Chapter 21
Chapter 21
dai-dai na dan nashi yayi masa hudu ba kamar yadda Annabi ya fada sannan ya kira shi da sunansa sau uku, sai ya mike tsaye gami da rungumeshi ya ce zamuje fada dashi domin tasan da zuwansa" Hankalin Fulani ya tashi amma sai ta dakewa zuciyarta tayi addu'a tasan babu abinda zai samu dan ta face da sanin ubangiji, nan Maimartaba ya fita da jinjirin a hannunshi fuskarshi dauke da walwala Fada na cigaba da tafiya kawai suka ga sarki ya shigo rungume da yaro nan hankalin kowa ya tashi aka fara rige-rigen karbar yaron Waziri Zayyanu ne yayi nasarar karbarshi daga hannun sarki lokacin da ya zauna yace"ranka shi dade a ina muka samu yaro mai kama da kai sak, sai kace an tsaga kara" A nutse Maimartaba ya ce"yau Allah yayi min baiwarshi Allah ya sauki Fulani lafiya shine dalilin kirana" Saura kadan Waziri ya yar da yaron jikinshi ya dinga karkarwa kafin kace kwabo gumi ya jika masa riga sai yafara mutsu mutsu da baki kwata-kwata ya rasa abinda zai ce, fada ta dauki murna kowa yana fadin albarkacin bakinsa wasu na boye damuwarsu ban da Waziri domin mikewa yayi ya bar fadar yana sabe babbar riga tamkar zai tashi sama haka shige gidansa dake cikin gidan sarautar, Kafin kace kwabo Labari ya watsu cikin gidan, Uwar gidan Maimartaba ta turo Jakadiyar ta domin ta tabbatar sannan tasa a ka kira mata malaminta domin yayi mata binkice, malamin yace"wannan yaron da a ka haifa ba zamu iya kashe shi ba sabuda yin haka zai janyo mana shiga hadari dani dake, amma abinda zamuyi masa guda daya ne zamu iya cire masa son mulki a cikin zuciyarsa sai dai yaga ana yi" Tace"dama ai abinda nake so kenan kamar yadda ban hafi namiji ba haka bana so wata ta zo ta haifi namiji wanda zai gaji sarauta sabuda haka kawai a cire masa son mulki inda hali ma a sanya masa tsanar gidan nan ko a kada shi ina nufin ai masa kurciya kawai ya bar garin gaba daya" "Zamuyi kokari iya iyawarmu ke dai duk abinda muka umarce ki kiyi kar ki fasa,yanzu dole zamuyi yanke-yanke kuma zamuyi kwanan bori in gari ya waye sai ayi sadake sadake zakiga abin mamaki" Haka suka dinga dauki ba dadi kan zuwan Sarki Almansor duniya dan ganin sun sabauta shi tun yana yaro amma da yake yana cikin kariyar Allah hade da addu'ar iyaye babu abinda ya sameshi dan gane da mugun abun da suke masa kullum cigaba yakeyi har kawowa yau da ake masa maganar aure. *Wannan kenan* Wayarshi ce tayi kara ya dauka yana dubawa. Maddibo2 sunan da ya gani kenan, a hankali ya daga yayi gyaran murya gami da cewa, ka shigo ne"? Daga daya bangaran Maddibo yace"Eh gani a fada muna gaisawa da mai maimartaba yanzu zan shigo" "Ok in bangaran Ummi" "Shikkenan zan shigo yanzu dama ina so mu gaisa da ita wallahi" "Sai ka shigo" yafada yana kakarin kashe wayar Ummi tace"kai da waye" "Maddibo ne" Murmushi tayi tace"ai shi babu ruwanshi wallahi na lura baya biyewa sauran "yan uwanshi, ya kan zo lokaci zuwa lokaci muna gaisawa" "Shiyasa muke shiri dashi sosai Ummi kin san bana shiri da mutum munafiki" "Nan Maddibo ya shigo ya zube gaban Ummi yana kwasar gaisuwa.Cikin sakin fuska Ummi ta amsa masa tana tambayarsa mutanan gida,yace" Ummi ni yau kwanana biyu da dawo wallahi gidan ma sai jiya na shiga" "Ayya to masha Allah, in ka kara shiga a mika min gaisuwa gurin iyayen naka" "Zasuji in sha Allah Ummi" Nan suka mike tare Ummi tana ta shi musu albarka tana musu fatan dorewar zumuncinsu Ban garan Sa suka nufa suna tafiya suna hira yayin da hadiman da suke harabar gurin suka dinga kawo gaisuwa Maddibo ne kawai yake amsawa shiko uban gayyar tafiya kawai yake kansa a kasa tamkar wanda ba ya son kallon rana, Wasu hadaddun kujeru suka zauna wanda suke kewaye da kayattacan falon wanda ya sha shimfido irin na gidan sarauta ga wasu manya-manyan tuntu can kan wani tudu shima ya sha shimfidu masu kyau, kafin ka hau sai ka taka matattakala nan yake zama in zai huta in baya son fita waje Maddibo yace"na lura sam baka iya tarbar baki ba wallahi baka ji yadda makogaro na ya bushe ba, a ko ruwa ka bani in sha" Wani irin kallo yayi masa yana ya mutse fuska yace"in har nine zan kawo maka ruwa zaka kwana a nan" Dariya yayi ya mike yace"masifaffe kawai kar Allah ya sa ka bani,ai ina da kafafu" Tsaki yaja yana lumshe ido yace"kasan kana da kafafu meye na magana" Sabuda ka rai namin hankali ni zan kawo maka ruwa ko kar Allah ya sa ka sha" Maddibo yace"dan Allah kar kadame ni da masifa ka tsaya ka saurari abinda nazo dashi, Yafada yana zama kusa dashi yana kokarin bude ruwan goran sake hannunsa *Muje zuwa* [28/06, 06:33] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» ββββββ _*GIMBIYA BALARABA*_ ββββββ πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» _*Na*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani Writes Associationπ€π» ```Bisimillahir rahamanir rahim``` *π Ώ33* _____Cikin Yanayin maganar shi yace"Allah yasa magana ce me muhumanci, kazo kana wani damuna matsalata tafi taka" Ajiye robar ruwan yayi bayan ya gama sha yace" magana ce mai muhumanci mana, tun kafin inyi tafiya naso mu zauna muyi maganar Allah bai nufa ba sai yanzu" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba da cewa"akwai yarinyar da na hadu da ita wallahi a garin yawace-yawace na na resturant, kasan ni dai da son abinci mai dadi,kawai kwanaki Buba ya dauke ni muka shiga kasuwa gurin wani abokinshi, a lokacin yunwa duk ta ishe ni, dole tasa muka futo daga kasuwar domin mu samu abunda zamuci, kawai Buba yace a kwai gurun cin abinci mai kyau bakin kasuwar mu tsaya muci ba sai mun futa wajan gari ba.Tunda muka shiga gurin idona yayi tozali da yarinyar naji duk duniya babu macan da ta dace da ni kamarta, yanzu abinda nakeso da kai kawai ka shige min gaba gurin neman auranta domin nikam nayi mata" Maddibo ya karashe maganar tashi yana sauke ajiyar zuciya, fuskarshi cike da farin ciki da annushuwa. Wani irin tsaki Sarki! yaja yana wa Maddibo wani irin kallo yace"Lallai ka rai namin hankali wallahi , duk ka gama ya wace ya wacen ka kazo ka kare a gurin mai tuwo-tuwo sabuda tsabar ka rai na ni kazo kace in shige maka gaba, kar Allah yasa ka aure ta din" Maddibo ya karyar da kai kamar wani maraya yace"Kasan kuwa yadda nake son yarinyar nan, wato na kawo maka kuka na kai da nake tunanin zaka sharemin hawaye ka mara min baya a kan al'amarin zaka sace min gwiwa, bai kamata kayi min haka ba, Alhaji" "Kaga malam nifa ka fitar dani daga cikin wannan al'amarin haka kawai kai karasa wacce zaka ce kana so sai " yar tallah a bakin kasuwa, kai ka san "yayan tallan nan ba tarbiya ce da su ba, ka sani ma ko tana biye-biyen maza kawai kaje ka kwasowa kanka datti da karzuwa, ka bata mana zuri'a kar ka kara sani a cikin wannan shirmen naka" Cikin fusata!Madibbo ya dakatar da shi, yace"kayi karya kace wannan yarinyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108