Skip to content

Chapter 41

Chapter 41

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

ta, tsayawa yayi yace" yawwa dama d'azu gajiya nayi na futa sabuda abokai na suna jirana a waje gashi baki dawo ba, sabuda haka yanzu me ake ciki, ki kawo kud'in da nace ki bayar domin za a sai wa Iro magani yanzu" "Kawu ina takkadun gida da shago na wanda Maimartaba da yaron shi ya bani gurin saukata"? Gabanshi ne ya fad'i sosai sabuda tun lokacin da ya karb'i takaddun daga hannunta yaje ya sanya su a caca lokaci guda a ka cinye shi cikin inda-inda yace" wannan maganar ki aje ta gefe guda domin bazan baki a hannun ki ba, sunan na adana miki" "Kawu kaje na bar maka su, kayi hakuri ni a yanzu bani da wani k'udi da zan baka, wallahi" tafad'a tana k'okarin shiga band'aki sabuda tasan tunda ta ganshi ya shigo afujajan tasan daga gurin caca yake, watakila an cinye shi ne ya tawo yana neman kud'i ruwa a jallo,tasan ko ta bashi k'udin gurin caca zai koma baba wani magani da zai sai wa Iro, tana jinshi yana zaginta ta shigewar ta band'aki, bayan ya gama zage-zagen nasa d'akin Lantana ya nufa sai kace zararre, cikin ikon Allah duk ya taddasu suna bacci, nan ya tsallake su ya shige k'uryar d'akin ya fara laluben inda, Uwa! take ajiyar kud'i Allah ya bashi sa'a ya ga wani k'aton banki, batare da b'ata lokaci ba ya fasa shi ya kud'i ne a ciki kimanin dubu bakwai, ya lissafa dubu biyar ya bar sauran dubu biyu, a watse a gurin ya tsallake yayi ficewar sa daga gidan. *Muje zuwa* ```Shin Balaraba in ta bar gidan ina zata koma?``` ```Idan Uwa! ta wayi gari taga bankin ta a fashe wace irin masifa ce zata biyo baya```? ```Ta yaya Sarki! zai fara bunkican Asalin Balaraba```? ``` Menene a zuciyar Sarki!dangane da Balaraba```? ```Maddibo ne mijin Balaraba ko Sarki!?``` *Duk wannan amsoshin suna gaba, ku cigaba da bina domin ganin wace irin waina za'a toya* *Comment* *Vote and Share* [16/07, 21:17] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿51* Bayan ta idar da sallahr tayi addu'oin ta kamar yadda ta saba, Usuman ne ya farka daga bacci ya fara kuka, " Yaya yunwa nakeji, abunda yaron ya fad'a, Sadiya ta hau tashi daga bacci,sam ta manta bata basu abunci ba suka kwanta bacci, Sadiya ta mik'e zaune tana mutsike ido, Balaraba tace"tashi kuci abunci,kinga Usuman ya tashi yana kuka,maza jeki dakin Iya ki dauko kular abuncin ku,da sauri Sadiya ta mike, ta nufi d'akin Iya, Iya na kwance kan dadduma bayan ta idar da sallah wani bacci ne me dad'i yake fuzgarta, zazzab'in ya sauka domin har wani gumi take, Sadiya tayi sallama, d'akin Iya ta mik'e zaune tace"Lafiya Sadiya"? Iya kular abuncin mu zan dauka" Iya ta koma ta kwanta,tana cewa "in kin futa ki ja min k'ofar, nan Sadiya ta d'auki kular ta futa daga d'aki, Bud'e kular Balaraba tayi tana duba abuncin, babu abunda yayi duk da yake dafa duka ce, har yanzu da zafinsa, nan ta zuba musu suka fara ci pure watar ta dauko musu guda biyu, Usuman yace" Yayarmu ke bazaki ci abuncin ba"? "Zanci mana Usuman kai da kuci ku koshi" tafad'a cike da tausayin yaran, bayan sun gama ta rakasu suka wanke hannuwan su, suka dawo ta gyara musu kwanciya suka kwanta, nan ita kuma ta cigaba da had'a "yan kayanta da suka rage tana sakawa cikin a kwatu, domin taci alwashin barin gidan gobe daga yau ta bar kwana a gidan, Sai wajan karfe d'aya saura na dare sannan ta kwanta, cikin ikon Allah a subar fari ta tashi daga bacci ta futo ta d'aura alwala ta koma d'aki da sauri ganin ana iska sosai hadari ya had'u har an fara yayyafi, tanaji massalacin bayan gidansu sun tayar ta bisu sallah, bayan an idar da sallahr rayi addu'onta, ta cigaba da zama kan dadduma tana jan carbi kamar yadda ta saba, wajan karfe shida, ta fara jin motsin mutanan gidan, sun fara futowa, bacci ne yake fuzgar ta kad'an-kad'an sai taji hayaniyar Uwa! tana buga kyauran d'akinta ta tare wa Sallau hanyar wucewa tana kunzuma masa ashar! "Wallahi tallahi babu wanda zai yi min wannan d'anyan aikin sai kai,domin dama kasha auna fasa min asusu na,ina kama ka,shine jiya ka faki idona, sai da kabari nayi bacci kafasa ka kwashe min kud'i ,wallahi Sallau ko ni ko kai a gidannan domin bazan sha wahalar neman kud'i na ba,ka dinga bin dare kana sacewa, eheee! ba zata sab'uba bunduga a ruwa! Ta karasa maganar tana tattaro wuyan rigarsa ta cukume shi, " Shikkenan daga kin ga an fasa miki banki an kwasar miki kud'i sai kice nine sabuda kin raina ni duk b'arayin "yayanki bakya tuhumar kowa sai ni, to komai masifar ki dole ne ki sake ni,inje inyi alwala inyi sallah tunda ke baza kiyi ba, baza ki hanani yi ba" "Kai dallah! rufe min baki" tafada tana kai hannuta dai-dai bakinsa kamar zata gwab'e ta cigaba da cewa"kai har kana da bakin da zaka fad'i wata magana a kan sallah, akwai babban makiyin Allah irinka, ai Sallau in kaga na cika ka agurun nan to tabbata ka futo min da kud'ina" Tafad'a tana k'ara tattaro wuyan rigar sa, k'arfi yasa ya angije ta, tafad'i k'asa ragwajab! ya futo daga d'akin da sauri, ya nufi k'ofar futa daga gidan, da gudu ta biyo bayanshi tana huci! cikin tashin hankali da masifa tace" ni ka tunkud'e ko, har kasa na fad'i a gaban yara na, to yau zanga yanda za'ayi ka futa daga gidan nan mutukar ba kud'ina ka bani ba" Mutan gidan duk sun futo suna kallon ikon Allah, Uwa! ta shak'e wuyan Sallau sai huci take, dama d'azu shammatar ta yayi ya ingije ta d'azu domin Uwa tana da mugun k'arfi sai kace doki haka take, K'ifta ido yake kamar b'era a ruwan zafi, bakin sai karkarwa yake,ya rasa abun cewa, duk alamu na rashin gaskiya ya bayyana a tattare da shi. "Ke dan ubanki sakar min wuyan d'ana kar ki kashe min shi ki cuce ni" Lanatana tafad'a lokacin da ta karaso inda suke, cikin tashin hankali take k'okarin b'anbare hannun Uwa!daga wuyan Sallau, doke hannun Uwa tayi, cikin rashin kunya tace"kinga Lantana, matsa dan Allah sam baki iya komai ba sai munafurci da kwad'ayi, in kinga na sake shi to sai ya futo min da k'udina ehee!" Gefe guda Lantana ta matsa tana rik'e hannun ta domin taji zafin buge mata hannu da tayi tace"shikkenan,to kashe shi ki huta mara kunyar yarinya kawai, a gidan ubanwa naje nayi k'wadayi da har kike kirana da haka" "Sai kiyi kuma kanki a keji" Uwa! tafad'a tana k'ara matse Sallau jikin garo Walidi ne ya shigo gidan, tashin sa kenan daga bacci ya fara jiyo hayaniya sabuda haka a fusace ya shiga gidan, cikin mamaki yake bin iyayen nasa da kallo, "Ke!dallah, wai menene haka, kuke sai kace wasu yara,k'ananu, ke Uwa! sakar masa wuya" yafad'a cike da bada umarini kamar shine Ubansu, "Walidi in kaga na saki wannan mutumin to sai ya futo min da

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108