Chapter 44
Chapter 44
yayi yace"gaskiya Mama yarinyar nan tana da fada! a gurinku, ke da Maimarta ba, shima lokaci guda ya amunce da maganar, ni kam banawa Moddibo sha'awar auran yarinyar" Da murmushi a fuskar ta tace"D'a duk na kowa ne, kai dai kayi masa fatan alkairi kawai" "To me nace yanzu, tunda yaji ya gani yana son ta a haka, Allah ya sanya alkairi" "Ameen, abunda zakace kenan" Hira sukayi irin ta tsakanin d'a da uwa sannan yayi mata sallama ya futa, ***** Karf'e takwas da rabi na dare, ya shirya tsaf cikin k'ananun kaya, riga da wandon jins, masu kyau ya sanya farin galashi a idonshi, sai a gogo daya d'aura a hannushi na silvar ya tsunsa uku sanya da wasu manya-manya azurfa masu kyau da tambari irin na sarauta, wani bak'in takalmi ya sanya a kafarshi mai kyau da tsada, yayi wani mugun kyau sosai, duk wanda ya ganshi bazai gane Sarki! bane sabuda yadda k'uruciyar shi ta futo sosai d'an gemunshi ya kwanta yayi luf a fuskar shi sai shek'i yakeyi, babu wanda zai ganshi yace, shine sai wanda yayi masa farin sani, Turaranshi ya fesa wanda yake amfani dashi me suna (pure love) nan take d'akin ya d'ume gurin da k'amshi a nutse ya futa. Buba Direba na jingine jikin mota, Sarki! ya futo sai yayi sauri ya b'ude masa motar tun kafin ya karaso, Cikin yanayin muryar shi yace"Malam buba, ba da wannan motar zamu futa ba" "Allah ya taimake ka, da wacce zamu futa"? Wata bak'ar toyota ya nuna masa da hannunsa yace" muje a waccan" Da sauri Buba Direba ya nufi inda motar take, yana buge ta, duk da tsaf take babu wata kurar arzki a jikinta nan ya bud'e masa ya shiga ya zauna cikin nutsuwa Buba yaja motar suka futa daga gidan. *Comment* *Vote and Share* [18/07, 20:08] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^° _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®{REAL BINTU BATULA}👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` _ZAMANI WRITES_ _ASSOCIATION_🤝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rashim``` *🅿53* Sai bayan sun futa daga gidan ne, Buba ya d'an waiwayo A hankali yana kallon Sarki! dake kishin gid'e a bayan motar,yace"Allah ya taimake ka,ina muka nufa ne"? A nutse yace"muje wannan unguwar da mukaje tare da Moddibo kwana uku da suka wuce, Maimartaba ya umarce ni da bunkicen wani abu" "To masha Allah ranka ya dad'e Allah ya bada sa'a" Buba ya fad'a yana cigaba da tuk'in mota, a nutse. Yau da wutar nepa a unguwar sabuda haka ko ina da akwai haske tar, can gefe guda Buba yayi parking din motar, yace"Yallab'ai gamu munzo" A nutse ya dago kanshi yana bin gurin da kallo, wasu gugun! matasa ya hango sunfi su a shirin a bakin wani kanti, wasu na shan rake wasu na cin gyad'a mai b'awo, yayin da wasu suke cikin a wara, a wata k'atuwar takkada, sai hira ake suna dariya, cike da rashin kamun kai, ya dad'e yana nazirinsu, kafin ya bud'e mota ya futo a nutse, ya gyara zaman gilashin dake fuskarsa, Buba yayi saurin futowa shima, a nutse ya kalleshi yace"ka koma ka zauna cikin mota,Buba bana buk'atar rakiya" Hannu ya d'aga alamun jinjija yace"a futo lafiya, ranka ya dad'e" ya koma cikin mota kamar yadda a ka umarce shi, A hankali ya rik'a tsallake kwatoci masu d'auke da dagwalo na k'azanta, har ya k'arasa gurin wad'an nan matasan. "Assalamu alaikum" sallama ya fara yi musu, cikin muryarshi mai dad'in sauraro. Hannu ya mik'a wa na kusa dashi yace"barka da dare abokina" "Barka kadai" Salihu ya fad'a lokacin da yake mik'a masa hannun sukai gaisa, wani irin taushi yaji lokacin da hannusa ya had'u dana Sarki! da sauri ya d'ago kanshi yana kallon fuskar Sarki! gefe guda kuma wani mugun k'amshi ne ya cika musu hanci, shiyasa duk sukayi d'if! suka bar hayaniyar da suke suna kallo Sarki! dake tsaye,hannusa cikin na Salihu, Gyaran murya yayi yace"Abokina in babu damuwa ina son in maka wasu tambayoyi" Duk da Sarki! yayi basaja,domin kar a ganeshi, amma muryarshi taso ta tona masa asiri sabuda duk wanda yake cikin garin har in yana sauraron kafofin sadarwa,to muryarshi ba b'oyayyi b'ace mussaman da azimi,da lokacin aikin hajji, akwai wani Maudi'i yake gabatarwa na addini wanda kafafan sadarwa suke sawa kullum, wannan Maudi'i kuwa shi kad'ai yake gabatar dashi sai dai kawai, a tura shi Media, shiyasa Salihu ya furgita jin kamar Muryar Sarki! magajin Sarki, yace"babu komai in sha Allahu zan baka amsar abunda zaka tambaye ni mutukar na sani" Fuskarshi a sake yace"muje can gurin maganar sirri ce" Jiki a sanyaye Salihu ya mik'e ya bi bayan Sarki! sauran abokanshi suka bisu da kallo cikin mamaki, Kai! wannan guy, d'in me ya kawoshi gurin Salihu, Allah yasa dai ba wani abun ya jawowa kansa ba" Maganar daya daga cikin matasan dake gurin kenan, "To wa yasa ni mudai babu ruwan mu" na kusa dashi yafad'a ya cigaba da shan raken sa. Can wani gefe suka tsaya,wanda yake da k'arancin haske, A nutse Sarki! ya kalli Salihu yace"Abokina kasan wata yarinya Balaraba a nan unguwar"? Shiru yayi na tsawan minti biyu yana tunani can yace"Eh na san wata a can lungun take" yafad'a yana nuna lungun gidansu Balaraba, ya cigaba da cewa, "amma gaskiya ba a fiye kiran ta da sunan ba sai a gidan su mu dai matasa muna kiranta da Gimbiya sabuda girman kanta, gashi ita ba " yar kowan kowa ba, a na tunanin ma Uwar da ta haifi baban ta Mayya ce" Shiru Sarki! yayi yana nazarin maganar yaron, daga bisani yace" kasan gidan nasu ne,inaso ka rakani gurin baban ta" "Nasan gidan mana" Salihu yafad'a ya cigaba da cewa"k'anin ta Walidi abokina ne, Allah yasa kai ma ba wani abun tayi maka ba, dan jiya ma wanta Iro ta cirewa d'an yatsa guda, yanzu haka yana can kwance yana jinya" Cikin mamaki Sarki! yace" garin yaya mace kamar wannan zata cirewa saurayi kamar ka d'an yatsa guda, dame ta cire masa"? "Humm Wannan yarinyar ai inda kasan " yar daba haka take, da wuk'a take yawo, mu dai inda mukaji wai tana so shi yayan nata yayi lalata da ita dama kuma shine zai aure ta, shine da yak'i amuncewa ta futo da wuk'a ta yanke shi, muje in raka ka kaji a bakin mutan gidan nasu" Cikin mamaki Sarki! yake bin bayan Sallau, yana al'ajibin abunda Salihu ya fad'a masa yanzu al'amarin yarinyar har ya kai haka Yayi mamaki sosai da inda yaga yarinyar take rayuwa a rin wannan lugun mai tattare da k'azanta da bola amma take wa mutane kallon banza, Shamsiyya na zaune a kujera "yar tsuguno tana lissafa cinikin a wara, ta bisu da kallo, da Sauri Sarki! ya dauke kanshi zuciyar shi na wani irin tashi, sabuda kauri gami da zarnin futsari da warin bola da ya cika masa hanci, hankici ya futo da shi yana d'an goge fuskarsa cikin basarwa, Salihu ya k'arasa kusa da ita yace" Shamsiyya babanku yana nan"? "Bayanan menene"? tafad'a kai tsaye "Dama wannan guy din ne yake neman shi" Da sauri ta mik'e ta karasa kusa da Sarki! cikin kwarkwasa tace"sannu ina wuni"? Dauke kai yayi da sauri, sabuda wani irin k'auri da yaji
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108