, ya bud'e ya karanta tsaf, cikin bada Umarni yace"Ka tafi da kanka kaje ka kaiwa wanda ya d'aura maka auran" Moddibo ya karb'i takardar ya kama hanya, yana tafiya yana had'a hanya jiri yana kwasar sa,Allah yasa bangaran babu ma'aikata sosai, sai da ya futa harabar gidan sarautar sannan ya dai-dai ta nutsuwar shi,amma duk da haka duk Wanda ya kalleshi a lokacin yasan yana cikin tsananin damuwa, haka ya isa fada, lokacin ana shirye-shirye kiran sallaar magariba me Martaba ya futo kenan domin shiga gida suka ci karo da Moddibo, yana kallonsa ya gane da akwai matsala, kafin yace komai Moddibo ya mik'a masa takardar hannunsa, da sauri maga takarda ya karb'a ya bud'e ya fara karantawa kamar haka. _Ni Yusuf Waziri Zayyanu na saki matata Balaraba Ayuba Tanko saki uku,saboda wani dalili,ina rokon Allah ya had'amu da ita a aljanar Firdausi_ *Innalilahi wa innailaihi raji'un* Kalmar da me Martaba yake ta maimai tawa kenan, kafin su ankara Moddibo ya zube a gurin yana wani irin murk'ususu, jini na fita ta baki ta hanci, ya rik'e cikinsa tamau! bakinsa na motsi,kalamar shahada kawai yake Sarki! ne ya futo daga b'angaransa ya na d'aure da alwala,sai ya hango abunda yake faruwa saboda haka cikin sauri da sassarfa ya k'arasa gurin,lokaci mutane har sun taro, hankali a tashe ya tsuguna ya d'ora gwiwarsa a k'asa ya d'auki kan Moddibo ya d'ora a cinyarsa, cikin damuwa ya sanya gefen rigar shi yana goge masa jinin dake futa daga bakinsa, Moddibo ya rik'e hannunsa tamau!! wani hawaye yana zuba ta gefen fuskarsa, muryarsa bata futa sosai yace"Allah yayi bazan yi tsayin kwana ba, a duniya balle in rayu da yarinyar da zuciyata take mutukar so, d'an uwana ne kai ko na mutu kai na amunce da ka maye gurbi na gurin Balaraba, ka bata hakuri,ga tanan na bar maka amana son Balaraba wani b'angare ne na zuciyata na tabbata ko na rayu a

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108