Chapter 5
Chapter 5
Balaraba tace taci gaba dacewa Kawu Naji kayiwa babanmu Addu'a banda Mamana" Bata Fuska Kawu yayi yace "Allah yajikanta itama daga haka yaja bakinshi yayi shiru ita tarasa wace irin qiyyaya Kawu yakewa Mama ta duk da bata raye. Yace"ae sai mutafi ko gaskiya naji Farin ciki sosai Balaraba zakije Makka Aikin Hajji mu Na zaune, Dariya tayi tace "Kawu kenan kar kadamu Nabar maka kaje kai kawai Tafada babu damuwa tattare da'ita. Wani farin ciki ne ya ziyarce shi A zucci yace "ja'ira mai kama da tsohowar Karuwa ae ko baki bani ba baki isa kije Makka ba in dai INA raye a doran duniyar nan. A zahiri kuwa yariqa washe baki tamkar me sai shi mata Albarka yake kamar babu gobe. Jin shi kawai Balaraba takeyi domin tafi kowa sanin waye Kawu. Haka suka ran kaya suka nufi gida Kawu sai hirarraki yake mata Na babu gyara babu dalili. Wani gida Nafara hangowa cikin wani surqoqin lungu Wanda kwatoci sukayi wa yawa gasunan duk sun bi hanya babu kyawun gani gefe ga tarin bola da tarkace da wata tsiya ce yara duk sun Tara kayan gwangwan da Alama yaran Layin suna fita Sana'ar gwangwan domin ga Alamu nan tarin robobin qarafuna da buhunhuna. Haka sukai ta tsallake shirgin gurin Kafin su shiga cikin gidan da babu kofar arziqi duk ta lauye ko tsayuwa batayi da kafarta sai an kare da dotse ko kujera,Kawu sai zage zage take yi kafin ya shiga gidan fadi yake shegu tsinannu "yayan Allah bani duk sun zo sun cika mana layi da kayan sata "yan iskan yara kawai" Wani kallo Balaraba taiwa Kawun Mai kama da Harara tace"Haba Kawu wannan zage zagen bashi da Amfani Shiyasa suka rai naka ina ruwanka dasu ,sai La'antarsu kake yi ta'ina zasuyi Albarka kar ka Manta fa harda su Babaye da Walidi cikinsu shikkenan tunda ka hadasu ka zage babu ta yadda zasuyi Albarka ,Neman halak dinsu sukeyi yafi suje su dauki Na wani " ta qarashe maganar Cikin bacin rai! Gyaran Murya yayi ko kunya babu domin shi yanzu lallaba Balaraban yakeyi so yake ya kwace mata duk Abinda ta samu gurin saukar. Yace"Rabu dasu diyar Albarka kinji ko shige muje ciki Ae ke kaman Dan Uwana yayi sa'ar Haihuwa ba wa"yannan "yan iskan ba" Yaran dake gurin suka kwashe da dariya suna nunashi da hannu domin dai dama yaran duk sun rai nashi sakamakon zubar da Mutunchin shi da yakeyi gurin in sunje gwangwan dinsu sun dawo yabi yana kar6e musu kudi. Balaraba taja tsaki ta shige ta barshi gurin tace"ae kaga Abinda nake gudar maka nan gashinan sun mai da kai mahaukaci" Walidi ne yafito a guje su ka ci karo da Balaraba yayi mata wata bangaza tamkar zai yadda ita kasa,yayi gaba ko saurararta bai yi ba. Da sauri ta jawo hannunsa ta zabga Masa Marika hagu da dama tace" Dan Uwarka ni sa'arka ce zaka bangaje ni ka huce ko kallo ban isheka ba ko ka ga INA shiga sabgarku ne"? Kuka Walidi yafashe dashi yayi cikin gida da gudu yana cewa"Allah ya isa ban yafe ba Shegiya "yar Karuwa" Wani Bacin rai! Ya dirar wa Balaraba tayi cikin gidan A fusace yau sai taga da Wanda walidi yake taqama Lallai yau za'ayi rigima gidan nan domin tagaji da irin cin zarafin da yaran suke mata. Da sauri Kawu yabi bayansu yana zagin Walidi ta Uwa ta Uwa ba Uwa" Na zaune kan kujera "yar tsuguno tana wanki dake sana'ar tace kenan wankau Walidi ya shigo yana burara ihu tamkar Wanda a ka yanka ,Sai tambayarsa take menene da qyar yace waccan "yar karuwar ce ra mareni hagu da dama inaji ma ido na yafashe yafada tana rintse ido daya cikin sharri Cikin Sababi! Da tashin Hankali! Uwa ta Mike tana gyara daurin zaninta tace "Lallai Yau zaci kambu a gidan nan Wallahi tallahi bazan lamunci wata "yar iska ta riqa dakar Min "yaya ba bara ta shigo inji meye dalil......kafin ta karasa tajiyo Muryar Kawu yana ta Surfawa Walidi zagi! Abin Mamaki! *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* πππππ [04/05, 02:52] +234 808 996 5176: π§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββ *πΎGIMBIYA BALARABA*πΎ π§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββ *βπ»writting by* *Binta Umar* _*MAMAN ABUDL WAHABU*_ *MRS AHAMAD GWADABE* _*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_ *π Ώ8* "Yau kuma da Abinda kashigo da shi kenan Malam me walidi yayi maka kake ta surfa masa zagi haka? Kar dai a ce tarewa mutsiyaciyar yarinyar nan kake Balaraba" Tafada tana nuna Balaraba dake jikin rijiya tana kallonta. Kawu ya gyara tsayuwa gami da riqe Abubuwan dake hannunsa da kyau ,ya kalli "Uwa yace"Laifi ne Dan Na tare mata Yarinyar kirki haka ka wai kin bata yaranki kin sangar tasu basa ganin kowa da mutumchi a gidan nan yanzu a ce kamar Balaraba ita Walidi zai zage yayi ta zagi kina kallonshi kice in yi shiru" Mugun Mamaki ne ya kama Uwa jin Abinda Kawu yake fada Lallai a kwai lauje cikin nadi kawun da yake zama a zagi Balaraba da ita da iyayenta da qannenta yau shine yake tare mata fada. Ta gyara tsayuwa gami da gyara daurin dankwalinta ta kalli kawun tace Au! Ashe kai ma tafara baka cin hanci cewa zakayi kafara cin kudin zina da sata Tafada tana wani girgiza jiki cike da Neman fitina, Kifta mata ido Kawu yayi ganin har ta hasala Duk Balaraba Na kallonshi. Aiko dake "Uwa tasan Halin Mijinta nan da nan ta dago Abinda yake nufi kifta mata idon da yayi [04/05, 02:54] +234 808 996 5176: π§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββ *πΎGIMBIYA BALARABA*πΎ π§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββπ§ββ *βπ»writting By* *Binta Umar* _*MAMAN ABDUL WAHABU*_ *π Ώ9* "Ke kuwa Uwa wane irin Abu mai muni yarinyar nan tayi miki ? Kike jifan ta da Mummunan Al'kaba'i haka me yayi zafi kema fa kin haifa" Iya take fada bayan fitowarta daga dakin ta tana tsaye ruqe da ha6a tana kallon Uwa cikin Mamaki Kafin Uwa tace komai sai gasu Mabaruka sun shigo a guje ko wanne hannushi ruqe da Farin botiki Wanda suke zuba Awarar da suke Siyarwa da kwai suna kaiwa kasuwanni Sai wasan banza suke suna dariya kamar wasu shashashai ko wacce taci janbaki gami da wani katon A cuci a kawunansu. Sai suka tsaya ganin Iyayen nasu a tsaye dagani Fada a keyi. Uwa tace "Yawwa "yayan Albarka dama tunda naji shiru nace Lallai yau Awara zata qare Allah dai yayi muku Albarka Ya Baku miji nagari duk Dan bakinciki sai ya mutu ehe!! Tafada tana kallon gefan da Iya ke tsaye tana kallonsu, Shamsiyya tace"wai meye ne ? Naga duk kunyi wani cirko cirko tafada tanawa Balaraba Wani Dan iskan kallo. Uwa tace"Wannan mai ido a tsakar kan ce take zagina bay an ta mari Walidi shine babanku yake cewa wai laifin walidi ne kan nayi mata magana Shine yar Ubanta tafito zata tare mata . Tafada gami da zama kan kujerar da tatashi ta ciga da wankinta tana sakin habaici ga Iya. Mabaruka ta kalli Kawu sallau Mahaifinsu ,Cikin Raini da rashin kunya tace "Haba Kawu yanzu har ka fi son bare da Jininka yanzu a gabanka wannan jakar! Take zagin Maihafiyarmu baka ce komai iyi!? Kawai sai ta aje botikin Awarar a Fusace tayi kan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108