Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,228 words 0 views Progress saved
Download Book

ma sabida kawai yazo ya gan ta yasa yake zuwa cin abincin ,rumfa ce da ita, sosai komai a tsare ,a kwai yaran da suke yi mata wanke wanke da goge goge,tana zaune aikin ta kawai in mutum yazo siya ,ta hada mishi duk abinda yakeso,domin babu abinda babu,wani abin ma idan ba tayi a gida,ba to a kwai mata masu girka mata anan su hada komai tsaf! In kasuwa ta tashi ta basu hakkinsu, duk wannan ,bai hanata karatu ba, yanzu haka ta kammala scondry scoohl , gashi tayi saukar Alkur'ani mai'girma, Iro yana mutukar son Balaraba, yayin da ita kuma tayi masa wata muguwar tsana,sabida halinshi,yanan bai sauya ba, Shamsiyya da Mabaruka dama sai sufi kwana da kwanaki basa magana da ita sai dai in zasu ari wani abin a hannunta kamar kayan kwalliya ko mayafi ko takalmi,wataran har kayan sawa suke ara,in zasuyi zance Ita ko Balaraba in ta basu bata kar6a in sun dawo mata dashi sai tace su riqe ta bar musu. Amma hakan baya hanasu zaginta gami da ai batata in zata fita,sana'ar ta si ta zinden ta ,suna yi mata dariya,wai zata tafi yawon iskanci ,cikin kasuwa, Balaraba bata sauraronsu sabida bata daukesu masu hankali ba daga su har uwarsu. Sallau ko tsoran ta yake ji ,kwata kwata bayason laifin ta, sabida bata masa koro in yazo maula gurinta, haka zata dauki dubu biyu ko uku ta bashi Shiyasa kullum cikin tsinewa su Shamsiyya yake. *wannan kenan* Kadan daga cikin halayen Balaraba Macace mai mutukar son girma bata son rai ni ko kadan,kuma bata son harkar qaranta,ko sitturunta babu kanana,duk manya ne ,shiyasa mutane da dama suke mata kallo mace mai girman kai da izza! sabida bata dariya ,sai ta kama kan kaga dariyar ta zaka dade,a kwai samari wadanda suka amsa sunansu a cikin unguwar amma tsoran tun karar ta suke da wani zan ce sabida kwarjin da take dashi Ko cikin kasuwar da take sana'ar ta akwai manya manya mutane da suke son ta amma sun kasa furtawa, sabida kwarjini ,sai kace mai bakin Aljani a jiki. Sai dai a gani da ido amma babu fuska, *Wannan shine jigon labarin* _in sha Allah zan cigabah bayan Allah in Allah yasa muna Raye_ *Yanzu a ka fara labarin gimbiya Balaraba* ~*Sadaukarwa*~ ~*Maraici*~ ~*Soyayya*~ ~*Bakin kishi*~ ~*Mulki*~ ~*Izza*~ ~*Takama*~ ~*Sadaukarwa*~ _DUK A CIKIN WANNAN LITTAFIN ,WATO GIMBIYA BALARABA_. *BINTA UMAR ABBALE* _MARUBUCIYAR_ *NANA KHADIJA* *YARO DA KUDI* *GIMBIYA BALARABA* 08089965176.. [13/06, 14:43] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? *GIMBIYA BALARABA* *NA* _BINTA UMAR ABBALE_ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* *25* Cikin bacin rai Balaraba ta fita daga gidan Uwa naji Mabaruka tana zaginta sabida nai man fitina amma sabida ta daure musu gindi suyi abinda suka ga dama shiyasa batace komai ba ita take kara ingiza "yar tata cewar tayi duk abinda ta gadama babu mai takura mata gidan ubanta ne Kicibus sukayi da Sallau ya dawo daga majalisarsu, sai ya tareta yana washe baki tamkar zai fadi yace"dama sai sauri nakeyi ina addu'ar Allah yasa baki fita ba" A nutse ta ke kallonshi bakinshi duk yayi gaja gaja da dattin goro jikinshi in banda warin taba da ganye babu abinda yakeyi, zuciyarta sai tashi take. Da kyar ta gai dashi ta bude jakarta sabida tasan abinda yakewa ta ciro gudar dari biyar ta mika masa Jiki na rawa ya sanya hannu ya karba yace"Allah yayi miki albarka Balaraba, ai ni kin fimin wadan can shegun "yan iska kawai Wanda ba 'acin ko kwabonsu uwarsu kawai suka sani ni mai zanyi dasu shegu "yayan asara" Mamaki da tsananin takaici ne ya kama Balaraba, jin irin zagin da yake ma "yayanshi, wai sai yaushe Kawu Sallau zai yi hankali ne.? Cikin bacin rai tace"gaskiya Kawu abinda kake ba dai-dai bane dan Allah ka daina zagin "yayanka kanai musu mugun baki, sam abinda kakeyi bai dace ba" "Rabu dasu shegu tsinannu jiya ina ganin Shamsiyya ta shi go da dubu uku ta bawa uwarta babu yanda banyi da ita ba tabani ko Dari biyu ce amma sabida batada mutumci taki, ni mai zanyi dasu" Takaici bai bar Balaraba tace komai ba kawai ta wuce tabarshi tsaye a gurin yana zage-zage da alama kwakwalrwarshi ta soma samun matsala Tun kafin ta karasa bakin titi mai Napep din dake kaita ya karaso dama tayi mamaki rashin zuwansa da wuri abinda ba ya yi sabida yasan lokacin fitarta,shiyasa itama tayi mishi uziri kila wani abin ne ya tsare shi Cikin mutumci suka gaisa dashi,ta Shiva ta zauna cikin nutsuwa Shi kuma ya dauki hanyar zuwa kasuwar sha tambaya Danja ce ta tsayar dasu dai-dai babban titin da zai sadaka da kasuwar, Balaraba ta kalli agogon dake daure a hannuta karfe goma shaura lallai yau ta makara da yawa, ranta ya baci ganin yadda masu mashina da motoci gami da motocin haya kowa yayi cirko cirko a cikin mota, kawai sai ta ziro kanta waje domin ganin abinda yake faruwa a gurin gashi danja ta sakesu amma kowa ya tsaya da abin hawarshi Motoci ta gani manya manya irin na gidan sarauta sun tawo a jere daga daga dayan titin wanda zai sadaka da gidan sarki Almustapah, wani mai sai da pure water taji yana cewa na kusa dashi "Sarki Almansor ne zai wuce shiyasa humm masu abu da abunsu" Motarshi na karasowa ya sauke glass din motar gami da ziro kanshi waje ya daga sannunshi, kan kace kabo gurin ya kaure da hayaniya wasu sai kokarin fitowa suke daga abun hawansu duk dan suyi tozali dashi, abin mamaki har da mata "yan mata da masu aure duk sun fito suna daga masa hannu Balaraba na hakimce cikin Napep din ranta in yayi dubu ya baci domin mai Napep din nata ma yayi ficewarsa, can ta hangoshi cikin jama'a sai kurdawa yakeyi wai lallai sai yaganshi Sai da motar da yake ciki ta shige sannan a kafara samun saukin cinko San da a kasamu a titin Mai Napep din ya dawo sai washe baki yakeyi ya ce "ranki shidade kowa na rubibin zuwa ya ga Sarki Almansor ke kina zaune cikin mota, yau dai nayi tozali da Sarki sarkin kyauta da karamci, Allah yaja zamanin masarautar Sarki Almusta...... "Kaga Ashiru" Balaraba ta katseshi a fusace Ta cigaba da cewa "idan ban ba danci zakayi to kaje kasameshi inda yake, dan tsabar wulakanci da rainin hankali a kan zai wuce kawai sai a dakatar da mutane, sabida ba'a damu da damuwar kowa ba, wato in mutum wani uziri mai karfi ya fito dashi shikkenan shi abin ya shafa sabida rashin imani, dubi time dan Allah munfi karfin rabin awa a tsaye a titi, sabida an rainawa mutane hankali, Mtsss dan Allah ni kai ni inda na nufa, Allah ka tsaremu da irin wannan mulki" Ta karashe maganar a zafafe! Cikin mamaki Ashiru mai Napep yaja Napep din yana satar kallonta ta cikin mirrow din din Napep din nashi, mamakin karfin halinta yakeyi da yadda take magana cikin gadara gami da takama ita ba "yar kowan kowa ba sai mugun bacin rai,a zuciyarsa yace" wallahi kika sake kika fadi wata magana akan masaurar garin nan sai kin kare rayuwarki a kurku ko kuma mutan gari suyi kuli kulin kubara dake in basu kashe ki ba ma, yana

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108