Skip to content

Chapter 70

Chapter 70

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,263 words 0 views Progress saved
Download Book

Mama Fulani tayi musu shiru kawai tana kallonsu da murmushi a fuskarta,taji dad'in sakin fuskar da Balaraba tayi. Yana kwance, cikin Sofa yayi lif kai baka ce a kwai mutum cikin d'akin ba,duk wannan abunda yake faruwa yana ji,tun futowar Balaraba, ya nemi nutsuwarsa ya rasa hatta baccin da ya rufe masa ido nemansa yayi ya rasa,ya lumshe ido kawai yana sauraron muryarta wacce ta kashe masa jiki, ashe haka yarinyar take da surutu,muryarta nada dad'i,abunda yake fad'a kenan cikin zuciyarsa. Mama Fulani ce kawai tasan yana gurin,domin da futo ta ganshi a kwance har tayi masa maganar tafiya shashensa yace"Sai ad'an jima zai tafi" Yanzu ma murya ta d'an daga kad'an tace"Magajin Sarki!" Da sauri Balaraba ta kalli inda Mama take kallo,gabanta na fad'uwa yanzu da yana gurin ta saki jiki take,dariya sai kace wata shashahsa, k'asa tayi da idonta lokacin da ta hangi inuwarsa kwance kan kujera, dake gurin da yake babu wadataccen haske,ya k'ashe k'wai shiyasa lokacin da ta futo bata ganshi ba, Jin muryar Mamansa yasa yayi gyaran murya,yana daga kwancen yace"Na'am Mamana" Cikin tausasawa tace"Yau da alama dai nan zaka kwana,ko"? Shiru na minti biyu,yace"Mama yau wani irin kad'aci nake ji wallahi,ki barni inyi kwanciyata nan,ina jin motsin ki" Murmushi tayi cike da tausayinsa tace"Yau yarinyar tar ce kuma ta motsa maka" Murmushi yayi wanda har sai da sukaji sautinsa,Balaraba taji wani yarrrrr! A jikinta. Yace"Dama ni kullum yaro ne,a gurin ki, tunda har yanzu banyi auran fari ba,kuma ban haihu ba" Shiru Mama tayi,kunya duk ta isheta Mama Fulani maca ce mai mutukar kunya a rayuwarta, Jakadiya Shafa'atu tayi murmushi tana k'okarin mik'ewa tsaye tace"Lallai Uban d'akina dole kasa Fulani tayi shiru,saboda ka tab'o abunda baza ta iya magana akai ba,saboda kunya, kana maganar auran fari,kai kasha kurumin ka, mata uku zaka aura me yafi wannan dad'i" Miskilin murmushi yayi iya leb'anshi yana satar kallon Balaraba shi yana ganin fuskarta sosai,itace takasa gano fuskarsa,sai dai zatinsa, Jakadiya ta runk'umfa tana fad'in A tashi lafiya Uwar d'akina" Mama tace"Allah ya bamu alkairi" Sarki!ta kalla kanta a k'asa tace"Yallab'ai a tashi lafiya" Hannu kawai ya d'aga mata,maganar tana masa wahala,dama zuwa-zuwa ce, in yaga dama wataran haka zai ta hira,mussaman da Moddibo ko Mamansa Balaraba ma mik'ewa tayi ,tai wa Mama sallama, Mama tace"Har zaki shiga Balaraba, ko dan kinga Jakadiya ta tashi" Girgiza kai tayi cikin jin nauyi tace"Ba haka bane Mama,ina so in d'an kwanta ne, naji kaina na ciwo kad'an watak'ila bacci ne" "Ayya, to ki tabbatar kin sha magani kafin ki kwanta kinji ko" Tafad'a cikin kulawa. Balaraba tace"Insha Allah Mama, Allah ya bamu alkairi" Mama tace"Ameeen Balaraba ta wuce d'akinta a nutse, Idansa a k'asa sai ka rantse da cewar bacci yake saboda yadda ya lumshe su, amma duk wani motsin Balaraba yana gani har ta shige d'aki. Ajiyar zuciya ya saki,yanayin jikinsa na sauyawa, ya rasa abunda yasa yake jin wani irin sauyi a jikinsa mutukar zai ga gilmawar ta,sai sha'awarsa ta motsa,yasan yanzu idan ba'ai wasa ba,kwana zaiyi yana mafarkai, shi kansa yasan mutum ne mai mutuk'ar Sha'awa, yana daurewa kawai,amma abun mamaki idan yana tare da Halisa baya shiga irin wannan yanayi Shi kad'ai a kabari a k'aton falon, domin Mama ma ta shiga ciki, rage haske futular yayi ya gyara kwanciyarsa,bacci ya d'aukeshi, mai cike da mafarkai, mafarkin da ya dad'e bai yi ba,yau yayi Balaraba ya gani, tare da wannan matar suna cikin farin ciki da annushuwa,suka zo gurinsa, kamar kullum, matar ta kama hannusa dana Balaraba ta had'a guri guda, ta tafi tana waiwayensu, fuskarta cike da farin ciki har suka daina ganinta. Balaraba ya kalla sai yaga tanai masa wani k'ayataccen murmushi, gashi ta rik'e hannunsa sosai, taja hankalinsa cikin mafarkin, wanda yayi sanadin da yakasa daurewa ya rungume ta sosai yana kiss d'inta, ji yake kamar gaske, jikinsa duk ya shiga babu abunda yake buk'ata lokacin sai Jima'i, sai da ya kai k'ololowa sannan ya farka cikin wani mugun yanayi jikinsa duk ya b'aci, still kamar yadda yake ganin girmansa cikin mafarkin haka take a fili, ta mik'e tsaye! Tana jiran hakkinta . https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿81* Ya dad'e yana jin wani irin yanayi a jikinsa, wanda bai tab'a jin irinsa ba, da k'yar ya samu ya mik'e a jigace, futa yayi daga shashen gaba d'aya, ya nufi nasa, lokacin ana kiraye-kirayen sallahr asubah, a gurguje yayi wanka gami da tsarkake jikinsa, ya futo ya zura jallabiya me yankakken hannu, wani takalmi mai kyau ya zura a k'afarsa ya futa, da nufin zuwa massalaci, domin gabatar da sallahr asubah. ******* Uwa! da Shamsiyya ne zaune gaban wani mutumi zaune a kan wani buzu, da wasu manya-manyan carbuna, gami da alluna irin na k'arfe a jijjigine a bango, yana sanye da riga da wando na wani yadi bulu, wanda akai wa d'inki "yar shara. Gabansa wani fefe ne k'aton gaske cike da yashi, yana zane-zane a ciki, shi kad'ai ya san abunda yake zanawa. Yana ganinsu ya saki fuskarsa, sannu da zuwa kawai yake musu. Suka nemi guri suka zauna suna gaisawa, amsawa yake, hankalinsa na kan Shamsiyya. Yashin, da yake gabansa ya hau zanawa, tsawon minti biyar, ya d'ago kansa yana kallonsu yace" Na duba naga abunda yake tafe daku, ina fatan dukanin abunda aka umarce ku dashi zakuyi batare da kun bamu wahala ba" Uwa! ta gyara zamanta sosai, tace"Allah ya gafarta maka, duk abunda aka umarce mu muyi zamu yi mutuk'ar buk'atarmu zata biya" "To Masha Allah" Arrama ya fad'a yana kallon Shamsiyya sai sid'e leb'e yake. Gayan murya yayi, yace"Naga wata yarinya buduwar wa,gata anan" Yafad'a yana nuna wani zane da yayi jikin yashin. Uwa! ta k'walalo ido tana son ganin budurwar da ya fad'a Murmushi yayi yace"Ai baza ki ganta ba, wannan aikinmu ne" Uwa! tayi yak'e tace" Allah ya taimake ka" Arrama ya cigaba da cewa "Wannan yarinyar da nagani, naganta kewaye da wasu taurari masu haske da d'aukaka, kuma na fahimci akanta kuka zo" Shamsiyya ta gyad'a kai tana fad'in "Hakane Arrama, Balaraba sunanta. Murmushi yayi, ya sid'i leb'ansa a karo na biyu yace" Itace Balaraba, gatanan cikin gidan sarauta, kewaye da dawakai da bayi, gatanan cikin shigar alfarma, kuma zata haifi "yaya maza sosai a gidan, ciki kuwa harda Sarki!" Arrama ya k'arasa maganarsa yana duba ya shin dake gabansa. Uwa! saura kad'an ta saki futsari saboda jin abunda Arrama yace, bakinta na rawa tace" Yanzu Allah ya taimake ka babu yadda za'ayi a rusa mata rayuwa,a sabauta mata rayuwa ta haukace, a maye gurbinta da Shamsiyya, gata a gabanka" Ta k'arasa magana tana nuna masa Shamsiyya Arrama, yayi wani bazawarin murmushi, yace"Akwai yadda za'ayi mana mutuk'ar zaku bi umarni kamar yadda na fad'a muku tun farkon zuwanku nan". Shamsiyya tace"Insha Allah zamu bi umarni" Arrama yace"To yanzu abunda za'ayi, ke zaki zauna a gurina tsawon kwana bakwai zan fara yi miki wankan magani, ke kuma" Yafad'a yana kallon Uwa! yace"Ke kuma zan had'a miki wasu magunguna da zakuje kuyi amfani dashi duk rintsi kar ku wuce kwana

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108