Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,224 words 0 views Progress saved
Download Book

babu yabo babu fallasa yace"Khalifa ya kirani a waya dazu yace kana nema" "Kwarai kuwa" Waziri yafada yana gyara zamansa kan kujera "To Masha Allah, ina sauraron ka" Mikewa Mama tayi ta bar gurin dan ta barsu su sake suyi maganarsu amma tana mamakin abunda zai sa Waziri kiran Sarki! sabuda tasan basa jituwa ko kadan. "Wato kana jina ko"? "ina jin ka" Yafada kai tsaye! "Kasan abokina Maimarta ba Sarkin Yalwa, ko? Cikin nutsuwa yace" Eh nasanshi " "To shine ya ke neman alfarma a gurina da gurinka, a kan yana so ka auri yarinyar shi Azima, ta nuna tana sonka, to shine na nake neman alfarma a gurinka, a matsayi na na Mahaifinka, kar ka bani kunya, a gurin abokina kaje ka nemi yarinyar nan, insha Allahu baka da matsala da ita, yarinya ce nutsatstsiya" Kanshi na kasa tsawon minti biyar bece komai ba, daga bisani ya dago kanshi, a nutse yace" Zanyi tunani akai" "Zakayi tunani akai"? Waziri ya maimaita maganar da yayi cikin sigar tambaya, "Fuskarshi ya hade sosai ya dago kanshi yana kallon Waziri, yace" Allah ya taimake ka, wannan maganar da kazo min da ita tayi min tsauri dayawa dole ne inyi nazari a kanta, kabani nan da kwana biyu,duk abunda na yanke zan maka magana" Kwantar da kai Waziri yayi sabuda yana nema, yace"A'a baza muyi haka da kai ba, Magajin Sarki, ka fada min kawai yanzu, wannan abun me sauki ne, a gurinka, domin kasan ko ba yau ba, dole zaka hada mata hudu,sabuda muna saka ran zaka gaji kujerar mahaifin ka" Wadannan maganganun da Waziri yayi sun bashi mutukar mamaki, wai yau da bakinshi yake kiranshi da Magajin Sarki, lallai akwai wani abu dake zuciyar shi wanda yake boye wa, Amma sabuda ya kyaleshi ya tafi yasa yace"Shikkenan na amunce da, Allah ya shige mana gaba, Murmushi Waziri yayi yace"Allah yayi maka albarka Magajin Sarki, in sha Allahu zakaji dadin auran yarinyar, kaga sai a hada da Halisa ko" "Duk abunda kuka yanke dai-dai ne a gurina" yafada yana kokarin mikewa da niyar tafiya Hannu ya mika masa suka yi sallama, Waziri sai shi masa albarka yakeyi, sai murna yake kamar ya ari baki, nan Sarki! ya barshi, cikin farin cikin amuncewar sa ****** *Balaraba* kuwa kwana tayi tana kuka a ranar kamar ranta zai futa, taji ciwon wulakancin da Sarki! yayi mata, wai ita yake kira "yar towo-towo " yar bakin kasuwa, tayi kukan rashin iyaye, tasan duk rashin su ne ya jawo mata wannan wulakancin, gashi tana shigowa gidan Lantana ta tare ta tana zagi, wai sai ta futo mata da kudin da ta samo, in ba haka ba, zata shiga gidan ba, nan su Shamsiyya suka dinga ihu! suna dariya, tafi minti ashirin a tsaye a soro sai da Walidi ya shigo gidan, ya ga abunda yake faruwa,ya zage Lantana tas! har Uwa bai bari ba duk ya hada ya dinga dura musu ashar, ya rike hannun Balaraba suka shiga ciki, Su Sadiya da Usuman suna zaune, a tsakiyar dakin sai kuka sukeyi, babu haske,ga uban sauro sai tashi yake, a dakin, haka ta shiga takamasu ta rungume tana kuka, har sukayi bacci, kwata-kwata zaman gidan ya ishe ta, dole ne ta samawa kanta ma futa. Sam, bata yi wani baccin arziki ba, da ta rufe ido sai ta hango shi lokacin da yake tofa mata miyau din bakinshi, bata jin bacin ran abunda Lantana tayi kamar wannan, sabuda tasaba, dashi,tunani kawai take, wace irin hanya zata bi ta rama abunda yai mata, Tunda tayi sallahr asubah bata koma ba, tana zsune kan abun sallah tana lazimi, bacci yana fuxgar ta, kadan-kadan, ta jiyo muryar Lantana tana kwala mata kira, "Balaraba, ke Balaraba" Lantana tafada tana dukan kofar dakin kamar zata karya ta. Tana jin ta tayi shiru har sai da ta ha'da carbi sannan ta mike a nutse taje ta bude kofar, Lantana tayi mata wani kaskantaccan kallo, tace"au! kwana kikayi kina kuka naga idanunki sunyi jajazir!" tafada tana rike ha6a cikin mamaki! "Me zanyi miki ki ke buga min kofa" tafada kamar bata san abunda ya kawo ta ba, "Au! tambaya ta kike me zaki min"? Lantana tafada cikin mamaki! " to kudin gasara zaki bani" ta karashe maganar tana gyara daurin zaninta "Lantana yau bani da kudi, sai gobe" "Baki isa ba wallahi" Tafada cikin hayaniya da masifa Rantsuwar da tayi ya mutukar bawa Balaraba,mamaki, ita ko yau batayi niyya bayar wa za taga inda wanda ya isa yasa ta bayar *Comment* *Vote and Share* [11/07, 05:47] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®REAL BINTU BATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*Zamani Writes Association*_🤝🏻 _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` *🅿45* ```Bisimillahir-rahamanir-rahim``` Kawu Sallau ne ya futo daga daki, hannushi rike da wata karamar redio yana kokarin dai-dai ta tasha, dake safiya ce , yana so ya saurari labarai, kofar dakin Balaraba ya nufa inda Lantana take tsaye tana karewa Balaraba zagi, tace"Jiya kinfi awa daya a waje,kuma ance me mota ne mutumin da yazo gurin ki amma sabuda kin raina mana hankali shine zakice baza ki bamu kudin gasara ba to ko sai kin bayar sannan zaki futa daga gidanan kinji na gaya miki" Jin abunda Lantana tace yasa Sallau saurin karasowa gurin yana rage karar redio dake hannushi yace"Lantana wai me yake faruwa ne, tun daga daki nake jiyo hayaniyar ki" Gyara tsawuyar ta tayi tace"Yo in banda sharri irin na wannan yarinyar, da tsabar mugun abu, wai yau bata da kudin gasara wanda take bamu muna siya muna karyawa dashi, jiya fa Wani me mota ne yazo zance gurinta, ta dade a waje,kafin ta shigo gida" Walidi ne ya bude kofar bandaki ya fito,hannushi rike da bota, da alama sai yanzu zai yi sallar asubah, a jiye botar yayi nan bakin rijiya ya nufi gurin da suke, ya kalli Lantana yana wani ciccije baki yace" Yawa! kike fa Lantana, Ehh wannan da kuke gani fa tafi karfin wulakanci a gurinku, kune mutsiya ta daga ke har ita Uwa!din, kudin gasarar banza da wofi, kullum da take baku kudin ai babu wanda ya taba gode mata, sai dai kullum ku bita da zagi! To wallahi kukayi wasa zan k'ona kudin da aka bani in baku, banzaye fattararru kawai!! ya karashe maganar yana wani tangadi kamar zai buge Lantanar, da ssuri ta matsa gefe guda, Cikin mamaki tace"Ni kake zagi ko Walidi" "Kinga Lantana"! Walidi yafada yana nuna ta da yatsa Ya cigaba da cewa" nifa a kan wannan zan iya kaddamar miki, gwara ki kauce kawai, Eh! ni dai na fada miki" Shiru Lantana tayi tana zare ido, shi kuwa Sallau ko a jikinsa, duk irin rashin mutumci da Walidi yakewa mahaifiyar sa, a cewarsa ai itace ta jawo wa kanta, Washe baki yayi yana kallon Balaraba yace" "yar Albarka, sannu da kokari, kinji ko ki cigaba da hakuri damu, ni dai nasan ban miki wani laifi ba, sabuda haka zan tafi gurin me shayi, yanzu" Balaraba ta gane munufar sa, sabuda haka sai tace" Kawu kai ma yau sai dai kayi hakuri, domin bani da kudin da zan baka yau da gobe kayan Allah" Murtuke fuska yayi, ya hau zuba mata ruwan ashar, yace"wato nima

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108