Skip to content

Chapter 53

Chapter 53

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,215 words 0 views Progress saved
Download Book

a furgice zata ruga da gudu cikin d'akin, sai yayi saurin damk'e hannunta, inda yaji zafi rad'au, da alama zazzab'i yarinyar take, k'okarin fuzge hannuta take cikin tsoro, yayi k'asa da murya sosai yace"me yasa kika futo nan uhumm"? Shiru Sadiya tayi tana kuka, "Baki da lafiya ne"? D'aga kai tayi tana zubar da hawaye " ina yayar taki"? yafad'a k'asa-k'asa "Bacci take yi, na tashe ta tak'i tashi gashi ni tsoran d'akin nake yayi girma da yawa" Bai ce komai ba, ya kama hannun yarinyar suka shiga d'akinshi ya futo da maganin zazzab'i ya ciro biyu yace"kinji abunci da zaki kwanta"? d'aga kai tayi, ruwa ya ciro mara sanyi ya mik'a mata maganin yace"maza sha kinji ko, yanzu za ki daina jin ciwon insha Allah" Cikin daurewa Sadiya ta watsa maganin a baki ta had'a da ruwa ta shanya, yace "muje in raka ki ki kwanta, kar ki k'ara futowa sai da safe" Tare suka futa hannusa rik'e da nata, Balaraba na tsaye a bakin k'ofa kamar ta d'ora hannu a ka, tana kamar an tashe ta ta farka daga nannauyan baccin da ya d'auketa,wanda kafin tayi shi sai da ta shafa, saboda tunanin da yayi mata yawa, kawai sai ta duba taga k'ofa a bud'e babu Sadiya, ta mik'e a zabure! ta sauka k'asa, duk girman farlon ta dudduba bata ganta ba, da sauri ta dawo sama ta tsaya bakin k'ofar tarasa abunda zatayi, hawaye kawai sai ya k'wace mata, zuba kawai suke zuciyar ta sai sak'e-sak'e take mata. kawai sai taga an bud'e k'ofa, suna had'a ido yayi saurin kau da nasa dan bazai iya kallonta a yanayin da take ciki ba, kai babu d'an kwali, ga kayan jikinta sun futo mata da k'irar ta, da sauri! tazo zata fuzge hannun Sadiya, tana kuka, gabanta sai fad'uwa yake tana addu'ar Allah yasa bai cutar mata da k'anwa ba, rik'e hannun yarinyar yayi tamau! yak'i saki yana son yaga iya gudun ruwan ta, hannuta tasa tana tureshi , kamar me ture dotse sam yak'i motsi cikin kuka tace"Allah ya isa tsakanina dakai, mugu azzalimi Allah sai ya saka mana, ka cuci marainiyar yarinya sai nayi shari'a da kai" tana kuka tana dukan k'irjinsa take maganar. Lokaci guda ya fahimci abunda take nufi, cikin tsantsar b'acin rai da damuwa ya fidda hannu ya tsinka mata mari, zuciyar shi tana tafasa yace"me kike nufi ne da wannan maganar taki"? "Duk abunda kake nufi shi nake nufi" tafad'a cikin hayaniya, abunka da dare, gari yayi tsittt! shi tsoransa ma kar hadiman sa suji tunda wasu, suna kwana a k'asa, wa ni k'ebantaccan guri, wanda yake da k'ofa w ciki da waje, saboda haka sai ya sa k'irjinsa ya tura ta cikin d'akin ya shiga shima da Sadiya a hannusa yarinyar duk ta furgice! da sauri Balaraba ta mik'e tsaye, saboda fad'uwa tayi k'asa lokacin daya angiza ta, tayi kan Sadiya tana dukanta tana kuka, kamar wata mata hankali, tunkud'e ta yayi a karo na biyu ta kara fad'uwa k'asa yace"wallahi ki shiga hankalin ki, banza shashasha kawai kin saki baki kina bacci, saboda abunda kikazo yi kenan, kin bar yarinya ta futo da zazzab'i a jikinta, dube ki don Allah" yafad'a yana mata banzan kallo, ya cigaba da cewa"duk abunda kike tunanin nayi da ita to nayi d'in ,kema bazan barki ba, zan biyo dare inyi dake, kuma tunda kika shigo gidana babu ke babu futa kin shigo kenan, zanga k'arshen rashin kunyar ki" Yana gama maganar sa ya fuce daga d'akin kamar walkiya. Sadiya ta jawo tana kuka tana duba mata jiki, ita har ga Allah ta tsorata dashi, sam bayanin da yayi mata bai gamshe ta ba, Yana komawa d'akinsa ya zauna bakin gado ya dafe kansa cikin damuwa, wannan yarinyar ta b'ata masa rai, ko neman mata yakeyi me zai tsinta jikin yarinya k'arama irin wannan, mik'ewa yayi da sauri yaje ya kunna CCTV Camara, ya sai ta komai, idon ya zuba mata sosai yana kallon yadda bakinta yake motsi, sai masifa takewa yarinyar tanayi tana kuka, Wani murmushi ne ya k'wace masa ya girgiza kai kawai, shi mamakin yarinyar ma yake, da gaske zargin sa take yayi wani abu da yarinyar. *Comment d'in da kuke min baya isa ta, in kun k'ara in k'ara yawan typing* *Comment Vote and Share* https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ _*DEDIGATED*_ *_TO_* ```RAHAMA ALIYU``` ```BISIMILLAHIR- RAHAMANIR-RAHIM``` *🅿61* Yana zaune yana kallonta cikin CCTV Camara ta zabga ta gumi dagani tana cikin damuwa, mik'ewa ya ga tayi tana gyarawa k'anan nata kwanciya, ta nufi toilet, da sauri ya d'auke kansa lokaci da ta juya baya tana tafiya, gabanshi ya dunga fad'uwa, idonsa k'urr! a k'ofar ban d'aki har ta futo da alamu alwala ta d'ora, yana kallo ta bud'e k'aramin a kwatunsu ta d'auko zanin atamfa da wani k'aton hijab tayi shirin yin sallah, can inda a ka tanadi daddumar sallah yaga ta nufa ta tada sallah, agogon bango ya kalla, hud'u shaura minti ashirin, mik'ewa yayi shima a nutse a shiga toilet ya had'a ruwa, yayi wanka, sannan ya d'auro alwala, niko nace, ko wankan me yayi oho,da asubar fari shi da ba mata gareshi ba. Sabuwar jallabiya fara kar, ita ya sanya a jikinsa, yaje ya kashe CCTV Camara, ta idar da sallahr tana zaune tana kallon gabas hannunta duk biyun a sama da alama addu'a take, sai yaji yarinyar ta burge shi, da alamu me ibada ce, Sallahar raka'atanin fajri ya tayar, bayan ya idar ya zauna yana jan jarbi har lokacin da a kafara kiran sallahar asubahi, sannan ya mik'e a nutse ya sauka k'asa, suka had'u da d'an rakiyar shi yana zaune a farlo yana jiransa, yana ganin sakkowar sa ya mik'e tsaye yana kwasar gaisuwa suka gaisa, a mutum ce, Sarki! ne a gaba shi a baya har suka isa masjid. Balaraba kuwa ta dad'e kan abun sallah bayan idar da sallah asubahi tana rok'on Allah ya futar da su daga damuwar da duke ciki da ita da "yan uwanta ba, bacci ne ya dunga fuzgarta dan haka nan kan abun sallahr ta b'ungire bacci ya kwashe ta. To bayan an idar da sallah ne anyi gaishe-gaishe kowa yana so ya koma shashensa, Moddibo yake tambayar shi amanar da ya bashi, rasa abunda zai ce masa yayi kawai ya share shi, Moddibo yace" to tunda ka k'i fad'amin muje inga ya suka kwana" A hasale Sarki! yace"ni wannan binbinin naka ne banaso wallahi, ni yanzu bacci nakeji jiya sam banyi baccin kirki ba kabi ka dameni da zan wata Balaraba, da ta hana mutane sakat!" Cikin sanyi murya da sanyi jiki Moddibo yace"muje dai in ganta, wallahi jiya kwana nayi ina mafarkinsu ita da "yan uwanta, ina kaunarsu, a zuciyata kuma nakeji kamar bazan yi wani dogon zama dasu ba" Cikin mamaki yake kallon Moddibo lallai yau ya gazgata da cewar Moddibo da gasken gaske! yake son Balaraba, bai tab'a jin tausayinsa ba irin na yau, tabbas ya yarda so bala'i ne. Yace"kan wane dalili zaka dunga yadda zuciyar ka tana maka sak'e-sak'e na abu marasa kyau, na d'auka tuntuni ka daina irin wad'annan tunanin naka" "Mubar maganar kawai

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108