Skip to content

Chapter 62

Chapter 62

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,264 words 0 views Progress saved
Download Book

dad'i irin ta Ango da Amarya" Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta.Ya mik'e tsaye da murmushi a fuskarsa,ya kamo fuskarta ya manna mata kiss, rufe ido Balaraba tayi cikin jin kunya, fuskar ya saki, ya nufi hanyar futa yana waiwayenta, har ya bud'e kofa zai futa,ya tsaya yace"Gimbiya sai na dawo" Bud'e ido tayi da sauri tana kallon kofar futa ko rigarsa bata gani ba,ya fuce. Jiki a sanyaye ta mik'e ta nufi toilet ta dauro alwala tazo ta shimfid'a dadduma ta tada sallah kamar yadda Moddibo ya umarce ta. Sosai ta yi addu'oi tana kuka tana rokan Allah, bacci ne ya ci k'arfinta nan kan daddumar ta b'ingire bacci me nauyi ya d'auke ta,ba tare da taci komai ba,hakanan su Sadiya basu ci komai ba suma bacci ya kwashe su, Humm baccin asara kenan baccin da Balaraba bata tab'a irinsa ba, ko sallahr asubah ba tayi ba, a tak'aice dai Balaraba bata da labarin rasuwar Moddibo domin bata tashi farkawa ba sai k'arfe bakwai da kwata na safe. [08/08, 04:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` _*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_ *🅿70* Bugun k'ofar Sarki! ne ya tashe ta,ta mik'e zaune jikinta duk a mace,da k'yar ta mik'e tsaye ta nufi, K'ofa domin bud'ewa duk a tunaninta ko Moddobo ne, tayi mamakin baccin da ya kwashe ta,me cike da tarin mafarkai marasa kyau.Bud'e kofar tayi tana koma wa ciki ba tare da ta kalli me shigowa ba, shiga yayi d'akin sosai yana bin su da kallo daga ita har su Sadiya Sai da ta zauna gefen gado tana kallon sa, gabanta ne ya fad'i lokacin da suka had'a ido da Sarki! Mutum me fararan idanu taga k'wayar idonsa ta rine tayi jajazur! K'asa tayi da kanta,gabanta na dukan uku-uku! A nutse yace"Kinyi sallah" Cikin wani irin yanayi ta kalleshi tana girgiza kai. Alamun batai ba. Ajiyar zuciya ya sauke k'asa-k'asa yace" Kiyi sallama ki sauko k'asa ki same ni, ina jiran ki" Cikin k'arfin hali tace"Ina Moddibo"? Yana k'okarin futa daga d'akin yace"Yana k'asa,zaki sauko ki same shi" Futa yayi ba tare da ya saurari abunda zata ce ba. Mamaki take me ya kawo shi d'akin ina Moddibo yake?,shine ya kamata ya shigo gurin ta ba Sarki! ba,bayan haka kuma taga kamar a kwai alamun rashin nutsuwa a tattare da Sarki! Sauri-sauri tayi alwala ta futo ta tada sallah.Bayan ta idar tai addu'oi yanda ya sauwak'a ta mik'e har zata futa ta dawo tana duba su Usuman dake ta faman bacci, Ajiyar zuciya tayi ta tashi Sadiya domin tayi sallah,sai da taga Sadiya ta shiga toilet sannan ta futa daga d'akin. Yana tsaye tsakiyar falon hannunshi goye a bayansa hankalinsa na sama ita kawai yake jira ta sauko, had'a ido sukayi a karo na biyu lokacin da take saukowa dukkaninsu suka d'auke kai,sai kace wasu surukai, bai jira sun jera ba, ya kama hanya zai futa, ita kuma sai ta tsaya a tana kallon sa,yace tazo kasa ta same shi zai futa kuma ina Moddibo yake? Mutumin dake take masa baya ne yace"Allah ya kara miki lafiya, ai bayansa zaki ni, me Martaba ne yake neman ki" Jin abunda yace yasa fad'uwar gabanta ya tsananta, babu kuzari tabi bayansa, kanta a k'asa Tayi mamaki da ta dunga ganin mutane a harabar gidan kuma kowa ta kalli fuskarsa babu walwala gashi wasu daga ciki sai kallonta da k'yar dai suka isa fada, Sarki!ya tub'e takalmin sa ya shiga,ita kam tsayuwa tayi bakin Kofa sai da akai mata iso sannan,ita babban abunda ya d'aga mata hankali shine dandazon mutanan da ta gani shiya furgitata. Me Martaba ne kad'ai cikin fadar sai gawar Moddibo dake cikin makara a killace, Balaraba na sanya k'afarta ciki taci karo da makara, fad'uwa ta kusa yi saboda tsorata da tayi,bango ta dafa da hannunta miyau din bakinta ya bushe tass!tamkar ba'a tab'a hallitarsa ba,a bakinta har wani shak'ewa take, zubewa tayi bakin k'ofa, tana shashsheka,shikkenan mafarkin da tayi kan Moddibo ya tabbata babu tamtama wannan Moddibo ne cikin makara,kamar yadda ta ganshi jiya cikin baccin ta, kamar zautacciya ta k'arasa kusa da Moddibo da rarrafe,ta sanya hannu ta d'aga mayafin da aka lullub'e masa fuska dashi, Silalewa tayi ta fad'i a gurin ta suma. Da sauri Sarki!ya mik'e yaje ya janye makarar,cikin tashin hankali yake tunanin yaya zai da ita Me Martaba,ne ya mik'o masa ruwa irin na gora,ragowa ne wanda ya sha ya rage yana aje a gefe, jikinshi na kyarma!ya karb'a ya gumtsa a bakinsa ya fesa mata a fuska, ta bud'e idonta zumbur zata mik'e a gigice!Sarki!ya dafe,hannunta dake rawa,karr!-karr! muryasa bata futa sosai ya kalli mahaifin nasa yace"Allah ya taimake ka, ya kamata a futa da Moddibo domin wannan kwata-kwata babu abunda zata iya yi masa na addu'a tunda bata cikin hayyacin ta,ina ganin zan shiga da ita gida gurin Mama dole sai tasa ido a kanta zata iya futa bata sani ba" Me Martaba yace"Wannan shawarar taka itace shawara, kai ta cikin gida, idan ka shiga kai kiro min Hajiya Kattime da Mahaifiyar ka, su futo suyi bankwana da Yusufu domin za'akaishi gidansa na gaskiya" "In sha Allah" Sarki ya fad'a lokacin da yake mik'ewa yana rik'e hannun Balaraba da ta zama kamar wata zautacciya, yayi da ya sanin zuwan ta gurin, mik'ewa tayi tsaye kafafunta na rawa, sai kace me koyan tafiya,haka ta kuma komawa ta zube gurin,Suma ta k'ara yi a karo na biyu,wannan karon hankalin Sarki!ya tashi,sosai da sauri ya d'auko gorar ruwan a karo na biyu,ya gumtsa a bakinsa ya fesawa fuskarta babu alamun zata farfad'o kuma fesa mata yayi a karo na uku na shiru, mik'ewa yayi har yana kusa tuntub'e da k'afarta, hanyar futa ya nufa, cikin sauri, Shamaki na tsaye bakin k'ofar shigowa yaga futowar Sarki! da sauri yazo ya rissina Sarki! yace" Yanzu ka umarci jama'ar dake bakin hanya su matsa zan futo ya zuwa shashen Mama Fulani" Shamaki yace"Angama ranka ya dad'e" Minti uku Shamaki ya dawo yace"ranka ya dad'e zaka iya futowa" Hannu kawai ya d'aga masa ya koma ciki, Balabara dake kwance ya hau tattaro wa da niyar d'aukar ta me Martaba na kallonsa, ya ciccib'eta cikin jarumta ya nufi k'ofar futa da ita kana ganinsa kasan yana cikin tsantsar damuwa dan dai shi mutum ne me tawakkali da mik'ewa Allah lamarinsa, cikin nutsuwa yake tafiya da ita,tana hannunsa yayi mata d'aukar jarirai, duk tsayin tazarar dake tsakanin fada da b'angaran Mama Fulani,bai damu ba, shi ko ya gaji ji yake maka tamkar yarinya k'arama ya d'auka,duk da cewar Balaraba tana da girman jiki kuma bata da rama, a jikinta. Yana tafiya yana kallon fuskarta, wani irin tausayinta na ratsa masa zuciya, haka ya isa shashen mahaifiyar tashi, mutan dake gurin sam basu dame shi ba, burinsa kawai ya kai Balaraba gurin Mamanshi domin yana jin tsoron amanar Moddibo ta samu matsala, ganin shine yasa bayi dake shashen suka dunga sunkuyar da kansu har sai ya wuce sannan zasu d'ago Kansu Wani k'aramin falo ya wanda zai sada ka da babban falon Mama Fulani,nan ya tarar dasu Mama Fulani Hajiya Kattime

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108