Chapter 102
Chapter 102
ne yasa yara 'yan makaranta na addu'a jiya an sauke al'kurani babu adadi" Mama ta cigaba da cewa." Insha Allahu tanan zuwa itama,kin san bata samu damar zuwa gurin bukin ku ba tun dai da tazo lokacin mutuwar me Martaba." Balaraba tace." Kai angode sosai wallahi ai Mama alk'urani mai girma yana tattare da waraka ko wace iri ce ,mutukar mutum zai rike shi, to ya rike babban kundi." Mama tace." Haka maganar ki take Balaraba." Su Shahid ne suka k'araso gurin cikin nutsuwa suka tsuguna suna gaishe da ita, ta amsa musu da walwala a fuskarta tace." Ya mai jiki? Domin Ku zan tambaya." Shahid yace." Jiki alhamdullahi Mama kin ganshi zaune k'alau dashi,wannan kuma aikin Gimbiya ne ga tanan kusa dake." Cikin farin ciki Mama tace." Nasan zata aikata fiye da haka, k'okarin tura while chair d'in yake, da sauri Shatima yace." Kabari mana inzo." Ko saurarensa baiyi ba ya cigaba da turawa ya k'araso kusa dashi gami da kama while chair din yana fad'in"Da ka bari an turaka." "Akan me zan bari hannuna aikin me yake." Yafad'a ciki-ciki murmushi kawai Shatima yayi yana fad'in" Dama kai ai babu me iyawa da kai sai Balaraba." https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ~*NA*~ _BINTA UMAR ABBALE_ *BINTUBATULA👄* *MARUBUCIYAR* ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```TSANTSAR BUTULCI``` ```LADIDI K'WADAGA``` _*ZAMANI WRITES ASSOCIATON🤝🏻*_ _____________________ ```We are here to educate motivate and entertain aur reades``` _______________________ *JAN KUNNE⚠* _*Ban yarda a siyar min da d'aya daga cikin books d'in ba, duk mai buk'atarsu sai ya nemi numbar ta, ban yarda ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba kuma zamu tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha, ka nemi halak d'in ka yafi kaci da gumin wani, halak d'in ka shine mafi alkairi a gare ka.*_ *DEDICATED* ~*TO*~ *RAHAMA ALIYU* ~*ABUJA*~ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿114* Shiru yayi masa har suka k'arasa kusa da Mama,ya fara k'okarin saukowa Mama tace." A'a kayi zaman ka kawai mu gaisa a haka lallai jiki yayi kyau,naji dadin ganin ka cikin walwala ubangiji Allah ya k'ara lafiya." Suka amsa da "Ameen" Cikin kauna irin ta d'a da uwarsa yace." Mama kin tashi lafiya."? Tace."Lafiya lau na tashi amma na kwanta da tunanin ka, shiyasa da na shigo na ganka cikin koshin lafiya naji dad'i kuma na godewa Balaraba." Sunkyar da kai kurrum yayi yana murmushi,tace." Ina fatan ka karya ko."? Balaraba tace." Ga kayan karin can kan daining." " To maza je ki d'auko masa in ga yaci a gabana." Kallon ta yayi yace." Mama sai kace wani k'aramin yaro." Murmushi tayi tace." K'aramin Yaro kake a gurina." Shahid yace." Wallahi hakane Mama mu yara ne a gaban iyayemu, Sarki! Shiru yayi yana kallon ikon Allah Mama tasa Balaraba ta had'a tea me kauri tace."fara bashi ya d'umama cikinsa." Balaraba ta mik'a masa kofin tae sai yak'i karb'a Mama tace." Ki cika ladanki mana." Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya ta nufi bakinsa da cup d'in, a hankali ya bud'e bakinsa ya fara kurb'ar tea d'in, ji yayi sugar yayi yawa ga madara tayi yawa baya son k'arni, a hankali yace." Ki aje Wannan ki had'a min bak'i." Ajewa tayi kamar yadda yace ta fara had'a masa wani,hannu ya mik'a ya d'auki cake guda d'aya ya fara ci, sosai yayi masa dad'i a baki sai da ya cinye guda uku kafin taga ma motsa tea d'in yadda zai fi masa dad'i a baki ta fara bashi cike da kunya a idon Mama da su Shatima, Mama sam hankalin ta baya Kansu tana can tana magana da Jakadiyar ta, Su Shahid sai tsokanar sa suke yak'i tanka musu, a hankali ta dinga bashi yana kurba yana gutsirar cake d'in, sai da ya ci guda shida sannan ya d'aga mata hannu alamun ya ishe shi, tissue yake k'okarin yagowa, ta ya ciro masa mik'ewa tayi tana goge masa gefan bakinsa,ya tsura mata ido yana kallo, ita ko taki yadda su had'a ido dashi, Halisa da Azima ne suka shigo cikin wannan hali, turus sukayi ganin abunda yake faruwa kowacce jikinta yayi sanyi ga Mama a zaune ga uban tafiyar zaune cikin shiri Balaraba ta had'u sosai domin shigar ta ta yau tayi mata kyau, tana tsaye kusa dashi tana goge masa gefan bakinsa . Suka zazzauna jiki babu k'wari suna gaishe da Mama ta amsa musu a sake tana tambayar su me jiki, Azima da yake tafi Halisa wayo ta b'oye damuwar ta ta saki jiki suna hira dasu Shatima,har tana sa Balaraba a ciki kamar ba itace ta bangaje ta d'azu ba, ita ko Halisa sai shan kunu take tana hira da Mama kawai, cikin wannan hali me girma governor ya iso, suka gaisa da Mama cikin girmamawa, Halisa ta kalli Mama k'asa-k'asa tace." Mama ina gani tafiyar nan ayi ta dani domin yau girki na ne, kinga sai in kula dashi" Mama tace."aikuwa kin kawo shawara me kyau dama ya kamata a d'auki daya daga cikinku a tafi da ita, to amma kinga Balaraba bata futa daga lokacin ta ba, ina ganin da ita za'a tafi, in yaso in ya dawo sai ya sauka a dakin ki, kin gane ko"? Halisa ta b'ata fuska bata ce komai. Me girma governor yaji dadin ganin jikin shi yayi kyau, sosai ba tare da wani b'ata lokaci ba, suka mik'e domin tafiya Shahid shine yake tura shi har suka futa harabar gidan jama'a a tsatstsaye Suna sauraron futuwarsu kowa na addu'a da fatan alkairi, tare da samun lafiya. Waziri na fada zaune shi da mutanan sa labari ya riske shi cewa gashi can an futo da Sarki! Zasu tafi Saudi'a sai ya kece da dariya yana fadin "Duk inda zasuje suje su dawo shida ya taka doran kasa da k'afafunshi to sai dai idan lahira yaje" mutanan sa suka ce "Wannan haka yake,takawar ka lafiya gyara kintsi dai!!!!!! Wani mugun dad'i ya rufe shi, jin yadda suke faman zuba masa kirari,abunda yake mutuwar so kenan a rayuwarsa. Azima da Halisa, na tsaye sai gani sukayi kawai Mama ta rik'o hannun Balaraba ta zaunar da ita bayan mota kusa da Sarki! Ta maida kofa ta rufe, fad'i take." Ubangiji Allah ya bada nasara a rayuwa Yarona ka dawo da k'afafun ka.' Sarki! Yayi mamakin abunda Mama tayi,sam ba son daya daga cikinsu ta bishi saboda ya San rigima ce, yana kallon b'acin rai da zallahr kishi a idon Halisa, amma bai san manufar Mamanshi ba, Wambai da Galadima da Liman suka shiga motar su,suna dagawa Mama hannu, Shahid da Shatima motar me girma governor suka shiga, shi kuma tashi daga shi sai Balaraba sai direba, d'ayan bayan d'aya suka futa daga gidan da niyyar zuwa eirport. Addu'a sosai Mama takeyi, har suka futa, ta dawo da hankalinta Kansu Halisa kamar su d'aura hannu aka don bakin ciki, nan ta basu umarnin ko wacce ta koma shashen ta. ********** Bayan awa biyu da tafiyar su. B'angaran Waziri Zayyanu, Khalifa ne da Ansar, Suna zaune a falo suna ciye-ciye sai dariya sukeyi da alama suna jin dad'i saboda yanda Babansu ya sakar musu kudi Sosai saboda duk cikin 'yayansa yafi son su, sune zai ce suyi Abu kai tsaye suyi babu gar dama, Khalida ya kalli d'an uwansa yana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108