Skip to content

Chapter 63

Chapter 63

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
Download Book

Halisa, Hajiya Madabo mahaifiyar Halisa Gimbiya Azima, domin itama tun yammacin jiya tazo sai ta riski abunda yake faruwa, duk suna zazzaune kowa da carbi a hannu,idanunsu sunyi jajazur! bai saurare su ba ya wuce da Balaraba ciki, har bedroom d'in Mama Fulani, kwantar da ita yayi a makeken gadonta,ya nufi k'aramin firji dake d'akin,ruwa ya ciro me sanyi sosai ya bud'e ya fara tuttulawa a jikin Balaraba, wanda yayi dai-dai da shigowar Mama Fulani cikin tashin hankali,tace "Me yasa me ta"? " Suma take Mama wannan yarinyar amanar Moddibo ne, Mama ki taimaka min kar tabi bayansa" Yafad'a tamkar wanda baya cikin hanlalinsa, lallai na yarda da ake cewa komai girman mutum a gaban iyayensa Yaro ne.Rarrashin sa take ganin yadda ya tada hankalinsa, ragowar ruwan dake hannunsa ta karb'a ta yayya mata, cikin sa'a Balaraba ta bud'e ido tana sakin wata ajiyar zuciya,, kalle-kalle kawai take yayin da take jin wani irin ciwon kai! Ajiyar zuciya ya sauke ganin ta dawo hayyacinta yayi saurin futa daga d'akin don kar ta ankara dashi a gurin, yana Futa k'aramin falon ya fad'a musu umarnin da me Martaba ya bayar, mik'ewa sukayi suka futo domin zuwa fada, tsakanin Halisa da Azima harara ce ke had'asu, Halisa wani bak'in kishi ne yake damun ta ganin yadda Habibinta ya rungomo Balaraba a jikinsa,sai kace Wanda ya dauko matarsa, itama Azima nata b'angaran haka abun yake domin kishin da taji lokacin da taganshi da Balaraba har yafi na Azima, kawai daurewa take,dan dai gidan mutuwa tazo. *Gaskiya ina jin dad'in comment d'inku*😀 _*ANATARE IYA WUYA*_ ❤❤❤❤❤❤❤❤ _Ina taya ku jimami na rashin Moddibo Allah ya bamu hakurin jure rashin sa_ [09/08, 17:22] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` _*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_ *🅿71* Cikin dauri Hajiya Kattime tsuguna gaban gawar Moddibo tayi masa addu'a sosai gami da nema masa afuwa gurin Allah,A fili tace"Yusuf ni mahaifiyar ka na yafe maka dukkanin abunda kayi min wanda na sani da Wanda ban sani ba,ina fatan Allah ya had'amu a aljanar firdausi" "Ameen" Ameen"Abunda mutane ke cewa kenan.me Martaba ya aika ai kiran Waziri tun d'azu yak'i zuwa, haka me Martaba ya bada Umarnin d'aukar Moddibo a kai shi gidansa na gaskiya, Sarki!ne ya d'ora makarar gefen kafad'arsa Galadima a gefe sauran mutane suka taya su rikewa a ka futa da Moddibo futa ta har abada, sai bayan futa dashi ne zuciyar Hajiya Kattime ta karye sai ga hawaye na biyo kuncinta,nan jama'ar dake gurin suka dunga tausar zuciyarta,da k'yar dai suka koma Shashen Mama Fulani, inda take zaune gefen Balaraba wacce take ta rusa kuka kamar ranta zai futa, magana take so tayi amma takasa saboda yanda muryarta take sark'ewa, tsabar kukan da take. Hajiya Kattime ce ta shigo d'akin saboda jikinta na bata wannan yarinyar da Sarki!ya shigo da ita, itace Balaraba. Kallonta Mama Fulani take har ta k'araso ta zauna gefen gado, tace" Ina kyautata zaton wannan itace yarinyar da ake rigima a kanta ko"? Mama Fulani tace"Itace kin ganta nan kuka take tak'i jin rarrashi" Cikin dauriya Hajiya Kattime ta matsa kusa da Balaraba ta rik'e mata hannuwa cikin tausayi da taushin harshe tace"Dole kiyi kukan rashin Moddibo, kiyi hakuri ki barwa Allah ikon shi, nice na haifi Moddibo ina ganin babu wanda zai kai ni jin zafin mutuwarsa, irin wannan ta farar d'aya, to da yake nasan kowa na hakane na hak'ura na barwa Allah mutuwa rigar kowa ce dole inda ya tafi zaki tafi zan tafi haka Mama Fulani zata tafi, saboda haka ina rokon ki ki yi shiru don Allah in ci Albarkacin Moddibo bana son ki jawowa kanki wata lalurar yanzu ke din kece zan dunga kallo a matsayin Yusuf d'ana, kiyi hakuri kiyi masa addu'a domin ita yake bukata a gurin mu" Cikin kuka Balaraba tace"Mama me yasa Yusuf zai yi min haka? bani da kowa sai shi,Yusuf shine gatana Allah ne gatana,gashi ya tafi ya barni lokaci guda, *Innalilahi wa'inna ilahi rajiun* Ya Allah ka kawo min a gaji" Ta k'arashe maganar tana jin tamkar numfashinta zai d'auke. Wasu hawaye Mama Fulani ta goge na tausayin Balaraba sosai yarinyar ta bata tausayi. Hajiya Kattime tace"Kar kiyi sab'o kinji ko, lokacinsa ne yayi dole ya amsa kiran da a kai masa" Mama Fulani tace"Ki daina kukan rashin iyaye kinji ko mu zamu zame miki uwa da uba Insha Allah ba zaki maraici ba" Cikin kuka da damuwa Balaraba tace"Nagode sosai kamar yadda kika fad'a Mama nima zan muku biyyaya dai-dai gwargwado tamkar Ku ne kuka haife ni" Hajiya Kattime tace"Yanzu ina "yan uwan naki"? Sai sannan ta tuna dasu Sadiya,k'okarin saukowa take daga gadon cikin faduwar gaba, tabarsu su kad'ai bata san wane hali suke ciki ba. Hajiya Kattime ta rik'eta tace" Bari aje a d'auko su,kinji ko kar ki futa cikin wannan halin" Muryar ta na karkarwa tace"Suna can Shashen Sarki!nan muka kwana" "Shikkenan bari in tura Mariya taje ta dauko su ki kwantar da hankalin ki" Hajiya Kattime ta mike ta futa. Mama Kuwa k'ara kwantar wa da Balaraba hankali take,tana d'an yi mata tambayoyi cikin hikima,irin tasu ta manya,nan ta fuskanci yaran sun sha wahalar rayuwa kuma sun taso cikin maraici, lokaci guda taji sun shiga zuciyarta zata iyayin komai a Kansu. Har akaje a ka dawo Waziri bai futo ba,yana shashen sa yana sak'e-sak'e mugun abu a zuciyarsa. Cikin "yan Uwan Moddibo kuwa babu wanda ya futo aka zauna dashi sai Ishak duk shauran basu fito ba, suna can suna goyan bayan mahaifinsu,Wanda har aka share makoki babu shi babu dalilinsa. Yau kwana takwas kenan da rasuwar Moddibo me Martaba yayi shirin zaman Fada, Hajiya Kulu me d'akin kudu tana kusa dashi, da yake yana shashenta, k'orafi kawai take masa na shashanci, duk wannan abunda take masa bashi ne a gabansa yana mamakin da har aka share makoki bata tab'a bud'ar baki tayi masa ta'aziyyar rasuwar Moddibo ba. Gyaran murya yayi yace" Duk wannan k'orafin naki bai karb'u ba a gurina saboda ke babbar me laifi ce,kinayi kamar baki San abunda yake faruwa ba a gidan, ke indai ba Matsalar "yayan ki bace babu matsalar da ta dame Ki, kina a matsayin matata Uwar " yayana na farko, kin tsaya kina rashin hankali, ya kamata ace kin nutsu kin San abunda kikeyi a rayuwar ki,saboda haka kar ki k'ara kawo min maganar Na'ja'atu nan saboda ban ga dalilin da zai sa kice dole in d'ebi kud'i masu nauyi har million uku in bata da sunan zata ja jari, Wanda nasan k'arya take, babu wani jari da zata ja zuwa zatayi ta b'arnatar dasu, ke da ita kuje ku sanja tuni" Ya k'arasa maganar yana k'okarin mik'ewa da niyar futa. Mik'ewa tayi itama da sauri tace"Allah ya ja zamanin Sarki, a duba maganar nan tawa, tunda kayiwa Na'ajatu aure bata tab'a zuwa tazo ta nemi alfarma a gurin ka ba sai wannan lokacin,kullum kana nuna min "yayana kamar ba kaine ka haifesu ba" Wannan magana da Hajiya Kulu ta fad'a ta d'agawa me Martaba hankali,sosai tsayawa yayi yana kallonta da ransa a b'ace yace"Kar ki

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108