Chapter 83
Chapter 83
mai kayan kamshi da tafarnu idan nasha shi duk zan daina jin wannan mutuwar jikin" Shahid yace"Bari in shiga shashan Mama yanzu nasan za'aha da maka" ****** Wasa farin girgi Shahid na futa yaga jama'ar gidan sun dura sabon buki irin na al'ada sai cashewa suke ana ciye-ciye ga masu kad'an k'warya nan sai bugawa suke "yan mata sun shiga suna ta rawa, gefe kuma wasu maza ne suke wasan wuk'ak'e, kai guri ya hargitse da sawu dukuna kowa na tashi murna, ko da yazo giftawa ta shashen Hajiya Kulu nan kad'e-kad'e ne kawai yake tashi irin na turawa,ta tara k'awayenta suna ta tsula stiyarsu Tsito ma yana zaune cikin mata yana ta busa sigari, duk macan da tayi masa sai daki d'uwawunta yana dariya aikuwa sai su saki shewa suna k'ara rawa da murgud'a d'uwawu" a gurin wasu daga cikinsu suke aikata fasadi batare da damuwar kowa ba. B'angaran Mama ma buki suke sosai irin na al'ada "yan uwa da abokan arziki sun cika mata falo kowa yazo taya ta murna, tana zaune cikin shiga ta alfarma ta fuskarta cike da walwala, Gimbiya Halisa tare da Mahaifiyarta Madabo suma nan suke hidimar bukin tare da Mama Halisa taci uban ado gwal ko ta ina alkyabar dake jikinta ma abar dubawa ce sai sheki take, jama'a sai kallonta suke ita kuma kanta yana kara girma dama so take ace tayi kyau , Taso Balaraba ta futo amma fafur tak'i futowa tana kulle a cikin d'aki kunya take ji sosai ita baza ta rashin kunyar da Halisa take ba, Lantana kuwa ai ta saje cikin mutane ta zama " yar gari sai kutsawa take tana shigshigi ga jama'a,, Tana sanye da wani irin material me kyau da tsada Multi color ne jikinsa duk stone anyi mata wani irin d'inki bubu wuyan rigar yaji stone work sosai tayi kyau kamar ka sace ka gudu d'aurin d'ankwalin da tayi ya k'yatar sosai Sam babu wani tarkacan kwaliyya a fuskarta, tana zaune gefan gado tana sak'awa da kwance wa su Sadiya kuwa Duk suna waje tun safiya. Da k'yar Shahid ya ganin Mama Fulani yayi mata bayanin abunda ya kawo shi, tace"Bari yanzu za'a had'o akawo muku in yaso d'aya daga cikin matan nasa sao tazo ta had'a muku abunci" Godiya yayi ya futa ta k'ofar baya, Ita kuwa Gimbiya Azima dama can shashen Waziri ta sauka da jama'arta nan suke shagalinsu, don haka ko da ta shirya ta futa tare da wasu bayinta da ta tawo dasu suna take mata baya, kai tsaye shashen Sarki! Ta nufa domin da zafi-zafi ake bugun k'arfe a ganinta wannan kwaliyyar da tayi baza ta tashi a tutar babu ba, dole Wanda akayi domin shi ya gani. Jakadiya Shafa'atu ce ta had'a musu duk abun buk'ata ta sanya baiwa Mariya wacce take shige da fuce shashen Sarki! Ta d'auko kayan abunci ta dunga kai wa can. Mama ta bi falon da kallo tana neman Halisa babu ita da alama ta futa, wasu k'wayenta ne suka zo, Sadiya ta kira Yarinyar tazo ta duk'usa Mama tace"Je ki kira Yayarku kice tazo inji ni" Domin tasan idan ba haka akace ba Balaraba tana iya k'in zuwa. Tana zaune taji sallama Sadiya kallonta take har ta k'araso kusa da ita tace"Yayarmu ka zo inji Mama" Balaraba tayi shiru tana tunani Sam bataso ta futa mutane suyi ta kallon ka" "Jeki ce gani nan zuwa" Sadiya ta futa cike da walwala. Mik'ewa tayi ta d'auki wani mayafi me kyau ta ya yafa har fuskarta sai da ta kusa rufewa, kanta a k'asa ta futa, kallonta kawai jama'ar dake gurin suke. Har ta k'arasa kusa da Mama ta tsuguna tana fad'in 'Mana gani" Shafa kanta tayi tace"Allah yayi miki albarka Balaraba ya albarkaci auranku,, Allah ya baku "yaya nagari" Duk jama'ar dake gurin suka amsa da "Ameen" Mama tace"An kai kayan abunci shashen me mijinku kije ki had'a musu shida abokansa" Gabanta ne ya fadi jin abunda Mama tace, a nutse tace 'To Mama" mik'ewa tayi a nutsu take tafiya k'afafunta duk suna hardewa tasan idanun mutane dake gurin suna kanta, tana futa, kowa ya fara fad'ar albarkacin bakinsa a kanta. 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿95* Da sallama a bakinta ta shiga falon. Kujerar da yake zaune tana kallon k'ofar shigowa karaf suka had'a ido, kasa d'auke idonsa yayi daga kanta, ta k'araso cikin falon a nutse su Shatima suna amsa mata sallamarta. Daining area ta tuna cikin yanayin tafiyar ta me d'aukar hankali, kallonta yake a sace har Shahid ya lura dashi sai ya tab'o Shatima yana nuna masa,suka dariya. Wayancewa yayi ya kalle su yana ya mutse fuskarsa yace"Dariyar meye wannan"? Da ido Shatima ya nuna masa Balaraba, tsaki yayi kamar gaske, ya d'an Sosa sumar kanshi kamar yadda ya saba yace"To sai me"? A hankali Shahid yace"Gaskiya kai d'an gata ne Wallahi mata uku rigis!" Tab'e baki yayi ya mik'e ya na k'okarin hawa saman bene. Shatima yace"Ya haka kuma kai da zamu ci abunci ka hau sama" Dai-dai baranda ya tsaya yana bashi amsa da cewar "Wanka zanyi yanzu zan futo" Ya bud'e dakin ya shiga. Tsab ta shirya abuncin cikin k'yatattun kwanuka irin na gidan sarauta, tasa wasu irin plate ta rufe masu kyau da k'yalli. A nutse tazo ta zauna ta saki fuskarta kad'an suka gaisa dasu Shahid, sai janta da hira suke sama-sama take amsa domin tun d'azu da suka had'a ido da Sarki! Tarasa kuzarin ta,,, Hak'ika ya cika cikkaken namiji yayi kyau cikin singlet d'in dake jikinsa, sosai ta dunga jin tsigar jikinta tana tashi,, tana jin wani irin yanayi a jikinta. Dai-dai lokacin da ya bud'e d'akinsa yana daga sama jikinsa d'aure da wani towol, da wani a hannusa, Balaraba yakewa magana, yana daga sama, Azima ta shigo falo bakinta d'auke da sallama, had'a ido sukayi da Balaraba sai taji zuciyarta ta buga, ganin irin d'anbanzan kyawun da Balaraba tayi kamar ka sace ta ka gudu,ji tayi kamar ta Burma mata wuk'a ta huta da masifar kishin da take ji nata. Saurin komawa yayi cikin d'akin domin baya so Azima ta ganshi, bashi da tabbacin cewar Balaraba taji abunda yake cewa. Wayar sa ya dauka ya kira numbar Shahid yace"Turo min Gimbiya tazo ta had'amin ruwan Wanka" Kitttt! Ya kashe wayar bai saurin abunda Shahid din zai ce ba. Shahid ya kalli Balaraba dake k'okarin mik'ewa domin tafiya ganin shigowar Azima tasan baza su kwashe ta dad'i ba ganin irin kallon da take mata, yace"Gimbiya umarni daga mijinku wai ki hau sama kije ki had'a masa ruwan Wanka" Cikin mamaki ta ke kallon Shahid d'in ita fa bata son iyayi, da itace take had'a masa ruwanka da zai zo yace taje ta hada masa. Shahid kamar yasan abunda take tunani yace"Nasan zakiyi tunanin cewar ai da bake bace kike had'a masa ruwanka ba, to yanzu duk nauyi ya dawo kanku" ya fad'a yana kallonsu ita da Azima ya cigaba da cewa "duk yawan bayinsa da kuyanginsa yanzu basu da alhakin kula dashi wannan aikin naku ne".
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108