Chapter 76
Chapter 76
ido tace"Kice kawai Babanmu ya wulla kawai ki sha shagalin ki" Duka Uwa! Ta kai mata suka sa dariya tamkar wasu k'awaye,Allah yasa lokacin da suke wannan zancan Lantana ta tafi siyo kalanzir d'in futalar ta. Shamsiyya ta mik'e tana fad'in bari inje in kwanta wallahi duk jikina ciwo yake yi" Ganin tayi hanyar d'akin Balaraba na da yasa gaban Uwa! Ya fad'i tace"Ashe zakuyi rigima da Walidi domin wannan d'akin da kike k'okarin shiga ya dawo nasa. Shamsiyya tayi mata wani irin kallo tana fad'in aikuwa bai isa wallahi domin bazan iya shiga cikin zarni da warin kashi in kwana a ciki ba" Uwa! Tace"Mu da muke kwana a ciki me ya cimu, kin san halin Walidi sarai ba saurara miki zai ba" Shamsiyya ta juya tana bud'e Kofa tana fad'in "Sai kiyi kuma" Uwa! Tsoran fushin Walidi take domin yanzu kusan shine yake d'aukar nauyin gidan,Saboda ita yanzu duk jarinta babu ta karar dashi gurin Arrama, da siyawa Sallau magani, Sai Mabaruka ta dawo daga yawon tallanta watarar suke cin abunci da d'an abunda ta samo. Shamsiyya na bud'e d'akin Walidi ya shigo gidan cikin sallama...... https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ ________________________ _Gaisuwar Ku daban ce, mutanan kirki, a gaskiya inajin dad'in addu'oin da kuke min Wallahi nagode sosai da sosai,Allah ya kara zumunci_ _______________________ *Takwara ta: Hajiya Binta Shitu* *Hajiya Indo Amadu* _Wannan pege d'in naku ne, kuyi yadda kuke so dashi, nice taku Binta Umar Abbale🤝🏻_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿88* Da sallama a bakinsa ya shigo gidan, ganin Shamsiyya yayi a k'ofar d'akinsa tana k'okarin bud'ewa. Da sauri ya k'arasa gurin yana fad'in "Ke mai zaki min a d'akina ne,? sai kace wacce kika bani ajiya zaki bud'e min d'aki,wai ni garin yaya akai ma na tafi na bar d'akin a bud'e? Ya k'arasa maganar tasa yana kallon Uwa! Cikin tuhuma. Diriricewa Uwa! tayi, baki na rawa tace" Yo in banda ka fad'a ma yanzu ni bansan a bud'e ka bar d'akin ba" Tsaki yaja ya juya yana kallon Shamsiyya cikin sigar rashin mutumci yace"Kinje kin gama yawon barbad'ar ki kin dawo gida zaki cigaba dai mana sace-sacen da kika fara ko" A hasale Shamsiyya ta juya kamar zata kai masa duka tace"Kayi k'arya in maka sata wallahi, Yo ina abun yake banza shashasha kawai Kai har wani kud'i ne da kai wanda za a sata d'aki duk kud'in cizo da kwarkwasa" "Kya k'araci sharrin ki dai ki matsa ki bamu guri banzaye masu mugun b'akin jini, duk sai an aurar da " yan matan unguwar nan kuna zaune a gida,saboda mugun bak'in halin ku" Tsabar bak'in ciki yasa Shamsiyya fashe da kuka tana kallon Uwa!tace"Kinajin irin cin mutuncin da yake min ko,kin ja bakin ki kinyi shiru" Uwa! Tace" Me zan ce miki ai na fad'a miki tun kafin ki tunkari k'ofar d'akin, kin san halin Walidi farin sani" Buge hannun ta yayi daga jikin k'ofar ya bud'e abunsa ya shiga yana fad'in, Balaraba dai ta huta da bala'in ku shegu sai ku k'araci bak'in cikin ku mutu" Rashin abunyi yasa Shamsiyya ta dunga k'unduma masa ashar! sai kace "yar maguzawa,yana jin ta yayi mata banza,ita kuwa sai sake fad'i take Cewar wallahi duk ranar da tayi aure Walidi yazo yace ya santa sai tasa and'aure shi, yana daga cikin d'akin yana mata dariya,domin shi yanzu d'aukar mahaukata yake musu ita da Mabaruka,ganin har yanzu sun kasa gane gaskiya, dama shi Iro ba'a sashi cikin lissafin mutane masu nagarta. Nan suka zauna har aka kira sallahar magariba mutan gidan suka fara dawo wa, Iya ta dawo daga gidan jikarta domin yanzu can take wuni saboda haihuwar da tayi,dake gidan babu nisa dasu. Ita kuma Sadiya Matar Kawu Maman, tana zuwa nany ne wata makaranta pravite tana d'aukar albashinta me tsoka, shiyasa bata da damuwa ta wanke goma ta tsoma biyar babu abunda ya dame ta. Uwa! Tayi tayi ta raba Sadiya da gurin aikinta Allah baiyi ba, ta k'ulla munafurcin da Sharrin duk Allah bai amsa ba,haka dai ta hakura amma tana bala'in jin haushin ace k'arshen wata yayi Sadiya ta shigo da kud'in ta, tayi cefane me kyau suci su sha ita da mijinta, ta zubo ko babu yawa ta kaiwa Lantana. Ita kuwa tai ya murna baki zai sauya abinci. Sai wajan goma da rabi Mabaruka ta dawo gidan hannunta nik'i-nik'e da manya-manyan ledoji, cike da fara'a ta zauna kusa da mahaifiyar tasu, wacce take ta washe baki tana k'okarin bud'e ledojin kana ganinta kasan tana cike da farin ciki yau zasuci kayan dad'i da alama Shamsiyya tayi sabon saurayi" Jin motsin Leda yayi yawa a tsakar gidan,yasa Lantana rarrafowa ta futo, domin taji sallamar Maburuka tabbas tasan ta kawo kayan dad'i, ilai kuwa tana futowa tayi arba da wata k'undumeniyar kaza gasashiya taji k'uli-kuli da tumatur da albasa,Uwa sai k'okarin kaiwa bakinta take. Lantana ta dunga washe baki tana fad'in Allah yasa banyi bacci kam,tun d'azu bacci yake so ya kwashe ni,Allah bai nufa ba" Zam tayi gefan Maburaka tana tai mata banbad'anci Mabaruka ta ciro cinya da hak'arkari ta bata, sannan ta bata robar yoghot guda d'aya, tace"Shikkenan na sallame. Ki tashi kije ki kwanta" Lantana ta mike tana. Fad'in "Ai ko baki fad'a 'yan nan, Allah ya bamu alkari" Babu wanda ya kulata a cikinsu duk suna can suna rubibin cin gasashiyar kaza me maik'o☺ Sai da suka kusa cinyewa sannan suka tuna da Sallau, Uwa! Tace"Wannan ragowar k'ashushuwan sai ku barwa babanku ki"? Shamsiyya tace"Wallahi ni har na manta ma dashi" Tab'e baki Uwa! Tayi ta mike tsaye tana niyar shiga d'akin take fad'in kin manta dashi ko na manta dashi, ummm". D'akin ta shiga,Mabaruka ta mik'e da Sauri,jiri yasa ta dafe bango sai da tayi minti biyu sannan ta d'an dawo dai-dai, cikin yanayin maye ta k'arasa bakin rijiya ta ja ruwa ta zuba a buta ta shiga band'aki. Lokacin da suka gama alfashansu da saurayin batayi wanka ba,ko da yake a cikin motarsa suka yi komai, babu gurin wanka dole sai ta dawo gida. *************** Yau sati biyu da rasuwar su Fiddausi mutuwar me Martaba kuma ta kasance sati uku,, Waziri ya saki jiki sosai kullum yana zama a fada sai dare yake tashi sosai ya jinjinawa Mak'asudu domin da yarjewarsa ya samu nasara, tun bayan mutuwar su Fiddausi Mak'asudu bai k'ara tsotsewa wani jini ba,ya bari ne k'ura ta lafa, amma yana sane da iya adadin mutanan da akai masa alk'awari. Komai yana tafiya dai-dai ta b'angaran Hajiya Kulu ita da yaranta, biyu daga cikinsu ma sun kaso auransu sun dawo gida, kullum sai su shirya su futa basa dawowa gida sai dare can,wani lokacin ma a can suke kwana. Hajiya Kulu kuwa kullum tana tare da k'awayenta "yan duniya sosai suke shek'e ayarsu Hajiya Kulu ta zama k'umgurmar " yar lesbian, sosai take jin dad'in harkar shiyasa take ganin babu wani dalili da zai sa ta tadaina more rayuwarta yanzu ta fara, k'awarta Hajiya ta Masu, itace take kawo mata "yan mata zuguda-zuguda. Sai ta biya ta kudi masu tsoka. Kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108