Chapter 6
Chapter 6
Balaraba gadan gadan! Dama sun saba dambe Dan su Shamsiyya basu da Hankali in dai Abu ya hadaka dasu Abu kadan sai a fara dambatuwa. Balaraba tayi saurin kaucewa daga jikin rijiya ta tari Shamsiyya tun kafin ta karaso suka kacame da kokawa Abin Mamaki!! Mabaruka tafara daukar Abubuwa tana dukan Balarabar dashi ganin ta kayar da Shamsiyya tana duka . Sai dura mata Ashar Mabaruka take ta Uwa ta Uba. Iya ta shiga tsakani tana rabawa gami da ruqe Balaraba Amma Ina!! Balaraba taqi rukuwa domin dama in tai zuciya fadanta baya rabuwa. Shiko Kawu sallau barin gurin yayi yana tsitstsinewa su Shamsiyya a zuciyarsa domin babu Halin yayi a fili sabida tsoran Masifar Uwa. Uwa dataga Ana cutar "yarta sai kawai ta daga ruwan daudar da take wanki dashi cikin roba ta kwararawa Balaraba a jiki tundaga tsakiyar kanta har zuwa qafarta tana ta zabga Mata zagi gami da mugun fata!! Da kyar Iya ta janye Balaraba daga kan shamsiyya tana bata hakuri gami da yi mata Fada, Shamsiyya da tasamu ta mike sai taciga ba da zagin Balaraba tana jin fan ta da kwanonisu Na cin Abinci Wanda suke gefe Dan qazanta har yanzu ba'a wanke ba qudaje sai bi suke gami da ruwan wanki da Uwa ! take kwara musu Har tasamu nasar jifanta a kanta gurin ya tasa ,cewa"take Wallahi sai naga bayanki Dan Uwarki karuwa Uwar tamu zaki dinga zagi shegiya wacce ba'a san Asalinta ba" Bakinci tamkar ya kashe Balaraba sai tafashe da kuka, a gurin su Sadiya da Shamsu kannanta suna taya dawowarsu kenan daga makarantar Allo,yara duk sun cika gidan, Iya ta janye Balaraba ta kai ta dakinta tana rarrashi tace"ko da yaushe ina fada miki ki daina Daka ta tasu Mabaruka su ba hankali garesu ba gashi yau a cikin farin ciki kike kinyi saukar Alku'ani mai girma Amma zaki bata wayonki Dan Allah ki daina kulasu. Cikin kuka tace"iya kinajin zagin da suke min fa wai mai Na tsarewa Uwa ita da yaranta suka tsane ni ,nifa basa bani ci basa bani sha komai bi nakewa kaina ni nake fita in nema in ciyar da kaina da kannena to gaskiya nagaji zan siyar da gado Na kawai in bar musu gidan gwara inje in kama haya sai yafi min" "Aa Balaraba kina nufin zaman kanki zakiyi bazai yihuba dama yaya Lafiyar kura kullum cikin yi miki sharri suke duk Wanda yaji cewar kin gama daki shikkenan sai zancensu ya tabbata ,ki kara hakuri kinji ko kwana nawane zaki yi Aurenki . "Aa Iya ki kyaleni kawai "tafada tana share hawaye. Iya tace"Aiko bazan kyaleki ba Balaraba yin hakan yana nuna cewar cin Amanar Dan Uwana Ayuba ,Sam baicancanci haka ba bayan haka kuma zumunchi bai CE haka ba Share hawaye tayi ta kalli su Sadiya da shamsu Wanda suke zaune sun zuba mata ido suma suna share hawaye,tace "kunci Abinci"? Girgiza kai sukai Alamun A'a. Mikewa tayi ta karbi mukullin dakinta gurin iya tace"Ku taso Ku je Ku siyo indomee sai in dafa muku kafin in daura girki" *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* ππππ 08089965176 [04/05, 03:04] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? π§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββ *πΎGIMBIYA BALARABA*πΎ π§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββ *βπ»writting by* *Binta Umar* _*MAMAN ABDUL WAHABU*_ ~*MRS AHAMAD GWADABE*~ *π Ώ10* Dakinsu Na gado ,ta bude musu ,suka shiga ,tana jin su Mabaruka da Shamsiyya ,sai zaginta sukeyi har yanzu ,sai tayi musu banza, Tafito da kudi gudar Dari biyar Sabuwa dal! Tabawa Sadiya ,dake tafi Isyaku ,wayo ,tace maza taje ta siyo musu indome guda hudu ,sai ta dafa musu kafin ta Dora musu Abincin dare. Cikin Farin ciki Sadiya ta kar6a ,ta tafi kantin Abbah ,dake bakin layinsu siyowa Sai Murna takeyi dake yarinyar ,tana son. Indomee sosai ,shiyasa kullum said tayiwa Aunty tasu Addu'a in tayi Sallah,sabida duk Abinda suke Nema tana musu . *wannan kenan* *ASALIN LABARIN* ___________________ Malam Tanko Makeri Shine Ai nihin sunasa ,Wanda jama'a suke kuranshi dashi ,Amma A salin sunansa dayyabu " to tun yana yaro Mahaifinshi ya sanya masa Tanko kasancewar sunan Mahaifinshi ne dashi Shiyasa sunan ya buya idan ba Tanko Makeri kace ba babu Wanda zai gane. Mutum ne shi Wanda Allah yayi masa baiwa da Fasa ta qere qere duk Abinda ya kalla sau daya to in sha Allahu nan take zai qera makashi ,tamkar daga kamfani Shi kadai Mahaifinshi ya haifa ya koma ga Allah. Shi kuma tun tasowarsa mutum ne mai Auri saki ,Matarshi ta Farko Lantana itace Uwarsu Kawu Sallau da Kawu Maman ,Matarshi ta biyu "yayanta duk mata ne su biyar ,haka ta zubesu gaban Lantana ,tayi tafiyarta ,Lokacin da Auran ya Mutu. Lantana wata irin mace ce mai zuciyar kafurai bata da imani ko miskala zarratin,ita ke daura yaranta a kan mumun dabi'a Idan Tanko ya fita sana'arsa sai ta daurawa "yayan kishiyarta ,mata talla ,tace duk inda zasuje suje su siyar mata tallah har da daddare daura musu take ,idan suka qi kuwa tasa Sallau ya Zane su. Tun Tanko bai Sani ba har yazo ya sani ,yayi tai mata fada,budar bakinta sai cewa tayi itafa baza ta zauna da gurda gurda "yan mata gida daya ba batare da ta more su ba idan baya so ta daura musu tallata to yayi musu Aure, Dake Tanko Jan wuya ne a gidanshi ,ya tsawar mata ,yace "gidansa takyale masa yara suyi karatu ,tukkuna idan Miji ya fito ai za'ai musu Auran. Lantana taqi ji ,Tanko yana sa kafa yana fita zata fafaki yaran da faratin tallah ,suna kuka suke tafiya, Karshe Suka yanke shawarar guduwa gurin Uwarsu, Aiko ranar da Asubah suka fito dukkaninsu suna labewa suna jiran babansu ya fita sallah su gudu Tanko ya fito kamar yadda ya saba ,ya tsaya shagon su Sallau ,domin tashinsu ,suje massalaci ,daga bakin kofa ya tsaya gami da bubbuga kyauran ,ya wucewarsa Su sallau ko sunajinsa ,da suka fahimci ya kauce daga gurin sai suka cigaba da baccinsu ,dakin sai tsami ne yake tashi ,sabida ,dama bawata tsaftace dasu ba ,sai su fi sati basiyi wanka ba. Su Atika kuwa bayan sun tabbatar da wucewar babansu ,sai suka fito sadaf sadaf zasu gudu. Abin Mamaki ! Sukayi gware da Tanko ya dawo domin daukar chazbah , Sai ya kara haske fitilar dake hannunsa yana kallonsu daya bayan daya,ga Atika riqe da katuwar jaka. Yace"INA zakuje ne"? Sai suka fashe da kuka dikanninsu , Kukan da yayi sanadiyar Farkawar Lantana daga Barci duk da tana cikin Uwar dakinta, Tafito da sauri jin kukan da soro ,tana Addu'a Allah yasa ba daya daga cikin "yayanta bane ya mutu ,kanta ko Dan kwali babu. Me za ta gani su Atika ne tsaye riqe da jaka suna zabga kuka ,ga babansu a tsay" Tace"Malam Lafiya dai in ce ko "? Wa"yan nan shashashan yaran sun tashe ni daga bacci" Ko sauraronta bai yi ba ,ya cigaba da tambayar su Atika ina zasuje da Asubar nan. Atika tace "babah mungaji da Azabar da ake gana mana ,zamu tafi gurin babarmu, Lantana tayi salati kamar gaske tace"Au!sharri zaku kullamin gurin Ubanku "ooo ! Ni Lantana Na hadu da "yayan zamani, Sai ta hau kwala Sallau kira. "Sallau" Sallaau!! Sallau"!! *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108