Chapter 22
Chapter 22
tana da karzuwa ko karuwa ko kuma me zaman kanta,yarinya nutsatstsiya kamila, maitarbiya, sana'ar siyar da abinci da takeyi domin rufin asirin kanta ne sabuda na lura iyayenta basu wasu masu karfi bane, amma bari kaji duk izzar ka da takamar ka wannan yarinyar tafi ka, sabuda haka in kanaso mu shirya da kai kar ka kara ai bata min ita,sabuda zuciya ba zata iya jurewa ba" Dariya Sarki!ya kama yi masa ba yana nunashi da hannu yace"amma ka bani kunya wallahi,yanzu a kan "yar towo-towo kake wannan tada jijiyar wuyar"? Shareshi Maddibo yayi. Har yanzu da murmushi a fuskarsa yayi gyaran murya gami da kara gyara kwanciya cikin ginshera yace" zanso in ga wannan yarinyar, da dai ban yi niyyar zuwa ba amma ganin yadda ka hakikance a kanta yasa dole zanje na ganta,yanzu yaushe ka shirya tafiyar" Sakin fuska yayi ya juyo yana kallon Sa yace"ai a inda ke sakar kwata-kwata yarinyar taki amince min zuwa gidansu, yanzu ma da kyar na karbi numbar wayarta wallahi, amma dole insa a buncika min gidansu" Shiru Sarki!yayi yana nazarin maganarsa ji yake tamkar ya tsinka masa mari,sabuda yadda ya bashi haushi,gashi bashi da halin magana yanzu zai hayayyako masa da masifa ya lura abokin nasa ya yi nisa sosai kan son yarinyar,sai kawai ya masa shiru yana ji yana magana bai tan ka ba. "Kayi min shiru ina ta magana ni kadai" "Me kakeso in ce maka yanzu" yafada hankalinshi a kan wayarshi, ya cigaba da cewa "kace yarinyar taki baka dama kaga kenan bata son ka sabuda haka sai ka hakura kawai,domim wahalar da kanka zakayi gurin macan da bata son ka" Shiru Maddibo yayi yana jin tsoran fada masa maganar dake bakinsa,da kyar dai ya samu yace"abinda zamuyi kawai muje can gurin inda take sana'ar tata, kafin musamu gidan nasu" "Wannan ne kuma baza ayi dani ba,kome zakayi sai dai kayi,in ka damu ka sa a duba maka gidan iyayenta,ni kuma nayi maka alkwari zan maka jagora insha'Allah" ya karashe maganar batare da ya kalle shi ba "Ai kuwa dole gobe na me adress dinta ko ta halin kaka ne" Tabe baki yayi yace" yace mubar maganar haka, muyi wata wallahi raina baci yakeyi dan dai babu yadda zanyi da kai ne" Dole tasa Maddibo barin maganar badan zuciyarsa naso ba suka shiga wata hirar daban. Can wayar Sarki! ta yi kara,a nutse ya duba fuskar wayar,Halisa ce dauke kansa yayi daga kan wayar har ta katse, wani kiran yakara shigowa a karo na biyu,nan ma ta katse bai dauka ba, Maddibo yace"matsala ta da kai kenan sai ai ta kiranka a waya dan tsabar wulakaci kaki dagawa" A ya mutse yace"kasan ko wacece ne"? "Sai kafada" "Wannan shashashar yarinyar ce Halisa" Dariya Maddibo yasa yace"wai kai har yanzu baka sallama mata bane"? "Tsaki! yaja cikin damuwa yace" Zaman da ka ganni inayi gurin Ummi zancan take maimaita min wai dole sai na aureta,babu yadda na iya dole in yi musu biyyaya amma kai kanka kasan yarinyar bata burgeni sabuda dabi'unta duk babu masu kyau" "Addu'a zakayi kasan dole ne muyi wa iyayenmu biyayya kan dukkanin abun da zasu zo mana dashi mutukar bai sabawa shari'a ba , amma ina ganin zaka iya da ita duk taurin kanta,tunda na lura ta sonka da yaw........Kafin Maddibo ya rufe bakinshi daya daga cikin, bayin dake tsaye bakin kofar shiga falon yayi sallama,ya zube nan bakin kofa kai a kasa yace" ranka shidade Gimbiya Halisa ce tazo da jamar'arta" Shiru yayi kawai yana latse-latse a waya Maddibo yace"je ka shigo dasu" Da sauri ya mike gami da cewa"angama ranka shidade, Allah ya taimeka ,yanzu zan cika umarninka" ya fuce da sauri! Maddibo ya kalleshi a fakaice ya na kunshe dariya yace"kaga mutuniyar taka ko muna zan canta sai gata tazo,gashi bakace komai ba" Uffan! bai ce ba masa ba har Gimbiya Halisa suka shigo ita da masu take mata baya. *MUJE ZUWA* [29/06, 05:20] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» ββββββ _*GIMBIYA BALARABA*_ ββββββ πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» _*Na*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani Writes Associationπ€π» ```Bisimillahir rahamanir rahim``` *π Ώ34* Cikin kasaita ta shigo falon kai tsaye in da yake zaune ta nufa,tana wata irin tafiya cike da izza da takama. Nan jama'arta suka zube bakin kofa suna kwasar gaisuwa,daga bisani suka fuce daya bayan daya, Wani irin zama tayi kan kujerar tamkar zata shige jikinshi tace"Yayana ya kake? kwana biyu duk kasa hankalina ya tashi in na kira wayarka sai kaki amsa min, kasan ko yadda na damu da kai kuwa" Fuskarshi a hade yace"ki matsa daga kusa dani mutukar kina so in saurare ki da abunda kikq zo dashi,kin san bana son wannan dabi'ar taki yana daya daga cikin abunda yasa sam ba kya burgeni" Jikinta a sanyaye tace"wai me yasa kake fadamin duk maganar da tazo bakinka,yanzu me ye laifin wanda yace yana sonka,kasan fa ban rasa masoya ba" Wani irin kallo yayi mata mai kama da harara cikin kasaita yace"ni ina ruwana da wasu masoyan ki kin san kina da masoyan zaki makale dole kice sai ni zaki aura,kije ki zabi daya daga cikin masoyan naki ki aura zai fi miki alkairi" Shiru tayi na minti biyu tana tunani tasan halinshi mugun dan wulakanci ne da girman kai,ya zama dole ta lallabashi tunda dai ita ke nema dole ta kwantar da kai har Allah yasa burinta ya cika. Kwantar da murya tayi tace"kayi hakuri insha Allah zan gyara,ni dai burina kawai ka dinga kulani kana daga waya ta idan na kira" Shareta yayi ya cigaba da duba wayarsa. Maddibo ta kalla tace"Ya Maddibo ka sanya baki mana wallahi ina jin tsoran wulakancin abokinka kullum da irin kalar da zai min gashi zuciya ta takasa hakura dashi." Cikin dariya Maddibo yace"kar ki damu insha'Allah komai zai wuce,amma dole kiyi hakuri da halinshi domin ba ke kadai yake wa,so tun yanzu ya kamata ki gane wane irin namiji zaki aura" Ajiyar ta sauke tace"bakaji yadda nakeji a cikin zuciya ta ba amma babu komai" Cikin dariya gami da barkwanci Maddibo ya kalli abokin nasa yace"mutumina kana ji fa ya kamata ka aje wayar nan ku fuskanci juna da mutuniyar kafin zuwan lokacin" Hankalinshi na kan wayar yace"ba kaji abunda tace min ba yanzu,wai tana da masoya,kajifa wani zance dan Allah, tasan tana da masoya me yasa ta nace min, "yar rainin hankali kawai" "Ni dai nace kayi hakuri" Halisa tafada muryar ta kasa kasa A ya mutse yace"in ban hakura dake ba yaya zanyi,ai dole ki kuyi iya magana,domin ni bana son shirme" "to zan koya in sha Allah" Nan dai ta lallabashi ya hakura suka cigaba da hira sama-sama, Maddibo yace"to ni zan wuce sai munyi magana a waya kafin gobe,insha Allah zan sa a duba min" "Allah ya kaimu" abinda yace kenan,Halisa tace"Ka gaida gida Maddibo a gaida su Mama" Sosai Halisa ta dinga jansa da hira, wani ya amsa wani ya share ta,to inda sabo ta saba da haka,cikin zuciyarta tace a juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe,yanzu ni burina kawai in ga na mallaka duk wulakancin ka zan jure **** Maddibo da ne ga wazirin Sarki,inda Waziri ya kasance kani ga Maimarta ba Sarki Almustapah,Uwarsu daya ubansu daya, Waziri yana da "yaya goma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108