Chapter 74
Chapter 74
ne da zaku dame ni da in tashi in ci abunci, ita tazo ke kinzo to me kuke nufi ne"? Halisa tana jin tsoran masifarsa tace"Umarnin Mama ne" Hararata yayi yace" Ko dai umarnin ki, nasan dai "yar aike ta farko da izinin Mama ta shigo, ke nasan neman maganar ki, dan haka ki tashi ki bani guri in inajin yunwa ai baku san sanda zan nemi abuncin ba" Halisa ta bud'e baki zatayi magana kenan Azima ta shigo d'akin. https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ ____________________ *Attention*⚠⚠ ______________________ _Akwai masu kirana a waya suyi min zancan banza, kusani baku kuka aje ni ba,,,, ban san wulak'anci ba,saboda ba halina bane,cikin Ku masoya babu wanda na ware nace dashi nake,mutukar kika turo min sak'o kikaga ban baki amsa ba,to ki min uzuri, kar ki bini ta pravite ki gayamun magana littafin gimbiya balaraba dai nawa ne, mallakina ne,nake rubuta muku da basirar da Allah ya hore min,ina fatan Allah yasa sak'ona ya isa, Hak'ika abunda wata baiwar Allah taimin ya bani haushi wallahi, ta sanadin haka ma na janye typing kwana biyu, saboda haka duk wacce tasan ba maganar arzik'i zatai min ba,to kar ta kirani a waya, idan Gimbiya balaraba take so ta nema a groups,wannan shine magana_ _________________________ _Nagode muku masu bina domin jin abunda ya dakatar dani kwana biyu Hak'ika kun cika masoya na na hak'ika, ina mugun sonku iya wuya ana tare_🥰 _Ku k'ara yawan comments ku ga redemore goma idan kunk'iyi na tafi hutu, wannan shine magana☺_________________________ ______________________ *Husaini Atk 80k* ______________________ _Allah shine abun godiya ina taya d'an uwanmu Husaini Atk 80k murna da samun nasara daga abokan adawa,ina fatan Allah ya k'ara muku nasara a rayuwarku_ *🅿86* Azima na shigowa Halisa ta sha kunu, kallon banza tayi mata tana hararata k'asa-k'asa tsaki taja tayi saurin zama kusa dashi har jikinsu na had'uwa. Azima ta k'araso kusa dashi cikin nata salon tace"Allah ya taimake ka, tuntuni nake so in samu mu zauna dakai Allah bai nufa ba, yau sati na biyu a gidan nan, ban keb'e dakai ba, tun mutuwar Moddibo komai ya hautsi ne,Allah me yadda yaso a sanda yaso,gashi ya d'auke mana ubanmu maganin kukanmu, ina mik'a ta'aziyata a gurin ka bisa rashin da mukayi gaba d'ayanmu" Azima ta k'arashe maganar tata tana sharar hawaye. Wannan kalamai da Azima tayi sun k'ara mata martaba a idonsa, tabbas tanan Azima tafi Halisa hankali da sanin ya kamata shi a ganinsa, don haka sai ya maida hankalinsa kanta yana amsa mata maganar ta, cikin sakin jiki, yace ta zauna a d'aya gefan nasa. Azima ta samu guri ta zauna tana k'ara lauya muryarta duk dan tayi dad'i ganin wacce tayi amfani da ita d'azu tayi tasiri a gurinsa. Tace" Wallahi mutuwar me Martaba bakai kad'ai akai wa ba,har damu domin munyi rashin suruki nagari,hakik'a har abada baza mu daina yi masa addu'a ba" Sarki! Gyad'a kai kawai idanunsa a lumshe suke yana jin duk irin rarrashin da Azima take masa,dama abunda yake buk'ata kenan,zuciyarsa ce ta fara yin sanyi, ya bud'e idonsa duka ya sauke su kanta, muryarshi k'asa-k'asa yace"Je ki d'auko min abunci naci" Azima ta mik'e jiki na kyarma, ta girgiza jiki da gayya ta gallawa Halisa harara ganin ta samu nasara, abincin ta d'auko cikin wani irin fulas mai uban kyau da k'yalk'ali. A fusace Halisa ta mik'e saura kad'an ta fad'i tana kumbure-kumbure ta futa daga d'akin. Kallo d'aya yayi mata ya kauda kansa. Azima ta had'a masa abuncin ta zauna kusa dashi yana ci tanai masa hira mai dad'i sai gashi yaci da yawa babu laifi. Da kanta ta zuba masa ruwa ya wanke hannusa cikin wani abu mai kyau, ta yago masa abun goge baki ya goge bakinsa,ya mik'e ya koma kan gadon ya zauna yana kallon ta,har ta gyara gurin tazo ta tsaya kusa dashi,cikin nata sallon tace"To zanje in kwanta Allah ya taimaka ka,Don Allah kayi bacci karkayi tunani kaji ko" Kallonta yayi na minti biyu yace"Karki damu, kije ki kwanta Allah ya bamu alkairi" Azima ta juya da niyar futa daga d'akin, tana wata irin tafiya domin ta d'auke masa hankali Allah Sarki! Azima ai bai san ma tanayi ba,domin tana juyawa ya kwanta kan gadon rigingine ya lumshe idonsa,,,D'an juyowa tayi a sace taga ko yana kallonta,ganinsa tayi a kwance da ido a rufe, bud'e k'ofar tayi ta futa jiki a sanyaye, ta wani gefan kuma murna take k'untatawa Halisa ita da Mahaifiyarta Madabo,, sauranta Balaraba, Azima na futowa falo ta ga su Halisa da mahaifiyarta a zaune suna magana k'asa-k'asa, d'auke kanta tayi ta shiga wani d'aki harda bugo k'ofa. Mama Fulani da Balaraba dama tuntuni sun bar falon. Madabo ce tak'i tafiya wai Lallai sai taga futuwar "yarta Halisa. K'wafa! Madabo tayi tace" Zanyi maganin ki ne yarinyar banza kawai tana fama rama sai kace jemage babu k'irjin arzik'i, ai da ni wata me fad'a aji ce a wannan gida,dana hana auran nan wallahi" Halisa tace" Don. Allah Mamana kiyi masa magana gobe ya hanye maganar auran,ko da ya kuntatawa Baba Waziri , kamar yadda ya k'untatawa mahaifinsa" Madabo tace"Rabu dashi gobe idan Allah ya kaimu zan masa magana ai yana jin magana ta" Halisa tace"Allah yasa ya d'auki maganar taki Mamana" Madabo tace"Ameen ke dai" A ranar Azima kwanan farin ciki tayi yayin da Halisa ta kwana bak'in cikin abunda Azima tayi mata. Bacci mai cike da rud'ani da mafarkai shi Balaraba tayi a ranar, Asubar fari,ta farka jikinta.yayi sharkar da gumi tamkar babu Ac a d'akin,wani irin nauyi kanta yayi mata, ta dad'e kan gadon tana sak'awa da kwance wa,wani irin mafarki tayi mai tsananin rud'u da tashin hankali,abun mamaki kuma so take ta tuno ko menene takasa tunowa gashi dai tasan tayi, k'arfin addu'a ne ya tada ita tsaye, toilet ta nufa domin yin wanka da alwala . Bayan idar da sallahr Asubah ne. Suna k'okarin futowa daga masallacin wani bawa ya k'araso gurin da sauri, ya zube gaban Sarki! Muryarshi na sark'ewa yace"Ranka ya dad'e babu lafiya shashen Uwar gida Hajiya Kulu, yanzu-yanzu Naja'atu da Fiddausi suka fad'i kwata-kwata sun daina numfashi sai wani abu dake futa daga bakinsu" Hankali a tashe Waziri da Galadima suka nufi shashen Kulu. Shi kuwa Sarki! Abun ne ya fara bashi mamaki, da kuzari a jikinsa shima ya nufi shashan,sauran mutanen dake gurin suka rufa masa baya,, Yanayin yadda yake tafiya cike da jamurta yasa har yazo ya Tatar dasu,bai saurare su ba,ya kutsa kai cikin falon.. Fiddausi da Naja'atu ne kwance a k'asan tayal sun mik'e samb'al basa nuffashi, Kulu ta tasasu agaba tanata kwarma ihu! Kamar gaske. https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿87* Jakadiya Ladi ce ta k'araso gurin hannuta d'auke robar ruwa me sanyin gaske, bud'ewa tayi zata zuba musu, Galadima ya buga mata tsawa yana fad'in "Kar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108