Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,242 words 0 views Progress saved
Download Book

sauka lafiya" Tafada gami da latsa wayar hannuta, Har ya wuce ya dawo fuskarsa a sake yace"yau baki da sako gurin Mama kilishi"? Murmushi ne ya subuce mata bata shirya ba,tun sanda ta ga hotan matar a wayarshi taji tana mutukar kaunarta,sosai shiyasa duk lokacin ya zo cin abinci take hada mashi waina(masa) sabida ya fada Mama tanason wainar shinkafa, shiyasa kullum take hada masa da yawa ya kai mata,Mama kilishi har tasan da zaman Gimbiya Balaraba, [18/06/2019 3:02 PM] Binta Umar Abbale: Mikewa tayi a nutse ya bita da wani mayataccan kallo,duk tana kallonshi, kawai sai taja ta tsaya gami da cewa"kayi gaba ganinan zan kawo maka sakon har gurin da ka aje motarka" "Menene hujjarki ta fadar haka,? Kina nufin in wuce gaba ke kya biyo ni daga baya, ban yadda ba"? Yafada gami da bin ta da wank kallo mai dauke da so da kauna Gaba tayi kawai bata saurare shi ba sabida ta riga ta San mugun nacin sa Bayanta ya bi yana kare mata kallo ji yakeyi in bai auri yarinyar rayuwarshi zata shiga garari, Hauwa tasa ta hada mata komai cikin wani take away na mussaman an nan nadeshi da wata Leda mai kyalli a sanya leda mai zurfi, ta fito rike da ledar a hannunta,ta mika masa, "gashi a kai mata ace ina gaidata da kyau" Cikin murumushi ya karbi ledar har yana kokarin hadawa da hannuta tayi saurin zare hannunta ledar ta kusa faduwa kasa, sai harararshi take Basarwa yayi yace"zataji insha'Allahu, kizo ki rakani gurin motana" Share shi tayi ta kawai ta koma gurin zamanta, ta zauna gami da dora kafa daya kan daya, babu abinda ya dameta. Girgiza kai kawai yayi ya wuce,ya na mamakin izza da mulki na yarinyar ya lura abin a jikinta yake,ko shi da yake dan saurata ba ya yin irin abinda take,asalima sam bayaso a san cewa yana da alaqa da masarautar garin, sai dai dayawa daga cikin abokanshi in sun ganshi cikin kasuwar sai su riqa mamakin mai yakawoshi har dai suka fahimci gurin Balaraba yake zuwa, to babu irin maganar da ba'a fada masa ba a kan Balarabar amma yayi kunnan uwar shegu da jama'a sabida shiyasan wacece Balaraba a cikin zuciyarsa. *๐Ÿ–‹YANZU MUKA FARA* [20/06, 05:57] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation [6/19, 12:18] Binta Umar Abbale: [๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป _*GIMBIYA BALARABA*_ ๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป *NA* _ยฎBINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYA* ```Nana Khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani writes Association๐Ÿค๐Ÿป BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM ๐Ÿ…ฟ28 _______ Biyar saura Ashiru mai Napep ya zo daukarta dama lokacin suke tashi sai da tabbatar su Hauwa sun tsaftace mata gurin komai an wanke an ajeshi in da ya dace sannan ta bawa ko wacce hakkinta sukayi sallama cikin mutumci, Ashiru ya dauketa suka bar kasuwa mutane sai zindanta sukeyi mussaman wadanda suka kawo mata maganar banza a kasuwar ta ci musu mutumci,shiyasa sam basa iyayin munafurce-munafurcensu a gaban idanta sai sun ga bata guri [6/19, 20:48] Binta Umar Abbale: Abin mamaki suna zuwa dai-dai danja kamar dazu suka tadda uban gosolow gashi yamma tayi duk "yan kasuwa kowa yana kokarin komawa gida, amma an dakatar da jama'a , cikin mamaki Balaraba tace " wai me yake faruwa ne? kallonta yayi ta cikin mudubin Napep din yana shakkar abinda zai fada mata,yace "ai Sarki Almansor ne ya dawo, ashe sun je daurin aure can gwarzo, maimarta bai samu damar halarta ba sai ya wakiltashi dashi da mai girma waziri Rayyanu" Tsaki taja tace"Allah ya kyauta, gaskiya an shiga hakkin jama'a dayawa wallahi, daga zai wuce sai a dakatar da jama'a sabida takama da sarauta,sam wannan bazai iya mulkin garin nan ba" ta karashe maganar tana tabe baki "yar dariya Ashiru yayi yana satar kallonta gefe guda kuma yana jin tsoran maganar da zai fada mata, amma sai ya dake yace" nura Gimbiya sam Sarki Almansor baya burgeki,kuma baki fahimce shi bane mutum ne shi mai sauqin kai gami da iya mu amula da jama'a yana da tausayin nakasa dashi sosai, matsalarshi kawai muskilanci shiyasa mutane suke masa kallon mutum mai girman kai da izza" shiru tayi masa batace komai ba, sabida ta lura da Ashiru yayi nisa da kaunar Sarki! wayarta tafito da ita tana dubawa ranta a bace, ta najin yadda motoci suke gudu kan titi dago kanta tayi tana ya muste fuska, cikin rashin dace idanunsu suka hadu dana juna, cikin sakon daya ya gane ko wacece,sai yayi saurin kauda kanshi gami da gyara kwanciya cikin motar tabe baki tayi ta kauda kanta,ko daga bacci ta tashi zata iya ganeshi sabida ranar saukarsu ta kare masa kallo, shiyasa in taga ana rububin ganinshi sai tai ta jin haushi sabida ita sam bata ganin kyawunshi da mutane suke zuzutawa bayan motarshi ta wuce sauran motocin suka dinga wucewa a jere har suka kare,sai sannan a kabawa jama'a damar wucewa, Agogon dake daure a hannunta ta kalla biyar da rabi sun samu kosan rabin awa a tsaye a titi, giriza kai kawai tayi a zuciyarta tace idan tasan wannan bacin ran zata samu da babu abinda zai kaita fitowa wallahi Sabida haka ana tsaka da kiran sallahr magariba ta karaso gida, tun daga nesa ta hango Shamsiyya na suyar doya da kwai matasan unguwar duk sun kewayeta tana karasowa gurin warin taba ya sata saurin toshe hanci tana kauda kai, da kyar ta samu ta ratsa ta tsakiyarsu tana kokarin shiga gida, Iro ne ya tare mata hanya yana wani washe baki yace"Kanwata kin dawo kenan? Sama-sama ta kalleshi tana kokarin wucewa tace"e wallahi" ganin tana kokarin wucewa tabarsha a gurin yasa ya kira sunanta, tsayawa tayi tana kallonshi yace"tuntuni nake so muyi wata mahimiyar magana dake dama" sabida sanin da tayiwa Iro da kafirin nacin tsiya yasa tace masa"yanzu dai lokacin sallah ne kaga isha'i ta kusa yi gashi banyi magariba ba kabari sai anjima sai muyi maganar ko"? Washe baki yayi wasu jajayen hakora suka bayyana Balaraba tayi saurin dauke kanta zuciyarta ta wani mugun tashi,lallai Iro ya bata rayuwarsa yace"babu damuwa ai zamu hadu anjima,yau bazan fiya yawon dare ba, watakila ma a gida zan kwana" ko saurarsa batayi ba tayi saurin shigewa cikin gidan sabida yadda taji zuciyarta tana tashi warin tabar wiwi da ganye duk sun cika soran gidan. *Muje zuwa* [21/06, 18:40] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป โˆ†โˆ†โˆ†โˆ†โˆ†โˆ† _*GIMBIYA BALARABA*_ โˆ†โˆ†โˆ†โˆ†โˆ†โˆ† ๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป๐Ÿ‘ธ๐Ÿป _*Na*_ _ยฎBINTA UMAR ABBALE_ *MARUBUCIYAR* ```Nana khadija``` ```Yaro da kudi``` ```Gimbiya Balaraba``` Zamani Writes Association๐Ÿค๐Ÿป ```Bisimillahir rahamanir rahim``` *๐Ÿ…ฟ29* ______ "Salamu alaikum" Balaraba tayi sallama cikin gidan nasu, babu wanda ya amsa mata,duk da cewa dukkaninsu suna zaune a tsakar gidan, har Lantana ma domin ita ma bata dade da dawo wa daga yawon tallata ba, tana zaune ta mike kafa kan tabarma tana lissafa kudin cinikinta, ita kuma Uwa na gaban murhu tana soya a wara dake bayan tayi ta safe wacce Mabaruka take dauka to da yamma ma sai ta kara dora kasko, bata tashi sai wajan karfe goma na dare, ita kuma Shamsiyya a waje take soya doya da kwai, Iya ce ta fito daga ban daki hannuta rike da buta ta tace"Balaraba kin dawo kenan" Tana kokarin bude kofar dakinsu tace"e wallahi Iya, ya gida"? "Lafiya kalau ai tun dazu nake cewa shiru baki shigo ba gashi ba kya kawai magariba" "Wallahi kuwa lokacin da

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108