Chapter 20
Chapter 20
ruwana" Shiru tayi tana nazarin maganarahi, tasan Yaron ta da tunani da hangen nesa yana da nutsuwa, nutsuwarshi ce ma tasa Maimarta ba ba ya zartar da wani abu da ya shafe shi ko na menene sai ya nemi shawarar dan nasa Cikin nutsuwa tace" duk na fahimci abunda kake nufi, ina so ka yi min biyyaya da dukkanin abinda na umarceka dashi, sabida kasan halin yadda nake rayuwa cikin kishiyoyina, da sauran matayen waziran Mahaifinka, mutukar kaki yadda da wannan abu to babu shakka zasuce nice na hanaka auran "yar uwarka, kasan halin mahaifin ka shi babu ruwanshi da kananun maganganu na gidan nan, sabida haka nake neman alfarma a gurinka ka daure ka aureta, na san yadda kake a tsaye duk fitinar Halisa sai tayi laushi, sabida nasan baza ka yadda da shirme ba" Ummi ta karashe maganar tana sauke a jiyar zuciya Shiru dakin yayi na tsawon minti biyu sannan yayi gyaran Murya yace" Ummi na amince da abinda kika umarce ni, zan auri Halisa domin in faranta miki rai, amma kin san ba zan yadda da kananun maganganu na cikin gidan nan ba, za'ayi rigima dani, mutukar naji wata magana ta biyo ba,domin ba zan lamunci wani ya zage min ke ba rayukan zasu baci, maganar Halisa ce, na kuma amince zan aureta shikkenan sai su bar maganar" *Yanzu muka fara* [26/06, 22:19] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πΈπ»πΈπ» πΈπ»πΈπ» ββββββ _*GIMBIYA BALARABA*_ ββββββ πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» _*Na*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani Writes Associationπ€π» ```Bisimillahir rahamanir rahim``` *π Ώ32* ______Cikin nutsuwa Ummi tace"alhmdulilahi in sha Allahu babu abinda zai biyo baya sai alkairi,sai dai ina san ka rage zakin zuciyar nan taka kuma ka din ga fitowa cikin jama'a kwata-kwata kwana kwana biyu na lura baka zaman fada ko zaka iya fadamin dalili"? Yafi minti uku baice komai ba daga bisani ya dago kanshi yana kallon mahaifiyarshi yace"Ummi kin san halina bana ganin ana yin ba dai-dai ba in yi shiru duk ranar da mai martaba bai fita fada ba in ya wakiltani na lura su galadima basa su mussaman Baba waziri,Ummi su mulki ya dama sam ni bana sha'awar shi zaman fadar ma dan dai Mai martaba yana so ne,shine dalilin da ya sa kawai bana son zama sabuda zakiga suna yin abunda bai dace ba, kuma ba'a isa ai magana ba" Shiru Fulani tayi tana nazarin maganar dan nata tasan a kwai badakala a cikin gidan duk ranar da Mai martaba ya fadi ya mutu,domin dukkaninsu abinda suke wa kenan mulki, shiyasa suka tsaneta in banda tana da karfin arziki a gidan da tuni sun koreta babu irin jifan da basa mata tunda suka lura tana da ciki shikkenan ko wanne ya tashi hankalinsa, kishiyoyinta tamkar su mutu Asiri ko ta ina,in da Allah ya taimaka itama ba a kwance take ba maca ce mai addini da addu'a shiyasa duk asirinsu baya kamata ko ya kamata bayayin wani tasiri yake karyewa, a taikaice dai sai da cikin Almansor ya kai wata goma da wata goma sanan ta haifeshi lafiya sumul gida ya kace me da murna,da hayaniya sarki Almustap ya haifi da namiji kasancewar duk "yayanshi mata ne su goma sha uku uwargidanshi kawai ta haifi " yaya maza uku, kuma suka dinga mutuwa daya bayan daya, shine malamin ta yace mata kishiyar ta ce take kashe matasu sabuda tana so ta haifi danta wanda take so ya gaji kujerar mahaifiyarshi dole sai ta tashi tsaye, nan ta daga hankalinta ta dinga kiran malamai gami da "yan bori suna mata aiki a gidan, a kan duk dan da Mai martaba zai haifa in dai namiji ne to kawai ya mutu tun kafin yazo duniya,sosai take aiki da aljanu a gidan duk dan kar wata tazo ta haifi da namiji Abin da bata sani ba shine sauran "yan uwan Maimartaba Almustapah basa so ya haifi da namiji sabuda gudun kar mulki ya koma hannunsa bayan babu shi. Babu irin abinda basa yi na shirka domin ganin bayan Sarki dan su samu damar hayewa kujerar mulki Fulani ita ce matar maimartaba ta uku lokacin da sarki ya aure ta sai a ka dinga surutai cewar ya auri " yar malaminshi kuma ba "yar sarauta ba ce, nan kishiyoyin ta suka sanya ta a gaba lokacin tana bata da shekaru da yawa batafi shekara sha uku ba, da yake yarinya ce mai hankali sam bata musu rashin kunya in suna zaginta sai dai ta shige gurinta tayi kuka ta gayawa Allah damuwarta, kusan shekarar ta goma sha biyar a gidan,sannan Allah ya bata ciki da yake doguwar maca ce sai cikin ya boya in banda Maimartaba babu wanda ya sani a cikin gidan,sai ko jakadiyar ta mai suna Shafa'atu da yake ita take hidima da ita, Cikin ikon Allah da lokacin haihuwa yazo ta haihu lafiya babu matsalar komai.Jakadiya Shafa'atu ce ta gyara jariri tsab ta kwantar dashi a wani kayataccan gado mai kyau irin na yara,sannan tazo ta taimakawa mejego itama ta shirya tamkar ba itace ta haihu ba, Nan ta zube a gabanta tanayi mata sannu tace" ranki ya dade ki fadi abinda kike bukatar ci yanzu sai a kawo miki,sai ki kwanta ki huta" Fulani ta sauke ajiyar zuciya kana kallonta kasan tana da damuwa tace"bana bukatar komai yanzu kawai kije fada ki kira min maimartaba" Da sauri ta mike ta fita daga dakin domin cika umarnin da a ka bata, Lokacin da ta isa fada cike take duk su Waziri Zayyanu da Galadima da Wamabai hade da dakatai duk suna gaban sarki a gurfa ne, ta karasa taje ta kwashi gaisuwa,sannan ta isar da sakon Uwar dakinta nan fada tayi shiru kowa yana mamaki yarinya karama zata aiko kiran sarki,kowa jira yake yaga zai je ko bazai je ba, abin mamaki! maimartaba ya mike a nutse ya kalli mutanan gurin yace"zan shiga in fito yanzu a cigaba da tattauna maganar da muke kai insha Allahu in nadawo za'mu samu mafita" yana gama fadar maganarshi ya wuce wasu dogarawa uku suka bi bayanshi suna baza babbar riga,tare da fadi takawar lafiya gaba salamun baya salamun Sarki mai adalci a fito lafiya, Jakadiya Shafa'atu ta bi bayasu itama tana nata kirarin. Nan baki kofa suka tsaya bayan Maimartaba ya shiga bangaran Fulani Tana zaune ita kadai tana tunanin irin rikicin da zai tashi mutukar mutanan gida suka ji cewar ta haihu kuma da namiji wadanda basu san sa zaman cikin ba ma cewa zasuyi karya ne,ita tsoranta kar taje a sabauta mata yaro Maimartaba yayi mamaki ganin ta tsaf tamkar bata haihu ba.Sannan ga yaronsa mai kama dashi mutuka tamkar an tsaga kara, a hannuta tana shayar dashi, sai ya karasa kusa da ita da sauri fuskarsa dauke da murmushi yace" Fulani mai halin manya mace ma kara da kawaici da kunya,yau na kara tabbatar wa cewa ke alkairi ce a gare ni" A nutse ta mika masa jinjirin tana murmushi tace"gaskiya naji dadin wannan yabon da kayi min, yau Allah ya sauke ni lafiya kaga bawar da Allah yayi mana" Hannu biyu yasa ya karbi jariri cikin farin ciki yace"masha Allah dukan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da yayi min wannan bai wa Allah shine abin godiya" Kunneshi ya kara
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108