Chapter 19
Chapter 19
tuntu ja da adon zane irin na sarautar garin, yana sanye da wata shadda milk colaur mai mugun tsada,wacce a kai wa dinkin "yar shara da dogan wando gaba da baya na rigar surfani ne irin mai dauke da alamun gidan saurata, duk kayanshi na zaman gida haka suke dai-dai da jallabiyoyinshi,a kwai tambarin sarauta, wani kara min littafi ne na addini a hannunshi yana dubawa, ta cikin farin tabarau din dake idanshi, duk wanda san Sarki!Almansor ya kalleshi a yanzu ya san da akwai abinda yake damunshi,sabida walwalar shi ta ragu kuzarinshi ya ragu duk da cewa dama tun fil'azal shi ba mutum ne mai fara'a da dariya ba, kafin ka ga dariyarshi sai kayi da gaske, sannan kullum fuskarshi a tamke take tamau, to a " yan kwanakin nan abin yakara karuwa wanda har sai da Mahaifiyar shi ta fuskanta, lokacin da ta tsirashi da tambaya yace mata babu komai, sam bata yadda da abinda yace ba,tafi zaton ko maganar da tayi mishi ce a kwanaki, take damunshi, sabida haka, tasa Jakadiya Shafa'atu mai mata hidama taje can shashensa ta kira mata shi,tunda takira wayarshi yaqi ya dauka, tasan halinshi da muguwar bakar zuciya da muskilanci, ba ai masa komai ba ma sai ya tsiri share mutane ko yayi kwana da kwana ki bai kula kowa ba, yanzu ma haka tun shekaran jiya da sukaje daurin aure gwarzo shida su Waziri bai kara fitowa daga shashensa ba, shi kadai yake rayuwarshi shida hadiman sa, daya daga cikin wayoyinsa ne tayi kara, cikin ginshera gami da kasaita ya karbi wayar daga hannun daya daga cikin fadawan nan guda biyu,ya kalli scerin din wayar yana ya mutse fuskarshi, "Muddibo na! sunan da ya gani kenan yana yawo ka screen din wayar Wani murmushi ya saki wanda ya fito masa da kyawunsa da zatinsa,ganin sunan Abokinshi kuma dan Uwanshi amininshi, ba tare da bata lokaci ba ya daga wayar, cikin Yanayin muryarshi kasa-kasa yace"ya akai ne, ka shigo garin ne"? *YANZU MUKA FARA*βπ» [23/06, 13:45] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» ββββββ _*GIMBIYA BALARABA*_ ββββββ πΈπ»πΈπ»πΈπ»πΈπ» _*Na*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani Writes Associatio ```Bisimillahir rahamanir rahim``` *π Ώ31* ________Daga 6angaran Maddibo yace"yau kwana na biyu da dawowa, nakira wayoyinka jiya shekaran jiya da jiya duk a rufe, ko jiya nazo gaisuwa fada ban gan ka ba, shine Fulani tace kana gurin ka kwana biyu a kulle ka ki saurarar kowa, hakane ko"? Zakuda kafada yayi ranshi ya soma baci jin irin maganar da Maddibo ke masa sai kace wani ubansa,yace"Ubana ne kai da zaka turkeni kana tambaya,in kana bukatar ganina ai kasan in da nake, meye sai ka tsaya tambaye-tambaye, zan kashe wayata in magana zaka fadamin, ya karashe maganar yana kokarin datse wayar, cikin zafin zuciya Sanin halin sa da yayi na saurin daukar zafi yasa yace"zaka fara halin naka ko, daga magana sai hayaniya, baka tsaya ka saurare ni ba, dan Allah ka rage wannan zafin zuciyar taka" Shiru yayi masa, Maddibo ya cigaba da cewa "zan shigo in anjima, muyi wata magana, kwana biyu akwai abinda yake damuna wallahi" Da kyar yace"ina sauraron ka, bai saurari abinda Maddibo zai ce ba kawai ya kashe wayar, Da sauri Dogari ya karbi wayar ya aje ta kusa dashi, ya koma ya tsaya inda yake Ko minti biyar ba ai ba wani kiran ya kara shigowa daya wayar tasa, mika hannunsa yayi ya dauka sabida ba ya san irin abinda suke masa ko zama zai gyara duk sai su zabura suna dube-dube,wani lokacin in abin yayi yawa sai ya hanasu, to ko ya hanasu din ba sa dai nawa Ummina! sunan da ya gani yana yawo kan scerin din wayar sai da takusa tsinkewa sannan ya daga, "Yayi maka kyau, Fulani tafada ranta a bace, ta cigabah da cewa, yau ni kake gwadawa halin naka ko, sabida kawai na yi maka fadan gaskiya,wato kai ba a isa ai maka fada ba ko,shikkenan kazo ina ne manka in kaga dama" tana gama fadar maganarta ta kashe wayar bata saurari abinda zai ce ba Ya fi minti biyar kanshi a kasa yana latsa wayar, zuciyarshi tana masa wani mugun zafi, sam Ummi takasa fahimtarsa da inda ya dosa, shi ba auran ne ba yaso ba, yarinyar da takawo masa a matsayin wacce take so ta zama matarshi kuma uwar "yayanshi itace sam bata kwanta masa ba, Halisa kwata-kwata bata cikin tsarin matan da yake so ya aura Mikewa tsaye yayi, da sauri daya daga cikin hadimanshi ya gyara masa ta kalmanshi wasu masu gashi masu kalar ja da baki, saman su a rufe, ya zira cikin kafafunshi masu dauke da zara zaran ya tsu tamkar wanda bai taba taka kasa ba,Yadda yake tafiya sai ka zaci tausayin kasa yake ko baya san taka kasa, cikin kasaita yake tafiya, hakan ya zamar masa jiki tun yana yaro haka tafiyar shi take, Mama Fulani na ki shingede a wata katuwar dadduma da wani katon tuntu, suna hira da Jakadiya Shafa'atu, tana yan ka mata lemon zaki,dake Fulani tana san shan kayan frut shiyasa kullum bata rabo dashi a gabanta, Yayi sallama ya shiga cikin yanayin tafiyarshi ya karasa ciki sosai Tunda ya shigo Shafa'atu tayi kasa da kanta,har sai da ya zauna sannan ta dago kanta,ta kai gaisuwa sannan ta mike ta bar dakin cikin ladabi Mintuna goma tsakani babu wanda yace komai tsakanin Ummi da shi, Gyaran murya yayi ya ce"Ummi an tashi lafiya"? Shareshi tayi ta cigaba da shan lemonta Matsawa yayi kusa da ita ya rike kafafunta, ya wani marairaice yace"Ummina an tashi lafiya"? Harararsa tayi tace"sai yanzu kasan dani, zaka dameni da tambayar tashi lafiya, da ban tashi lafiya ba baza ka ganni ba" Shiru yayi mata tunda shi maganar ma wahala take mishi, har yanzu kafafunta na rike a hannunshi Tace"sakar min kafa mana" kin saki yayi ya kara rikewa tamau Tasan halin rigimarshi, shiyasa ta saki fuska kadan tace"Lafiya lou nake shikkenan ko"? Gyara zama yayi sosai yana kallonta fuskarshi dauke da wani kayataccan murmushi wanda ita kadai ce take ganinshi, yace"Masha Allah Ummina, "Me sa kaki daga waya ta kwana biyu jiya kuma na aiko kazo kaki zuwa,? Kasa yayi da kansa sabida yasan halin Ummi da saurin fahimtar mutum,gashi shi sam bai iya karya ba, yace " Ummi bani da lafiya" "Karya kakeyi" Ummi tafada kai tsaye" Baki ya bude yana kallon Ummin jin abinda tace saura kadan dariya ta subce masa,sabuda yasan halin Ummi ba ai mata karya "Ko nai maka karya ne"? Ummi tafada hankalinta kwance " Baki ba Ummina" yafada yana boye dariya "Yawwa ko da naji, in ban yi karya ba, sai in ce yaji ka daka min sabida nai maka maganar Halisa ko"? Shiru yayi Tace" ko ba haka bane"? "Hakane Ummi" yafada babu wani boye-boye Kallonshi take cike da mamaki tace"har yanzu kana nan a kan bakanka kenan"? Zama ya gyara sosai yana fuskantar mahaifiyar tasa, domin maganar da yakeso ya da ita muhimanci ce, yace"Ummi ba wai ina kin Halisa bane, a'a ina kin halinta ne, Halisa bata da tarbiya sam bata cancanci ta zama matata Uwar "yayana ba kamar yadda kikeso, amma tunda kina so shikkenan sai ayi amma dukkanin abinda ya biyo baya babu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108