Skip to content

Chapter 55

Chapter 55

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,262 words 0 views Progress saved
Download Book

Ajiyar zuciya ta sauke,ya cigaba da cewa"maganar gurin sai da abuncin ki ki bar wa su Hauwa'u su cigaba da samu a ciki, in sha Allahu xaki fara business in munyi aure" Cikin murna da farin ciki take masa godiya,a bisa karamcin sa a gareta, tanaji a yanzu bata da babban masoyi kamar sa, zata dunga k'okarin danne damuwar ta duk Dan ta kwantr masa da hankali, Salmanu ne, ya k'araso gurin hannunsa d'auke da wani faranti me fad'i ya aje a tsakiyar su, Moddibo yace"jeka abunka kaji" godiya Salmanu yayi ya bar gurin, Sauri-sauri yake ya gama abunda yake yaje ya fesawa abokinshi Dauda labari,shi Dauda yana b'angaran uwar gidan Sarki wato, Kulu,mai d'akin kudu, kenan Mama Kulu kenan, A nutse suke karyawa ita dashi, kana ganinsu kasan masoyan asali ne,Wanda suka yarda da Kansu, Usuman na gefe yana karyawa shima. Cikin nutsuwa yake sakkowa daga sama step by step hannunsa na rik'e dana Sadiya, yana sanye da wasu kaya na alfarma, masu tafe da wata alkyabba, kafarshi sanye da wani takalim me gidan ya tsa, babu nad'i a Kansa, duk da cewar shigar dake jikinsa ta nad'in ce amma bai yi ba, cewarshi ya gaji da kayan nauyi, sumarshi ya gyara,sosai da gemunshi, sai sheki yake,d'an k'aramin bakinsa mai d'auke da siraran lips Wanda suka d'an yi duhu kad'an, yayi Kyau kwantaccan gashi ya kewaye shi, as'usul idanunshi a lumshe kamar ko da yaushe,sai k'amshi yake zubawa, yana sakkowa masu hidima a gurin suna zubewa suna kwasar gaisuwa, ko wanne munafurci fall a abakinsa saboda ganinsa da k'aramar yarinya "yar shekara goma, cikin yanayin tafiyarsa ya nufi, daining teble d'insa Wanda yake cike da abubuwan ci, dai-dai inda suke zaune yazo ya gifta Balaraba taji gabanta yana fad'uwa duk da cewar ba ta kalli fuskarsa ba,gefansa ta kalla, Yanayin kwarjinsa da yadda yake tafiya cikin k'asaita ya furgitata ko ba'afad'a an San d'an mulki ne shi saboda abun a jinsa yake, jin kamshin turaran sa yasa Moddibo saurin waiwayo wa sai yaga yana k'okarin zama kan kujerar daining d'in, ga Sadiya ta zauna itama, ku-ku shi na tsaye gefe,yana jira ya dai-dai ta zamansa yafara had'a masa,abin kari. Mik'ewa yayi ya bar Balaraba a gurin ya nufi inda Sarki! yake zaune, sukai yi magana sama-sama,batajin abunda suke cewa, saboda a kwai tazara a tsaksninsu can ta hango,Sadiya ta zage sai kwasar girki take, babu wani kamun kai sosai yarinyar ta bata haushi, Moddibo ne ya k'araso inda take,tayi saurin kauda kanta saboda wani lokacin shima haushinsa takeji in taga yana wa Sarki!rawar jiki. "Gimbiya zanje in gaisa da mutan gida,zuwa yamma zan shigo sai muk'arasa maganar mu, don Allah ki cire fargar ba komai a ranki" A sake tace"shikkenan sai ka dawo a gaishe min dasu" "Zasuji insha Allahu" Yafad'a yana k'okarin barin gurin. Bayan futar Moddibo daga falo,sai yayi shiru saboda duk masu hidima a gurin sun gama sun futa,sai sautin AC ne kawai yake tashi, Usuman can gefe yake yana ta "yan wasaninsa, sai taji zaman gurin ya gundure ta, taja tsaki ya kai sau biyat r in ta d'aga kai ta hango Sadiya,na cin abunci ta sake sosai dashi tana masa hira har da dariya. Sam! tak'i yarda su had'a ido dashi, a sace take k'are masa kallo yana cin abunci cikin nutsuwa, gashi fuskarsa a sake,yana sauraron hirar da Sadiya take masa,cikin zuciyar ta take ayyana irin dukan da zata yiwa Sadiya. Taku! tafaraji k'was!k'was!k'was! irin na mace, takun takalmin ya d'auki hankalin ta har shi uban gayyar, da yake can inda yake zaune saitin k'ofar shigowa ne, shiyasa ya ga wacce ta shigo Gimbiya Halisa ce, Balaraba na zaune can wata kusuwar wa shiyasa bata ganta ba, Halisa tana tare da wasu bayi guda biyu suna take mata baya, wanda suka tsaya bakin k'ofar shigowa, can inda ta hange shi zaune ta nufa fuskarta babu walwala,ganinshi zaune da wata,daga can nesa tana yiwa Sadiya kallon wata k'atuwar budurwa, shiyasa ta sha kunu,sosai tana tunanin me ya kawo mace har falonsa duk da tasan halinsa ba ya Neman mata. Giftawar ta Balaraba ta hanga,ta bita da kallo daga sama har k'asa, tana ganin yanayin shigarta ta gane," yar sarauta ce. Sarki! kuwa d'auke kansa yayi daga kanta har ta k'araso gurin ta tsaya gami da d'ora hannuta kan kujerar da Sadiya take zaune tana mata wani kallo irin na raini tace"Habibi wannan yarinyar a ina ka samo ta,naga sam ba jinsin mu bace" Banza yayi mata,kawai ya cigaba da cinsa abuncin sa a tsana ke, K'ara maimata maganar tayi,ya d'ago kansa cikin jin haushin ta yace"ban sani ba, ki kauce daga kan mutane tunda ke baki da ladabi da sanin ya kamata" Ganin ya hasala! yasa ta fara yak'e tace" tunda na shigo na ganka zaune da mace a guri guda naji hankalina ya tashi shiyasa na rasa nutsuwa ta, sai da na k'araso kuma naga ashe ma yarinya ce,amma dai duk da haka hankalina bai kwanta da ita ba,yarinya sai kace,me dubi yadda take k'walo ido kamar mayya" Karaf! a kunnen Balaraba,dama taji abunda Halisa tace a farko Dan gane da Sadiya. Ranta a b'ace ta futo daga inda take,ta tsaya a gurin tana kallon su, a cunkushe ta bud'e baki tayi magana, tace"ke! Sadiya baro gurin nan, kinji ko" Duk hankalinsu ya koma kanta har shi,uban tafiyar, ganin fuskar yayar ta a murtuke ya fad'ar mata da gaba,sai ta fara yunk'urin mik'ewa tsaye domin ta cika umarnin ta, yayi saurin dafe hannun yarinyar ya hanata tafiya, ido ya zubawa Balarabar dake tsaye can gefe tana cika tana batsewa, ganin Sadiya tak'i tasowa yasa ta k'ara buga mata tsawa,a karo na biyu. A nutse ya d'an daga muryarsa yace"tak'i zuwa d'in in kin isa kizo ki jata,da k'arfi mugani" *Comments Vote and Share* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ _*DEDIGATED*_ *_TO_* ```RAHAMA ALIYU``` ```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM``` *🅿63* Cike da karsashi,da jarumta ta durfafi inda suke fuskarta a had'e tamkar wacce bata tab'a dariya ba, tana zuwa tafara yunk'urin fuzge hannun Sadiya daga cikin nasa, a nutse ya d'ago kanshi tare da zuba mata idanunsa,ya bud'e tar! Gabanta ya buga! sai kace mai lak'ani a idonsa, duk gwiwarta ta sage! kanta ta sunkuyar k'asa domin bazata iya jurar k'alon k'wayar idonsa ba, amma duk da haka bata fasa k'okarin fuzge hannun Sadiyar ba saboda k'arfin Hali, rik'e hannun yayi tsaf! da tazo zata k'wace sai su had'a hannu, sai ya had'a da hannun nata ya matse,ganin abun nasa harda iskanci, yasa ta fuzge hannunta tana zabga masa harara, batare da tabari ya gane gazawar ta ba,ta kalli Sadiya,cikin fad'a tace"zan kama ki,wallahi tunda kike barin maza suna rik'e miki hannu" barin gurin tayi a fusace,ta kama hannun Usuman suka haura sama. Kallo ya bita dashi, fuskarsa d'auke da murmushi, girgiza kai yayi kawai yana mamakin k'uruciyar ta, yanzu ya gane itama yarinya ce, sakin hannun Sadiya yayi dake zaune tana mayar da k'walar da ta taro a idonta,saboda tasan halin masifar yayarta Yace"kwantar da hankalin ki kinji ko Halimatu, duk abunda tayi miki in mun had'u zan rama miki, tashi kije" mik'ewa tayi jikinta a sanyaye, ta haura

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108