Skip to content

Chapter 107

Chapter 107

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

sai kice ni in zama silar shi." Kuka ya fara yi sosai harda sharb'ar majina." Yace." Meye abun kuka, kuma." Tace." Ina jin takaicin yadda wata zata fara haihuwa dakai bani ba." Tsaki yaja yana girgiza kai yace." Matsalata dake rashin wayo da dubara ni dake da balaraba babu Wanda ya Isa ya hana Allah ikonsa akanmu Balaraba zata fara haihuwa dani haka Allah ya tsara.'' Kuka sosai takeyi takasa cewa komai ta kwanta kan bed din tana Jan ajiyar zuciya, tausayinta ne ya kamashi,ya kashe futal dakin tare da aje k'aramin littafin hannunsa ya rungume ta yana fada mata daddadan kalamai, nan labari ya sha BABBAN, na futo na barsu ina fatan samun nasara da 'yaya masu albarka. To sarki! Ya biya Halisa domin dai jiya ya kashe ta da soyayyar sa mai wahalar mantawa lokaci kad'an ta manta da damuwar ta,ta cigaba da kyautatata masa. ****** Tsito ne ya dura a gidan kamar tsohon mahaukaci ya nufi b'angaran Hajiya Kulu me dakin kudu, yazo domin ya karb'i sauran kud'in aikin sa. Nan ya samu babu. Kowa a shashen nata sai hadiman ta, suka ce masa satin ta biyu bata gida,hakanan yaranta suma ba kullum suke kwana a gida ba, haka ya futo yana tunanin ina zashi,domin yanzu duk aljanun da suke kanshi sun dare sun gudu baya iya yin aikin komai watarana ma da yunwa yake kwana, ya tabbatar da cewa abunda suka aikata da Waziri ne ta shafe shi, zuciyarsa ta bashi shawarar kawai yaje ya nemi afuwar iyalin Waziri ko Allah zai sa ya gama da duniya lafiya, sannan suyi masa iso gurin Sarki! Almansur domin ya nemi gafarar sa Halin da yaga Waziri a ciki ya bashi tsoro bakinsa ya dinga rawa ya rasa abun cewa,Hajiya Kattime tace." Bawan Allah daga ina haka domin banga ne ka ba."? Tsito ya fashe da kuka yana fad'in." Yanzu haka Waziri ya koma oo ni Tsito." Kattime tace." Kayi min bayani mana, yace." Nine Tsito wanda nayi ma mijin ki aiki duk Dan yayi mulki nan ya warware mata duk abunda ya faru, yaran ta suka taso domin suyi masa duka ta hanasu, tace." Ku kyale shi shima zai ga karshen sa, nan Tsito yayi dasu su masa iso gurin me Martaba Kattime ta hana, haka suka tarkatashi suka futa dashi fadawa suka tasa keyarsa har waje, yana futa ya kasa gane hanya kawai sai ya dauki wata haya ta daban yana tafiya yana tsayawa bola-bola yana tsince-tsince duk ledar da ya gani sai ya d'auka ya sa a bakinsa yana taunawa. *Ubangiji Allah kasa muyi kyakyawan k'arshe* ******* Kwana biyu da Halisa tayi ta samu kulawa sosai a gurinsa ganin yanda ta kwantar masa da kai tana kula dashi komai sai tace idan BALARABA ta haihu za'ayi kaza da kaza, hakan ne yasa ya Sakar mata jiki suka sha soyayya. Azima ya ta karb'i girki sai girin gidishi take tasha magunguna mata kamar banza mararta sai kullewa take jira kawai take dare yayi ta shiga part din Yallab'ai a kashe boss. ***** Hajiya Kattime ce tayi sallama ta shiga a nutsue Mama ta amsa Jakadiya ta gyara mata gurin zama,sannan ta futa ta basu guri, Kattime ta gyara zama tana fadin ." Fulani magana nake tafe da ita." Mama tace." Ai tunda naga fuskar ki nasan akwai magana." Kattime tace." Wallahi kuwa, jiya na samu wani labari da bakin da ya fada min bazai k'arya kai asalima shine ya asassa al'amarin." Mama ta zuba mata ido, Kattime ta cigaba da cewa." Kin san Azima da ita aka had'a baki gurin cutar da Almansur." Mama ta mike zaune sosai tana kallon ta cikin mamaki! Kattime ta cigaba da cewa.' Jiya Tsito mashirikin da yayi aikin yazo ya warware min komai, saboda haka Nazo na fada miki auran Azima da Almansur dama da wata manufa aka had'a shi don haka ki umarce shi da ya rabu da ita tun wuri." Mama jikinta yayi sanyi sosai da sosai tace." Dama ni kaina banyi na'am da wannan hadin ba wallahi oh! Mugu bashi da kama yanzu Azima itace ta bawa yarona guba yaci domin ya nakasa."? Kattime tace." Kina mamakin wannan duniyar wallahi." Mama tace." Yanzu zan sanya ayi min kiran su ki zauna a gaban ki za'ayi komai, Jakadiya ta kira ta umarce ta ta kira mata Azima da Halisa BALARABA Wayar ta ta d'auka ta kira uban gayyar, suna tare da me girma governor suna shirye-shuiyen yanda za'a gudanar da nadin sarauta,domin an tsai da rana jama'azuwa ,Yaga kiran Mama a nutse ya d'auka tace." Kazo yanzu shashena." "Insha Allahu ganin zuwa." Ya fada yana kashe wayar. Sallama sukayi da governor suka futo tare me girma ya shiga mota tare da mutanansa shi kuma ya. Nufi shashen Maman shi tare da jama'ar sa, duk suna zaune suna jiran isowarsa yayi sallama ya shiga duk suka amsa, matansa na rige-rigen gaishe ya amsa mu a nutse ya zauna, yana gaida Maman shi tare da Hajiya Kattime, Fulani tace." Kattime yi musu bayani da bakin ki." Nan Kattime ta fara fada masa duk abunda ya faru tun daga farko har k'arshe da manufar Waziri akan auransa da Azima. Nan take Sarki! Ya tuno da ranar da ya shiga gurin Azima da daddare har yayi Tara da ita tunda lokacin nan ya tashi da wannan ciwo, Azima tayi tsuru-tsuru tuni hawaye ya soma ambaliya a fuskarta tayi da tasani yagi cikin kwando shikkenan yanzu tasan karshen zamanta dashi ya kare ganin yadda ransa yayi mugun b'aci, shiru farlo na minti biyar yayi gyaran murya yana goge gumn da ke tsatsafo masa, yace." Mama ki gafarce ni, da abunda zan aikata yanzu hak'ika zama da Azima babbar musiba ce saboda haka na sawwake mata igiya guda taje in ta samu miji tayi aure." Yana gama fadin haka ya mike ya futa zuciyarsa babu dad'i. Babu Wanda yace komai cikinsu,Azima ta dunga kuka tana rokan Mama ta sanya shi ya janye sakin Mama tayi shiru da rarrafe taje ta rike k'afafun Halisa tana rokonta Halisa ta fuzge kafarta tana maka mata harara tace." Wallahi na tsane ki Azima muguwar azzalima kawai." Cikin kuka Takarasa kusa da Balaraba tana rokonta wai tabawa Sarki hakuri Balaraba tayi shiru kawai tana Mamakin halin Dan Adam. Fadawan dake waje mama ta umarta tace su futa da Azima kuma su tsaya kanta ta had'a duk wani ko matsanta ta kama gabanta. Aikuwa haka akayi aka tasa Azima a gaba har garin su. ******** πŸ”•πŸ“£πŸ“£πŸ“£πŸ”ŠπŸ”ŠπŸ”ŠπŸ”ŠπŸ“’πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸŽΆπŸŽΆπŸŽΆπŸŽΆπŸŽΆπŸŽΆπŸŽΆπŸŽΆπŸŽΆπŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸŒ™πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ’₯πŸ§πŸΌβ€β™€πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ€΄πŸ»πŸ§πŸΌβ€β™€ *Rana bata karya* Yau juma'a uku ga watan uku, yau aka gudanar da shagalin nadin sarauta. Wannan nad'i ya samu halartar dubban mutane kama daga shugabanin kasa she,governor ni shahararun malamai da limamai da shahararun 'yan kasuwa duk sun samu damar halarta nad'in sarautar Sarki! Almansur YARO me dattako me halin manya me nagarta da sanin abunda takeyi kowa na masa fatan alkari tare da jagoranci me cikin adalci, lokacin da ake gudanar da wannan nad'i Waziri na kwance yana zurarar da hawaye duk an d'ad'e an barshi shi kadai kuka yake tukuro gami da nadamar abunda ya aikata,, labari ya riske cewar ga Almansur can an mik'a masa sandar mulki, ihu!!! Ya kurma yana buga kansa a bango nan take ya futa daga hayyacinsa

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108