Chapter 81
Chapter 81
sauke wata irin zazzafar ajiyar zuciya, kwata-kwata a "yan kwana kin nan, yana yawan jinta a cikin zuciyarsa, duk sanda ya tuna da cewar tayi mu'amula da maza ta shiga cikin kasuwa ta saida abunci,sai yaji wata irin kibiyar kishi ta soke, ranar sai ya yini yana kwance duk ransa a b'ace! Yana kishinta sosai da sosai. Kasa daurewa yayi yasa yayi mata maganar. *********** *********** *********** Lantana na bayan mota duk tayi tsuru-tsuru sai zare ido take, burinta kawai ta isa gidan ta ganta gata ga Balaraba sai ta fara gudanar da aikinta. 👸🏻👸🏻👸🏻 _*GIMBIYA BALARABA*_ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* ```MARUBUCIYAR``` *NANA KHADIJA* *YARO DA KUD'I* *GIMBIYA BALARABA* *TSANTSAR BUTULCI* _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ _________________________ ```We are here to educate, motivate and entertain aur Reades``` _________________________ _*DEDIGATED*_ _*TO*_ _RAHAMA ALIYU_ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*_ *🅿93* Kai tsaye shashen Mama Fulani suka nufa,, bayan Buba yayi parking d'in mota suka futo cikin nutsuwa, Buba ya bud'ewa Lantana k'ofa ta futo daga cikin motar sai zare ido takeyi ganin wasu irin mutane manya-manya a shashen Mama Suna kaiwa suna kawowa kuwanne jikinsa sanye da kaya jajaye da k'aton ta wani, gefanta ya kalla taga wani tsaye hannusa rik'e da k'atuwar bulala sai zare ido yake ga idanunsa sunji kwalli rabad'au, saurin d'auke kanta tayi tana k'ara damke abunda yake hannunta. Ganin suna ta zubewa k'asa suna gaidasu Shatima ne yasa ta shiga taitayinta, ta dunga bunsu a baya simi-simi har suka shiga falon a tare. Lantana ta tsorata da ganin irin had'uwar falon Mama Fulani ko ina ta kalla sai taga kalarshi daban, ga kayan alatu na jin dad'i da more ta yuwa, wani irin mugun kamshi me dad'i yana shiga hancin ta. Tun daga bakin Kofa ta zube tana gaida Mama. Cikin mamaki Mama Fulani tace"Bisimilah mana ki shigo daga ciki sai mu gaisa sosai" Da k'yar Lantana ta mike ta isa kusa da Mama Fulani ta zauna a k'asa sai washe baki take. Tana fad'in "Ranki shi Dade ashe ina da rabon ganin ki a duniyar nan, ashe jinina zai had'u da jininku,gaskiya nagode Allah nagode Muhammadu rasililahi" Mama tayi murmushi kawai tana kallonsu Shahid nan yayi mata bayanin Lantana Cike da farin ciki ta kalli Lantana tana fad'in "Gaskiya naji dad'in zuwanki sosai,dama nace aje a sanar daku halin da ake ciki,Gobe insha Allahu bayan d'aurin aure zan tura a d'auko sauran mutanan gida suma suzo ayi hidimar buki dasu" "Lantana tace" Ai naji dad'in wannan abu ranki ya Dade nace Ashe da rabonmu muma zamuci arziki mu bar shi inda yake, haihuwa tayi mana rana" Murmushi Mama tayi batace komai ba. Su Shahid suka mike. Inda Shatima yake tambayar Sarki! Mama tace"Ya koma Shashen sa. Sallama sukai mata suka wuce Shashen Sarki! Lantana ta dunga b'arin jiki sai zuba take tanaiwa Mama labari,tace"Ina angon namu yake ne yazo ya zab'a ko ni ko ita" Mama bata iya surutu ba saboda ba d'abi'arta b'ace,gashi bata San wulakanta mutum sai ta dunga biyewa Lantana kawai domin karrama ta. Jakadiya Shafa'atu ta shigo suka gaisa da Lantana, nan Mama take sanar da ita cewar kakar Balaraba CE,Jakadiya ta kara gaida Lantana cikin girmamawa, Mama tace, taje ta kira Balaraba dasu Sadiya su gaisa da kakarsu sannan Balaraba ta bata abunci, Sadiya da Usuman ne a gaba kafun Balaraba, da sauri suka ja tunga suka tsaya ganin Lantana a gurfane gaban Mama sai surutu take sai kace wata tsuhuwar redio, Sadiya ta juya da sauri zata koma suka ci karo da Balaraba tayi saurib tare ta tana tambayar ta menene"? Bakinta na rawa tace"Yayarmu Lantance" Da sauri ta kalli inda Sadiyar take nuna mata, Lantana ce, kuwa hankalinta na kan Mama basu ga futowar su ba, fad'uwar gaba taji, tana mamakin me ya kawo Lantana gidanan,, wata zuciyar tace mata kika sani ko Mama ce tasa aka d'auko ta. Da kuzari a jikinta ta nufi inda suke, Binta sukayi a baya suna cike da tsoran abunda zai faru Usuman addu'a kawai yake a cikin zuciyarsa Allah yasa Lantana kar ta gudu dasu shikam yaji dad'in zaman gidan nan. Lantana na hango Balaraba ta mike da sauri zaninta ya fad'i ta d'auka da sauri ta d'aura taje ta rungume Balaraba ta fashe da kuka tana fad'in "Ashe kina nan Balaraba, munyi neman duniya bamu ganki ba,Shima Sallau da k'yar ya koma gida ranar ashe alkairi ne a tartare dake Balaraba" Wasu irin sambatu Lanatana ta dunga yi Mamaki ya kama Balaraba sai ta rik'e ta ta zaunar da ita tana fad'in ki zauna mana, don Allah ki nutsu sosai sai muyi maganar. Ita dai Mama tana kallonsu cike da mamaki Jiki narawa ta zauna tana hawo hannun Usuman yana fuzgewa yana komawa bayan Balaraba, Tace"Zo nan Sadiya mu gaisa" k'in zuwa tayi yarinyar. Fashewa da kuka Lantana tayi cike da munafurci da kitifi tace"kinga abunda nake fad'a miki ko Balaraba, dubi wai jina ne yake guduna duniya kenan" Balaraba na jinta tasan dai makircin Lantana,, tace"Ki nutsu nu gaisa mana" Jikinta na rawa ta hau gaida Balaraba, amsawa tayi kawai tana kunshe dariyarta ita Abunda Lantana take ya soma bata mamaki wallahi. Mama kanta ta fuskanci rashin gaskiya gurin Lantana. Da k"yar ta hillace ta suka nufi gurin cin abunci Lantana taka tunga ta tsayawa wai baza ta hau kan daining ba, haka ta had'a mata ta kai ta aje mata can wani k'ebabtaccan gurin Cin abunci take kamar wata jaka babu kamun Kai babu komai, Mama Fulani na daga gurin zaman ta tana kallon ikon Allah, Balaraba kuwa wata irin kunya ce ta kamata, a hankali tace "Lantana kici a nutse mana" Ko saurarenta batayi ba,sai da ts cika Uwar hanjinta da kyau sannan ta tsame hannuta tana goge bakinta,,, Mik'ewa tayi ta koma falo kusa da Mama Fulani,,Tsaki Balaraba taja tana d'auke kanta,tanajin Lantana tana cewa Mama wai tana so ko bayan biki ta zata zauna anan" Mama Fulani tace"Ai babu komai sai ta zauna d'in. Mama Fulani dai shiru tayi musu ita da Jakadiya suke hira itama da tagaji sai tao shiru ta k'yaleta,, sai banbadanci takewa Fulani. Mintu ashiri Mama ta kara a gurin ta mike tsaye tana musu sallama domin zataje ta kwanta, nan sukai mata sai da safe, ta shige d'akinta, Jakadiya ma sallama tayiwa Lantana ta mike ta nufi dakin kwananta. Balaraba ta kalli Lantana da rai a b'ace tace" Ai sai ki tashi haka muje ki kwanta, wai don Allah meyasa kike haka ne"? Lantana ta hau yak'e tana fad'in "Me na aikata " yar nan, baki San su irin wannan mutane dole sai kana musu banbad'anci ba" Tsaki taja tana fad'in "To banda wannan masarautar ta masu hankali ce,don Allah ki dunga nutsuwa kar ki bani kunya gurin abokan zamana da mutanan gida" Lantana tace"To naji zan kiyaye ai kina da damar da zaki fad'a min duk irin maganar da kike so, saboda Kinga zaki auri Sarki! "Shiru kawai tayi mata tana surutai a cikin zuciyarta take fad'in ko wannan auren ya dama,ni a gurina sunan shi auran biyayya. *********** *********** *********** *Komai yayi farko yana da k'arshe* Cikin shiri sosai suka futo daga shashinsa gida ya cika ya tumbatsa baka jin komai sai busa da sarewa irin ta gidan sarauta, marok'a da magogo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108