Skip to content

Chapter 91

Chapter 91

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

gudu tunda taga inda ya aje mukullin,, yanzu daga ita sai briz da wando, hawayen bak'in ciki take sharewa, tana tunanin yaya za tayi yanzu. Lullube jikinta tayi da bargo har fuskarta,, tana jin motsin futowar sa daga toilet d'in tayi shiru abunta har yanzu ba ta daina hawaye ba Shirya jikinsa yake yana satar kallonta ganin ta rufe fuskarta,, ko motsi ba tayi,, a tsakana ke ya shirya tsaf Cikin shigar sa ta ko da yaushe wato kayan su na sarauta, turaren shi ya fesa tas dashi kana kallon shi kasan yana cikin walwala da farin ciki,, har inda take ya k'ara ya tsaya a kanta kusan minti biyar yana nazarin ta. Duk da take lullub'e tasan da mutum a tsaye a kanta,, jikinta ne ya fara d'aukar zafi, gyaran murya yayi gami da fad'in"jimana" Banza tayi dashi ba tan ka masa ba Zama yayi kusa da ita yana Jan bargon, ta rik'e da kyau, "Wai meye haka kike ne ? Sai kace wata " yar k'auye uhumm? Ki tashi ki kimtsa jikin ki ni zan fita" K'in kula shi tayi, sai shashekar kukan ta da yaji,, yasa jikinsa yin sanyi yace"Kuka kike"? A sark'e tace"Ba dole nayi kuka ba haba wannan abun takaici duba fa yadda ka b'ata min jiki da kaya na, yanzu wane kayan zan sanya"? Fuskarta a lullub'e take maganar. Sai yanzu ya fahimci yayi kwab'a rigar ta ya d'auko yana dubawa,aikuwa duk ta b'aci,,, bai CE komai ba ya mike tsaye had'e da cire alkyabar dake jikinsa kai s.tsaye toilet ya nufa da ita, da kanshi ya bude injin wanki ya sanya rigar ya wanke mata tass ya busar da ita,, hannushi rik'e da rigar ya futo daga toilet din ya tsaya kanta yana fad'in "Tashi gashi na wanke miki" Cikin mamaki ta bud'e fuskarta tana kallon shi,, aikuwa rigar ta gani a hannushi da alama kuma a wanke take, hannu ta ziro ta karb'i rigar tana dubawa,, kallon ta yake fuskarsa babu yabo babu fallasa, ita kam mamaki take wai da kanshi ya wanke mata Riga,tarasa gane wane irin hali ne dashi,, K'asa-k'asa tace"Ka matsa daga kaina to zan sanya rigar" "Baki Isa ba" Yafad'a kai tsaye ya cigaba da cewa "Ki tashi kawai kije ki tsarkake jikin ki sannan. " Babu fa kaya. a jikina fa" Tafad'a jikin haushi. "Eh na sani" Yafad'a yana zama kusa da ita,, yana fad'in "Ko ki tashi ko nayi me gaba d'aya, babu abunda akai miki kin lanjare, ita Azima ai jaruma ce" Haushin abunda yace yasa ta mike a fusace daga ita sai k'aramin wando da briz ta nufi toilet d'in da gudu... .. Domin tana ganin ta tsaya sanya zai kalle mata jiki 😃 Ni ko nace Balaraba kenan yanzu ma ai ta kalle miki duk wayon ki Sarki! Ta fiki" Dariya yake sosai bayan shigar ta ya mike a nutse ya sauka k'asa.Lokacin da ta futo baya d'akin cikin sauri ta sanya kayan ta, ta sauka k'asa,, yana zaune kan kujera da waya a kunnen sa, da alama waya take, da sauri ta nufi k"ofar futa tun kafin ya gama wayar ya b'ullo mata da wata tsurfar,, ba zato taji yace"Jirani mana mu tafi tare zanje mu gaisa da Mama" Da sauri ta futa ba tare da taji karshen maganar tasa ba,yaya ma za'ayi ta jera dashi ga mutane da dama ai da kunya,, yanzu ma bata San abunda zata cewa Mama ba in ta koma. ******* Shamsiyya kuwa kullum tana tafe a hanyar gidan Arrama ba ta dawo wa sai dare, sai sun gama sha'aninsu kullum yana fad'a mata ta kwantar da hankalin ta, kamar ta auri Sarki ta gama ne,, Uwa yau da bakin ciki ta tashi a gidan kasancewar ko ina ta juya babu dad'i gashi bata da ko kwabo yanzu bata sai dai komai duk jarin NATA ya k'are gurin bin malamai da bokaye,, Tsarkar gida ta futo tana ta surfa bala'i ta zauna kan kujera sai durawa Lantana ashar take tana fad'in"Ban tab'a ganin tsohowar najadu ba irin wannan matar kiri-kiri ta gudu ta barni da wahalar jiyyar danta shegiya munafuka Ashe da ta karb'i asirin domin taje ta aiwatar ba abunda ya kai ta bane, to Wallahi yau sai naje na tona mata asiri a gidan,wai ni zata munafurta shigiya tsohuwar najadu" Sallau na daki yana jin Uwa na zagin mahaifiyar shi bakin ciki kamar ya kashe shi,,, cike da taikaci yace"Uwa!! Yanzu Lantana kike zagi? itama fa a matsayin mahaifiyar ki take"" Cikin masifa tace"Rufe min baki mutsiya ci kawai Uwata ko uwarka ni wannan munafukar matar bata haife ni me halin "yan wuta" Wani mugun tari ne ya sark'e Sallau yana daga hannusa guda yana son yayi magana ya kasa da k'yar yace"Uwa!ke ba matar rufin asiri bace kije na sake ki saki uku tunda kika zagi mahaifiya ta" "Ahayye nanaye"!!! Ayurrrrrr" Yau Allah ya raba ni da k'aya mutan gida Ku futo Ku taya ni murna" Sadiya da Iya duk suna jin abunda ya faru sukayi shiru suna mamakin abunda dama ya kai Lantana gidan sarauta duk Dan ta cutar da Balaraba ne, Allah yasa Allah ya tona mata asiri.. Iya bata tsinke da al'amarin ba sai da taji Sallau na fad'in ya saki Uwa saki uku sannan ta futo daga daki tana salati gami da fad'in "Assha Sallau ka yanke hukuncin da bai dace ba, Sallau ba a saki cikin fushi" Sallau ya fashe da kuka yana fad'in "Dole In rabu da Wannan bak'ar dagar matar Atika kina ji fa tana zagin Lantana duk lalacewar ta mahaifiyar ta CE kuma itama ta haife ta tunda dai yar uwarta ce" Iya tace"Duk da haka dai, hukuncin da ka yanke bai dace ba" Uwa! Ta futo daga daki Cikin shiri tana fad'in "Duk naji abunda kake cewa munafuki me kashi a kwance akwai bak'ar daga irin uwarka me muguwar zuciya kawai wallahi yau sai na tona mata asiri a gidan Sarki yanda ka ganni nan a shirye nake" Waje ta futa kamar sabuwar mahaukaciya sai surutai take, Iya da Sadiya suka bita da kallo cikin mamaki. Tana futa Sallau ya dunga wani irin tari Wanda I n yayi sai wata majina ne kauri bak'ak'irin ta futo daga bakin sa, ga wani uban wari da take,, DA k'yar ya bud'e bakin sa yace"Atika ki yafe mun abubuwan da nayi muku ke da "yan uwanki Wanda na sani da Wanda ban sani ba ki yafe min Wannan ciwon nawa bana tashi bane, hak'ika na aikata abubwa Mara kyau don Allah ki nema min gafara gurin Balaraba da duk Wanda na batawa jikina na bani mutuwa zanyi" Iya ta fara share hawaye tana cewa"cuta ba mutawa ba Sallau Insha Allahu zaka tashi kayi hakuri ka daina wannan maganar" Sallau yace"Kayya Atika ni nasan abunda nake ji hak'ika na zalinci Ayuba da matar shi da yarsu Balaraba don Allah ko na mutu Ku Bini da addu'a" Kuka iya take tana bashi hakuri gami da yi masa addu'a ta kalli Sadiya dake tsaye hawaye na zuba tace"Ki kira Maman a waya yazo su gana" Cikin dauriya tace"Kin manta "yau kwanan shi biyu da tafiya sun tafi Jalingo,zasu sauke kaya" Iya tace"Hakane kuma kira Walidi yazo ya kai shi asibiti jikin

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108