Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,247 words 0 views Progress saved
Download Book

wani abu, ni Sunana Balaraba Ayuba Tanko kamar yadda kasani, kana ji na ko"? tafada tana hura hanci, kana ta cigaba da cewa, "kai kuma in har ban mance ba Kai ne Almansor Sarki! dan Sarkin Almustapah, hakane ko ba haka ba"? tafada cikin sigar tambaya gashi ta tsare shi da ido, tana tsaye babu fargabar komai a tattare da ita, Cikin jarumta tacigaba da cewa" Wallahi baka isa kazo har kofar gidanmu ka ci mun mutumci ba, domin ni bani na kira ka ba" Tsit!!!! gurin yayi Maddibo yana mamakin jarumta irin ta Balaraba,ko shi da yake Namiji bazai iya tsayawa gaban Almansor har ya gaya masa magana irin wannan ba, sabuda kwarjinin da Allah yayi masa. A tsanake ya dago kanshi fuskarshi a murtuke, ko da wasa bai kalli inda take tsaye ba, murya a cunkushe yace"in kagama abunda kake kashigo mutafi,in kuma baka gama ba zan wuce kawai, sai katawo" "Wai me yake Faruwa ne,? tsakaninku naga kamar a kwai abunda kuke boya min, gaskiya banji dadin irin yadda kuka gaisa da junanku ba, abun bai min dadi ba" Maddibo ya fada yana kallon Balaraba, Murmushi tayi mai cike da takaici tace"Yusuf abokinka dan rainin hankali ne, wallahi ni kuma kasan bana daukar raini, ni "yar talaka ce, amma ban nema gurin wani ba sabuda haka babu mutumin da ya isa ya zage ni ban rama ba" A fusace!Sarki ya bude murfin motar Balaraba na tsaye jiki tayi taga-taga kamar zata fadi,cikin tsoro ta matsa gefe,gabanta yana dukan uku-uku, duk da cewar babu wadataccan haske a gurin sai hasken farin wata, hakan bai hanata hango tsantsan bacin rai a fuskarsa ba, ganin fitowarsa yasa Buba Direba dake can gefe a tsaya yayi saurin karaso gurin yana baza babbar riga, ya na zuwa ya zube a gurin gami da dunkule hannunsa alamun jin jina, yace"ranka shi dade, a kwai abunda za'ai maka ne" Cikin wani irin murya yace"Babu abunda za'ayi Buba koma inda kake" Buba ya mike da sauri, kanshi a kasa yace"Allah shi taimaki Yarima Sarki Allah ya ja Zamanin ka" Da Sauri Balaraba ta dauke kanta, ganin ya maido da hankalinshi kanta, ya zuba mata ido, kawai yana kallo, Lokaci guda ta nemi nutsuwar ta tarasa jikinta yayi mugun sanyi, ganin shi tayi yana matsowa kusa da ita a hankali, fuskarshi a murtuke! jinsa daf da ita yasa ta jingina da jikin motar a karo na biyu, kamshin turaransa duk yq cika mata hanci, sai sa ya tsaya daf da ita sosai har numfashinsu yana haduwa, sannan ya kafe ta da idanunsa masu tsananin kaifi,da kassara jikin duk wata "ya mace me ji da kanta A nutse a bude bakinsa yace" Duk abunda kikayi a yanzu, bazan yi mamaki ba sabuda nasan zakiyi abunda yafi haka" Wani irin kamshi taji yana futa daga bakinshi, lokacin da yake mata magana, kanta ta sunkuyar kasa kagabanta na lugede tunda take, babu wani da Namiji da ya taba kusantar ta kamar haka, kokari kawai take ta kwaci kanta, amma babu hali,sabuda yadda ya yi bake-bake a gurin,duk tsahonta ya rufe ta. Yayi tsawan Minti biyu kafin ya kara cewa komai kana ya cigaba da cewa" Babu mamaki duba da yanayin unguwar da kika taso a ciki, babu abunda yake damunki sai tsan-tsan jahilci, da gidadan ci , da Zama cikin maza, a cikin kasuwa, shashashar yarinya kawai, zan koya miki hankali, zaki nuna min da me kike gadara, da kikewa kanki kallon ke wata aba ce" Yana gama fadin wannan maganar ya tattaro miyau, a bakinshi ya dai-dai ci fuskarta ya tofa mata, ya dora mata da wani banzan kallo yace"ina sauraron ki da duk hukuncin da zaki dauka a kaina" *Comment* *Vote and Share* [06/07, 13:37] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ† _*GIMBIYA BALARABA*_ βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ†βˆ† πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ» _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*Zamani Writes Association*_🀝🏻 ```Bisimillahir-rahamanir-rahim``` *Real Bintu BatulaπŸ‘„* *πŸ…Ώ39* Hannu kawai ya dagawa Buba Dreba da sauri ya karaso gurin, Cikin nutsuwa ya mai da idonshi kan Maddibo yace"Ni zan wuce, naga alamar baka da ranar tafiya, ka kawoni gurin yarinyar mara tarbiyya tana neman ta zageni" Cikin daga murya Balaraba tace,"to in na zageka me zaka yimin karkari kasa a daure ni to ka dade baka sa an daureni ba,kuma zakasan wanda ka tofawa miyau dinka,wallahi sai na rama kaji na rantse" Cikin hayaniya take fadar maganar,hawaye yana kokarin zubo mata, Babu zato taji wani sabon yawu a fuskarta ya kara tofa mata a karo na biyu, baice komai ba ya shige mota Buba Direba ya shiga ya kunna mota suka bace daga gurin. Maddibo kamar ya dora hannu aka domin takaici da Sarki! ya kunsa masa, ya dauko shi domin yazo ya gyara masa lamarinsa gurin Balaraba, yazo ya bata daya goma bata gyaru ba,yanzu yaya zaiyi? Cikin muguwar kunya gami da jin nauyi ya kalli Balaraba tana goge hawayen bak'in ciki,tana sane ta matse kukan batayi a gabansa ba,sabuda kar yaga gazawar ta, sai bayan ya tafi hawaye ya balle mata,kamar me tunda take a duniya babu mahalukin da ya taba yi mata tozarci irin na yau,dole ne ma sai ta rama wulakanci da mutumin nan yayi mata. "Kiyi hakuri dan girman Allah,Balaraba, hakan ba halinshi bane, dana san abunda zai faru a tsakanin ku da ban gayyato shi ba,dama da yaya ya yarda zaizo din,kiyi hakuri dole zan dauki mataki akan haka,sabuda ke kanki kiba da daraja da mukami cikin zuciyata" Fuskarta goge da hannuwanta duk biyun,fuskarta a hade tace" Ya kuke dashi,ma'ana menene alakar ka da gidan Sarki"? Tsayuwa ya gyara sosai yana fuskantar ta, yace"Ni Sunana Yusuf kamar yadda kika sani, amma Mutan gida na kirana da Maddibo asali sunan kakanmu a gare ni shiyasa suke kirana da haka, Sarki Almustaph Wan mahaifina ne, Waziru Zayyanu" Da sauri Balaraba ta dago kai tana kallonsa cikin mamaki! Ya cigaba da cewa"Sarki! Almansor dan Uwana ne na jini kuma aminina abokina tare mukai karatu dashi tare muke rufewa mu kashe, amma halin kowan daga cikinmu daban yake da na dan uwansa, yana da saukin kai sosai in ka fuskance ki, amma bashi da hakuri ko kadan in ka tabashi, Mugun muskiline,sosai shiyasa nayi mamakin abunda ya hadaku haka kuke fadawa junanku bak'aken maganganu, da alama s kwai abunda ya taba hadaku a baya" Shiru tayi na minti biyu ta kalleshi a nutse tace"kana kallonshi yayi min wulakanci har da tofa min miyau bakace komai ba, dama ka dauko shine domin yazo ya wulakantani ko, babu komai, Nagode" Tana gama fadar maganarta ta kama hanya ta barshi tsaye a gurin,tafiya take kamar zata kifa jin zuciyarta take kamar zata kone sabuda tsabar turiri da take mata, da kyar ta kai kanta gidansu, Maddibo ko binta da kallo yayi har ta bace masa, jikinsa a sanyaye ya futo da waya ya kira daya daga cikin Direbobin cikin gidan Maimartaba Sarki Almustaph ya fada masa unguwar da yake,yace yazo yanzu-yanzu ya dauke shi Yana nan a tsaye a gurin, Sallau Direba ya karaso gurin Lokacin goma da rabi na dare,da sauri ya bude motar ya fito ya budewa Maddibo ya shiga suka bar unguwar, Salihu Yana tukin mota yana mamakin me ya kawo Maddibo irin wannan unguwar, ya gaza hakuri ya yace"ranka

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108