Chapter 94
Chapter 94
_*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿105* Yara suka fara taruwa a kanta sai kurma ihu! Take, da sauri wannan matar ta d'ora ta a hanyar gida tana tafe tana kuka kamar shashasha sai surutai take. ********************** Mota a ka kawo su har k'ofar gida cike da kayan arziki, yaran unguwa suka yi dafifi suna shafa motar suna tsalle har yanzu sun kasa sabawa. Yara matasa suka kwashe kayan da suka zo dashi suna shiga gadan dasu,, suka bi bayan su duk jikinsu a sanyaye,, Buba direba yaja motar sa ya tafiyar sa,, suna k'okarin shiga gidan ana k'okarin futo da Sallau a rirrike jikinsa yayi tsanani, Lantana ta rafka salati gami da fashewa da kuka tana fad'in "Ina zaku kai shi"? Walidi Yace" Asibiti za a kaishi domin jikinsa yayi tsanani, nan ta bisu a baya tana kuka, Uwa! Kuwa gida ta shige tana matsar hawaye, Sadiya da Iya na tsaye tsakar gida cike da tausayin Sallau Uwa ta shigo gidan, kallo suka bita dashi ganin tana matsar hawaye domin sun d'auka ko ganin jikin Sallau ya rikice yasa ta kuka, zauna tayi a tsakar gidan tana kukan nadama. Ko minti goma ba'ayi ba sai ga Shamsiyya ta shigo gidan tana kurma ihu, ta zube gaban mahaifiyar ta tana fad'in"Shikkenan Uwa! Aiki ya lalace "yan sanda sun kama Arrama jiya da yamma" "Don Allah ni yi min shiru da zancan wani Arrama in zaki hak'ura ki hak'ura ki zauna inda Allah ya aje ki, ni kam. na dawo daga rakiyar wannan duniyar me cike da rud'u" Uwa! Ta fada tana sharb'e hawaye Shamsiyya ta d'ago kai tana kallonta cikin mamaki tace"Ban gane abunda kike nifi ba kina nufin in rabu da maganar aure na da Sarki! Ko me"? "E abunda nake nufi kenan, Domin babu yadda za'ayi ya aure ki yana da Balaraba" Shamsiyya ta fashe da kuka tana fad'in "Uwa kar muyi haka dake kinji, kece fa kika yi mana alk'wari cewa ko da zakiyi yawo tsirara sai in da k'arfin ki ya k'are zaki tsaya min gurin ganin buk'ata ta ta biya" "Ke ni ki k'yaleni don Allah inji da masifar da nake ciki, ubanki ya sake ni saki uku, ga masifar Ku ta same ni, Nazo a banza zan koma a wofi ni yanzu waye zai aure ni" ta k'arashe maganar tana rusa ihu! Shamsiyya ta dafa kirji tana fad'in "Baban bamu ne ya sake ni yau she haka ta faru"? Nan Uwa ta kwashe duk abunda ya faru ta fada mata har da zuwan su gidan Sarki! Shamsiyya ta kwanta tana rusa ihu! Babu kamar wacce uwarta ta mutu *********************** Suna zaune gaban Mama Fulani duk su ukun sai shi da ya zama cikon na hud'un,, yana hakimce kan kujera. Mama tace "Salati goma da Annabi" Duk suka amsa da "Sallalahu alaihi wasalam"Minti goma tsakani tayi addu'a ta shafa suka shafa suma,, ta kalli Sarki a nutse tace" Babban abunda yasa na tara ku anan shine, in ja muku kunne gami da nasiha, mussaman kai" tafad'a tana nuna shi da hannu, kansa ya sunkuyar kasa, ta cigaba da cewa"Allah ya d'ora maka wani babban nauyi a kanka na mataye har uku, dukaninsu suna da hakki a kanka babu wacce tafi kowa a gurin ka sai wacce tafi kyautata maka a cikinsu, don haka ina mai gargadin ka da ka rike amanar su ka bawa ko wacce hakkin su,da ya rataya a kan ka" Yace"Insha Allah Mamana kar ki damu" "Ku kuma na dawo kanku" Tafad'a tana kallonsu duk su ukun, ta cigaba da cewa"Ku yi kokari Ku kula da mijin Ku Ku fahimci me yake so da Wanda ba ya so, yi nayi bari na bari Ku yi k'okarin zama lafiya da juna domin Ku kwantar masa da hankali gurin ganin ya rik'e amanar Ku, da jagorancin mutanan gari da ya hau kansa, ni Wannan kawai zakuyi min Ku faranta min, insha Allahu , kuma idan wani sab'ani ya shiga tsakanin ku dashi, ba fata nake ba,, zama ya gaji haka zo mu zauna zo mu sab'a haka duniyar take, to sai Ku same ni Ku sanar dani insha Allahu komai zai zo da sauk'i" "Mama Insha Allahu zaki same mu masu zaman lafiya da juna" Balaraba tafad'a kanta a kasa,, Azima da Halisa ma Abunda suka ce kenan, Mama tace"Masha Allahu Allah yayi muku albarka" Ameen suka ce gaba d'ayan su. ************************ K'arfe shida na yamma, gurin Walima ya d'auki harami ya tsaru ya k'yayatu sosai Shahid da Shatima ne suke ta kai kawo a gurin suna saukar abokan su, da suka fara zuwa. Suna sanye da wata arniyar gezna wacce ta amsa sunanta anyi musu dinki iri daya hula da takalmi duk kalar shaddar ne,, ruwan toka kenan sai shek'i take aikin ya. zauna a jikinta. Suna zaune a falonsa ko wacce kujerar ta daban da "yar uwarta babu wacce tayiwa " yar uwarta magana, suna sanye da kaya iri d'aya Shadda ce, sky blue anyi musu d'in ki Aliya taji sirfani duk gaban rigar ko wacce ta d'ora d'auri dai-dai da kwalliyar ta, gwal kuwa kamar yayi magana hannayen su da wuyan su, takalman su iri daya ne, Azima da Halisa sun sha kwaliyyar fuska, babu Mayafi a jikinsu, Balaraba kuwa babu laifi fuskarta babu komai sai farar hoda da kwalli da ta zizara a idonta, bayan haka ko man leb'e bata sa, amma haka bai hana bayyanuwar kyanta ba, ta yafa k'aramin mayafi Wanda ya sauko ya rufe mata k'irji. A hankali yake sakko wa yayin da k'amshin tura ransa ya cika gurin , dukanin su suka mai da su kansa,, Kallo guda tayi masa ta d'auke kanta gabanta na fad'uwa. Yana sanye da shadda irin jikin su Sak,, anyi masa dinki irin na zamani,, me falmaran wacce yaji sirfani me tambarin sarautar su,gaba da baya hular shi ma da yanki shaddar aka had'a ta,, kafar shi sanye da wani ruffan takalmi mai gashi-gashi sky blue hannunsa daure da agogo na zallahar azurfa, ya tsunsa ma zobuna ne manya-manya masu d'auke da tambarin sarautar su. Cikin nutsuwa ya k'araso gurin su,, Fuska babu yabo babu fallasa yace"Ku tashi muje" a nutse ta mike jin abunda yace, gaba yayi suna bin shi a baya,, sai ga Shahid da sauri ya tare shi tare da wasu fadawa su uku suna take masa baya, Shatima yace"Kuyi tafiyar ku kawai,, suka ce "An gama ranka ya Dade, magana yake masa k'asa-k'asa, tsayawa yayi yana d'an hararsa, shi kuma ya sa dariya, yace" Hakane mana sai kayi gaba ka bar amaran naka a baya kai fa d'an gata ne" banza tayi masa yana d'auke kai da alama yau "yan muskilancin nasa na kusa,, Shatima ya k'araso tare da su Balaraba dole suka tilas tashi ya shiga tsakiyar su,, suna tafiya su uma suna take musu baya. Tunda futowar su har zaman su a masu hotona da vidio suke aikin su, marok'a duk sun cika gurin da roko, sosai gurin ya cika ya tumbatsa da mutane kowa sai farin ciki yake, ciki kuwa babu " yayan Waziri Zayyanu ko guda. D'aya suna can bakin ciki kamar ya kashe su, jin cewar har governor sai da ya hallarci gurin. Walima tayi kyau sosai an raba kaya naci Dana sawa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108