Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,243 words 0 views Progress saved
Download Book

kwance kan cinyarta yace"yayi bacci kenan" "Baccin dai yake so yayi" tafad'a tana shafa kansa Girgiza kai yayi yace"yaran suna bani tausayi sosai, in sha Allahu maraicinku ya k'are" Wasu hawaye masu zafi ta d'auke tace"godiya a gareka gwarzo na zuciya ta,a yanzu banda kowa banda komai sai kai, nice kai, kai ne ni" Sosai Moddibo yaji dad'in wannan kalamin nata, wani irin nishad'i yake ji a zuciyarsa Hanyar gidan Sarki yaga ya nufa, bata kawo komai a ranta ba, sai da ta gansu dai-dai kofar shiga cikin gidan sarautar yana kokarin shiga da Motar tace" me za muyi a nan"? Fuska sake yace"bana ce miki k'ebantaccan guri zan kawo ki ba,kinga nan gidan babu wanda zai san kina ciki, Shiru tayi kawai gabanta yana wata irin fad'uwa, wata doguwar kwalta dake shimfud'e a cikin gidan suke bi, a hankali yake jan motar har suka iso shashen Sarki! me gadin gurin ya bude masa get ya shiga da Motar, gabanta ya dina fad'uwa wanda bata san dalili ba, duk inda ta kalla a gidan wasu irin tambari ne da zane-zane irin na sarauta anyi musu ado da wani abu mai kyalli,kasancewar a kwai haske tarwai a gurin, yasa taga hadiman dake kaiwa suna kawowa a gurin kowa da aikinshi, gurin aje mota suka nufa, tana ciki motar ta zama "yar k'auye ganin wasu shirga-shirgan mota masu kyau irin na masu a mulki,a fake a gurin, shima gurin k'ayata shi da wata rumfa, mai mai d'auke da ado mai tsari, parking d'in motar yayi, da sauri wani fade ya bude masa ya futo ya tsaya ya jingina jikin motar, ya futo da waya,yana k'okarin kiran Sarki! *_Muje zuwa_* *Comment Vote and Share* [24/07, 16:56] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿59* Ya zaune a farlo cikin kujerar shi ta hutawa, wani k'aramin littafi ne a hannunshi irin na addini yana dubawa, idanunshi sanye da farin tabarau na k'ara k'arfin gani, yana cikin wasu kaya na shan iska, cikin nutsuwa yake duba littafin,sai yaji wayarshi dake can kan kujera tana k'ara, alamun an kirashi, mik'ewa yayi a nutse ya k'arasa inda wayar take yana dubawa Moddibo ne, a nutse ya daga, gami da yin sallama, Moddibo yace" gani nan zan shigo da ita" "Wacece" yafad'a cikin sigar tambaya. Cikin mamaki Moddibo yace"har ka manta da maganar mu ta d'azu kenan"? Shi sam! ya manta da sunyi wata magana dashi,sai yanzu tsaki ya d'anja k'asa-k'asa yace"naman ta ni, ina fatan kaja mata kunne dai" "Baka da matsala da ita insha Allah" Kashe wayar yayi,ya ajeta kusa dashi ya cigaba da duba littafin dake hannunsa. A nutse Moddibo ya kalli Balaraba dake tsaye duk jikinta yayi sanyi, cikin zuciyarta take cewa anya batayi ganganci ba kuwa, ta guda daga gidansu,tabi wani namiji uwa duniya,duk tsiyar naka,shine naka amma tayi amanna da Moddibo ba zai cuceta ba. Hannun Usuman ya kama, suka fara tafiya, cikin nutsuwa yake k'ara kwantar mata da hankali, ganin da yayi jikinta yayi sanyi k'alau. Wata k'atuwar k'ofa me murfi biyu taga sun nufa, suna isa bakin k'ofar wasu bayi ne tsaye d'aya a gefe d'aya a gefe hannusu rik'e da wata sharb'ebiyar bulala, suna ganin Moddibo ne sai d'aya yayi saurin bud'e masa suka zub'e suna kwasar gaisuwa, a nutse ya amsa musu, suka gaida Balaraba, ta amsa a dake! sannan suka shiga ciki, Ji tayi k'afarta ta nutse a cikin wani abu mai taushin gaske, da sauri ta kalli k'asa inda taga wani kwantaccan kafet ya mik'e samb'al har inda Sarki! yake zaune, wani mugun k'amshi ne ya ziyarci hancin ta, lumshe ido tayi cikin jin d'adin k'amshin ta bud'e ido tana rarrabashi cikin katafaran farlon mai d'auke da set d'in kujeru uku, ko wanne da sentar teble d'inshi a tsakiya, a tishawa su Sadiya da Usuman suka fara, saboda sanyin air condition d'in dake farlo, wannan atishawar da yaran sukayi itace tasa ya d'ago kanshi cikin isa yana kallonsu daga can bakin k'ofa, shi kuma Moddibo dama ya gano shi a can in da yake hutawa, a nutse yake tafiya domin zuwa gurin, Balaraba kuwa sam bata lura da mutum a gurin ba da suka shigo, shiyasa da taga Moddibo yayi wani gurin sai ta zage,jiki tana ta kalle-kallenta na k'auyanci. Usuman ne ya rik'e mata hannu, yace"Yayarmu sanyi nake ji" jikinsa sai b'ari yake, kallonsa tayi,taga da gaske sanyin yake ji, ta kalli Sadiya taga itama ta takure cikin hijabi,sai mutsu-mutsu take, rarraba ido take a farlon tana so taga inda Moddibo yake, yazo ya kashe musu wannan abun mesa sanyi, bata ganshi, ba dalili yana isa gurin Sarki! ya saki wani labule me igiyoyi masu kyalli yana gudun kar yayi masa halin nasa har Balaraba ta gani shiyasa ya saki labulen, duk iya laluben ta ba taga Moddibo ba, ga Usuman bayan atishawar da yakeyi har da tari sai k'warewa yake, sam! ta tsani matsalar "yan uwanta, kalle-kalle take a farlo ko zataga inda ake rage k'arfin fankar a cewar ta can ta hango wasu abubuwa a manne jikin bango, kai tsaye can ta nufa, batare da b'ata lokaci ba ta sanya hannunta ta murd'a da k'afi! aikuww farlo ya d'ume da wani sauti!! dimmmmmmm! da gudu! ta matsa daga gurin tana zare ido,wanda yayi dai-dai da futowar su Moddibo da sauri ya k'araso inda suke, yayi saurin yaje ya saisaita komai, shi kuma Sarki! tun kafin ya k'araso gurin yake zabga mata harara, yana k'araso gurin yayi mata wani banzan kallo cikin wani irin murya yace" ke bagidajiyar ina ne,uhumm! kawai zakiyi tad'aga mana hankali baki iya abuba kice zakiyi, ni wallahi bana son hauka" yafad'a yana me zama cikin kujera tare da hard'r kafa d'aya kan d'aya Sai da ta kusan suma,lokacin da taji muryar sa, hankalin ta ya tashi, sai ta nemi miyau ko d'aya ta rasa a bakinta, sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya, tana tunanin abunda yasa Moddibo ya kawo ta gurin mutumin da baya k'aunar ta, wata zuciyar tace"k'ila had'a baki sukayi dashi,domin ya wulak'an taki,dama namiji ba d'an goyo bane. Shiru farlo yayi Modibbo ya rasa dame zai fara, Hannun Usuman ya rik'e da hannu d'aya, d'ayan hannun kuma ya rik'e Sadiya dashi ya kalli Balaraba yace"zo muje kinji Gimbiya" D'ago kai tayi tana kallonsa fuskarta a murtuke tace"ina zamuje, Yusuf dama ka d'auko mu ne domin a tozartamu, ni banga gurin zama ba anan" ta k'arasa maganar ta tana kokarin kama hannun Usuman dake cikin hannunsa, Tayi-tayi ta k'wace hannun daga cikin nasa ta kasa, rarrashin ta yake kan tazo ya nuna mata d'aki a saman bene,amma fafur tak'i ita k'okarinta ya bar ta ta futa da "yan uwanta domin sai yanzu ta fahimci abunda yake nufi ya kawota gurinshi, domin yayi mata cin mutumci sam baza ta iya zama inuwa d'aya dashi ba. Cikin k'asaita ya d'ago kansa yana kallon tababar da sukeyi, tsakaninsu ya kalli Moddibo yace" Meya sa kafin ka kawota nan baka fad'ama ta ba,? nifa wannan hayaniyar da kuke ta ishe ni, babu dole in zata zauna ta zauna, kai da zaka taimake ta kaine kake wani

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108