Chapter 35
Chapter 35
tayi bata ce komai ba, "Tuba nake gani tun misalin bakawai ina nan ina zaman jiran ki nazo in baki hakuri bisa laifin dan uwana yayi miki jiya" Ajiyar zuciya tayi, tace "Yusuf halinka daban da kai da dan uwanka" Murmushi yayi kamar yana kusa da ita, yace"Halinmu daya da dan uwana,shima dan dai baku fahimci juna bane, ta wani gefan ma yafi ni kyawun hali" "Hummm, yanzu dai ina kan hanya, ganin zuwa sai muyi maganar" bata saurari abunda zai ce ba ta kashe wayar, Tunani take wace hanyar zata bi domin ta dauki fansar abunda Sarki! yayi mata _Muje zuwa My Fans๐_ *Comment* *Vote and Share* [11/07, 20:48] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ๐ธ๐ป๐ธ๐ป๐ธ๐ป๐ธ๐ป ^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^ ๐ธ๐ป๐ธ๐ป๐ธ๐ป๐ธ๐ป _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *ยฎREAL BINTU BATULA๐* *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` _*Zamani Writes Association*_๐ค๐ป _*DEDIGATED*_ _*TO*_ ```{RAHAMA ALIYU}``` *๐ ฟ46* ```Bisimillahir-rahamanir-rahim``` Tun kafin ta futo daga Napep din ta zuge jakarta ta futo da niqabi ta rufe fuskarta sabuda ganin kasuwar ta soma cika da jama'a wataran har kusan faduwa take sabuda idanun jama'a Sai da takara jaddadawa Ashiru akan kar ya wuce shida da rabi na yamma, bai zo ya dauke ta ba,domin bata so ta dinga kai wa Magariba a waje. Duk da niqab din dake sanye a fuskarta hakan bai hana wasu gane ta ba, sabuda yanayin tafiyar ta, wasu suke gane ta, shiyasa bayan wucewar ta suka kama yi da ita, Wani Alhaji Musa yace"wallahi na rasa yadda zanyi in tunkari yarinyar can, sabuda mugun kwarjinin da take min,gashi Allah ya jarrabe ni da sonta kamar me" "Ai ba kai kadai ba" wanda yake kusa dashi ya fada, ya cigaba da cewa"ni kaina kwarjini take min,wallahi ina mutukar son tsarin jikinta, da yanayin tafiyar ta, yarinyar fa tayi sosai, matsalar kawai "yar talakawa ce" "Duk wannan ba matsala bace a gurina mutukar zan samu fuska a gurinta" Alhaji Musa ya fada, yana jan numfashi, yace"kwanaki da muke zancan ta da Alhaji dan Yaro, yake fadamin, wai Yusuf Maddibo ne yake neman ta,kasan Abokin Buba ne,shi kuma Buba kasan tare suke harkokinsu dashi,shine yake fada masa" "Ai kaji abunda nake fada maka,wallahi yarinyar matar manya ce,sosai amma in kaga zaka iya shiga bisimillah,amma fa zaka sha wulakanci, domin shi ma Yusuf din, dan kore ne a gurinta har yanzu bata karbe shi ba" "Duk wannan baya damuna,indai zan samu biyan bukata" Alhaji Musa ya fada, nan suka cigaba da tattauna maganar, Kafin ta shiga gurin nata sai da ta tsaya suka gaisa da Me kosai cikin mutumci, ta futo da dari biyar ta mika mata tace"gashi a rabawa yara kosai sadaka" Almajiran dake zaune gurin suka dinga murna da farin ciki, dama dakon zuwanta sukeyi sabuda sun saba kullum tana sawa a raba musu kosai, nan suka dinga godiya gami da fatan alkairi Anutse ta shiga ciki inda ta tarar da Su Hauwa'u suna ta kai wa da kawo wa komai tsaf duk wani costomas an bashi abunda yake bukata, sama-sama suka gaisa da su, fuskarta babu walwala, kullum haka takeyi sabuda bata son wani ya kawo wargi a cikinsu,can gefe guda ta hango Yusuf zaune cikin kujera, ya zuba mata ido,kamar zai cinye ta,fuskarsa dauke da wani kayataccan murmushi, da sauri ta dauke kanta, ta nai wa Hauwa magana, Reciptoin ta futo ta zauna kan kujerar ta, kamar ko da yaushe, tana kallon masu shige da fuce, a gurin. Ganin ta futa yasa Maddibo mikewa a nutse ya bi bayanta, mutanan dake gurin suka bishi da kallo, ganin dukaninsu a gurin suka taddashi,gashi ya mike ya futa batare da yaci komai ba. Zama yayi kujerar dake fuskantar ta fuskar shi dauke da murmushi har ila yau, yace"Ranki ya dade,barka da zuwa" Sakin fuskarta tayi tace"kai ma ranka ya dade,fatan ka tashi lafiya"? Bai yi tsammanin zata sakko da wuri haka ba, ganin yadda ranta ya ba'ci jiya, amma abin mamaki ko a fuska bata nuna masa ba,asali ma yau tafi kowane lokaci sakar masa jiki. Yace"Lafiya kalau, na tashi ke fa"? "Nima lafiya kalau" tafada tana yi masa wani kayataccan murmushi. "Hakuri nazo na bawa Gimbiya sarauniyar zuciya ta" Yafada yana wani karyar da kai, gwanin tausayi "Humm Yusuf kenan, wane hakuri zaka bani, ai kai ba kayi min laifin komai ba,wanda yayi laifi shi ya kamata yazo ya bada hakuri in ana so in huce, fushina" Ta karashe maganar tana wani fari da ido. Shiru yayi yana binta da kallo,cikin so da kauna, yace"Ayi masa afuwa,Gimbiya na ari bakinsa naci masa albasa, abunda yayi shi, shine yayi ni, A yafe masa" Girgiza kai tayi tana tabe baki tace"in kaga na hakura to sai dai idan ka dauko shi ka kawo min shi nan yazo gurina a karo na biyu,wannan zuwan nasa ya zama na bada hakuri ne, a gurinshi, shine kawai zai sa na hakura, Murmushi yayi yana gyada kai cikin zuciyar sa yace"lallai na kara tabbatar da cewar sarauta a jinin yarinyar nan yake,wato ta na nufi yaje ya dauko Sarki! a karo na biyu ya kawo mata cikin kasuwa, lallai lamarin Balaraba ya shallake tunanin sa, ko mutuwa zai yi baya tunanin Sarki! zai yadda yazo kasuwa gurin ta da zumar bata hakuri, sai dai idan zai rufe masa yaki fada masa gaskiya, amma domin ya nuna mata son ta dake cikin zuciyar sa na gaske ne, yasa yace"duk wannan me sauki ne, mutumi na zai iya zuwa ya baki hakuri kamar yadda kike bukata,sabuda dan uwana yana mutukar son abunda nake so" Harararsa tayi tana fari da ido tace"ni dashi wa kafi so"? Dariya yasa yana kallonta yace"matsayin ki daban, nashi daban, a zuciya ta, amma bari ki fara ganin naki matsayin a gurina" ya karashe maganar yana kokarin futo da wayarsa aljihu, A nutse tace"me zakayi naga ka futo da waya"? Kashe mata ido daya yayi ya sai ta Camara ta wayar shi ya hau daukar ta a hoto, Da sauri ta sanya hannu tana kare fuskar ta domin yayi mata bazata, "Kabari bana so dan Allah" tafada tana kauda fuskar ta. Sai da yai mata kusan goma sannan ya dai na Shan kunu! tayi tana dauke fuska tace"ka dauki hotana ba da yarda ta ba zakaje ka nunawa abokan ka su kalli munina ko"? Yana dariya kasa-kasa yace"babu wanda zan nunawa sai mutum daya" "Wanene shi" tafada cikin sigar tuhuma "Mutumin ki ne" Tabe baki tayi tace"har yanzu ban yadda da son da kake min ba har sai kaje ka kawo min shi nan sannan zan yarda da kai" Wayar shi yake latsawa yana murmushi yace"bari kiga Zahiri,kafin in kawo miki shi bari in kira shi a waya sai kuyi magana" Numbar Sarki! yafara lalube cikin wayar tasa Shiru tayi kawai tana kallon shi, duk layin da ya kira a kashe, na ukun ne ya shiga,sai da ta kusa katsewa sannan yaji an daga wayar, da sauri ya bude handsfree ya mika mata, Ta karbi wayar cikin basar wa Muryar shi taji kamar ta me bacci, yace"Assalamu alaikum" Gabanta ne ya fadi! jin muryar shi duk da kasa-kasa take bai hanata jin dadin ta ba, Cikin jarumta! tace"Amin wa'alaikassalamu" Jin muryar mace yasa shi sauri tashi zaune, dama a kwance yake a kan wata katuwar Sofa, Mamaki yake, me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108