Skip to content

Chapter 58

Chapter 58

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,272 words 0 views Progress saved
Download Book

ba" " Ai in itace ma,kanta ta kai domin a gaban me Martaba zan zayyane masa abubuwan da take na fajirci" Lantana tace"Kayi min dai-dai kar ka rage komai duk ka fad'a masa zinace-zinacen da takeyi" Haka Sallau ya futa Lantana tana k'ara yi masa hud'uba. Lokacin da suka isa fadar Sarki Almustafa a cike take, me Martaba yana sauraron k'urafe-k'urafen mutanan sa, sai da fada tayi sauk'i sannan me Martaba ya waiwayo kansu, suka k'ara mik'a gaisuwa, Sallau duk ya sare! da al'amarin ganin yadda me Martaba yake yanke hukunci cikin adalci a bawa me gaskiya,gaskiyar sa, mara gaskiya a bashi rashin gaskiyar sa,sai gumi! yake sharcewa, Cikin nutsuwa me Martaba, ya d'ora idonsa a kan me gari, Halilu, yace"Halilu ya al'amura da fama da jama'a"? Me gari Halilu yace"Alhamdulilahi Allah ya taimake ka" "Masha Allahu" me Martaba ya fad'a yace"kasan wancan yaron"? Sallau da Me gari Halilu su ka kalli inda me Martaba yake nuna was, Walidi ne zaune cikin dugayen kaya kamar bashi ba,sai Moddibo dake gefan sa,a zaune, Cike da furgici Sallau yace"Walidi me ya kawo ka nan"? Wani dogari ya buga matsa tsawa,gami da cewa"gyara kintsi!! nan ba gurin shirme bane" Shiru fada tayi,na minti biyar me Martaba ya kalli me gari Halilu a karo na biyu yace"ina sauraron ka" Sunkuyar da kai k'asa me gari yayi yace"k'warai kuwa Allah yaja zamanin ka,nasan wancan yaron farin sani domin yana d'aya daga cikin matasan gari na, yanzu haka ma muna tare da mahaifin sa,Allah ya taimake ka" Ya k'arashe maganar yana sunkyar da kansa cikin ladabi, "Alhamdulilahi" me Martaba ya fad'a ya cigaba da cewa, " yaron nan yazo min da magana wacce naji bata kwanta min ba,wato kuna so ku had'a aure babu sanin kowa,hatta yarinyar da kuke so kuywa aure bata sani ba,kuma bata amunce ba, shine nasa aka kira ku inji kan wane dalili zakuyi haka"? Sallau yayi karaf! yace"Allah ya taimake ka wannan yarinyar da kake magana a kanta nine mahaifinta,saboda nine wan ubanta,nafi kowa sanin halinta muguwar karuwa ce,yawo take tana bin maza,ga shaye-shaye,kwanaki ma har ciki ta zubar,shine ni kuma nake tsoron kar Allah ya tambaye ni amanar da ya bani yasa kawai nace gwara inyi mata aure in huta, to sai a kayi sa'a kuma d'an uwanta wato yaron gurina Iro yace yana sonta zai aureta a haka duk da mugun halin nata, nayi murna da naji haka,shine banyi k'asa a gwiwa ba,naje na siyo alawa da goro, na kai gidan me gari domin a d'aura auran bata sani ba, Allah ya taimake ka yanzu zan can da nake maka ma, tunda ta samu labari,mun nemata mun rasa tunjiya bata kwana a gida" Fada tayi shiru tana sauraron maganganun da Sallau yake, kowa yana jiran abunda me Martaba zai ce" A nutse ya d'ora idonsa kan Walidi,yace"kaji abunda mahaifin ka yace a kan "yar uwarka" Walidi ya gyara zama sosai yace"Allah ya baka nasara,a rayuwarka, duk abunda ma haifina ya fad'a ba gaskiya bane, gaskiyar magana Balaraba kintstsiyar yarinya ce me gurin zuciya, nan dai Walidi duk ya fayyacewa me Martaba abunda yake faruwa, ya cigaba da cewa,maganar cewar Balaraba ta gudu, an neme ta an rasa, hakane, Allah ya taimake ka,Balaraba ta hannun Moddibo, shine ya taimake ta ita da "yan uwanta guda biyu" Kallo ya koma kan Yusuf Moddibo musamman Mahaifin sa Waziri Zaiyyanu Me Martaba yace"hakane Moddibo"? A nutse yace"k'warai kuwa Allah ya taimake ka,yarinyar tana hannuna kuma ina me farin cikin sanar dakai cewar itace yarinyar da na fad'a maka inaso in aura" Cikin mamaki me Martaba yace"jeka d'auko min yarinyar,ka kawo min ita,yanzu zan sa a kira min d'an uwanka,Almansur,domin shi nasa yayi min bunkice a kanta,shi kuma muji ta bakinsa" A nutse Moddibo ya mik'e ya na kai gaisuwa, ya futa daga fadar, Sallau kuwa duk rigar jikinsa ta jik'e jagab! ganin reshe yana nema ya juye da mu jiya, babban abunda ya d'aga masa hankali shine ,jin da yayi wai Balaraba na gidanan,kuma wai wannan da yayi maganar shike san ta da aure ,lallai asirinsu ya tuno. [03/08, 19:52] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` _BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM_ *🅿66* Jakada me Martaba ya bawa umarnin kiran Sarki! ba tare da b'ata lokaci ba,ya tafi shiru fada tayi tamkar babu mutane a ciki, Sallau sai zufa yake sharcewa duk ya rasa yanda zai yi sai gyara hula yake, yana kalle-kalle a tsorace! Lokacin da Moddibo yaje wa da Balaraba zan can halin da ake ciki,ta tsorata sosai da taji cewar me Martaba ne da kansa yake neman ta, jikinta yayi sanyi domin bata san abunda zai je ya dawo ba,tunda yace mata Sallau yana gurin,nan dai Moddibo ya rarrashe ta da ta kwantar da hankalinta insha Allahu k'arshen matsalarsu tazo,haka suka futo tare,da Sadiya da Usuman Balaraba na sanye da dogun hijabi har k'asa, Yana zaune a inda yake ya hangi sakkowar su daga matattakalar bene, sai yayi sauri d'auke kansa yana jin wani abu a zuciyarsa, dake namiji ne me jarumta kwata-kwata fuskarsa bata nuna ba, Tsayuwa yayi kusa dashi suna magana, ita kuma taja hannun su Sadiya sukayi gaba, Bud'e k'ofa tayi suka kusa cin karo da Mariya wato baiwar shi, ta shigo kai a k'asa ta k'arasa inda yake zaune ta zube gwiwa biyu tana gaishe su,sannan tace" Ranka ya dad'e Jakada na waje yana neman iso" D'aga kai yayi kawai Mik'ewa tayi ta futa da sauri, ko minti biyu ba ai ba Jakada ya shigi, cikin sallama, ya kwashi gaisuwa sannan ya fad'i sak'on me Martaba. A nutse yace" A ce masa gani nan zuwa yanzu in sha Allah" Mik'ewa Jakada yayi yace "A futo lafiya ranka ya dad'e" Moddibo yace" Nafad'a maka kak'i yarda yanzu dai gashi kaji daga bakinsa ko" A nutse ya mik'e tsaya ya d'an ya mutse fuskar sa kad'an yace"muje" Moddibo ne ya bud'e k'ofar suka futa tare,Balaraba na tsaye a wani guri ta hangi futowar su, saurin dauke kanta tayi ganin yadda kyawun Sarki! ya dusashe na Moddibo,wani in rana ta daki fuskarsa yana muuni!sai taga shi wannan wani k'yalli da annuri fuskarsa take, tafiya yake cikin kasaita, tana kallon bakinsa daga inda take yana motsi da alama magana suke da Moddibo, ta lura tunda ya futo bayin da suke gurin suka bar abunda suke suna gaishe shi, Ganin sun kusa zuwa inda take ne yasa tayi saurin kauda kanta,ta gyara yanayin fuskarta sosai gudun kar ya kawo wargi. Moddibo yace"Yi hakuri Gimbiya kina tsaye kina jiranmu ko" Murmushi tayi kawai ta basar, Sarki! kuwa wucewa yayi ya barsu a gurin, sai suka biyo bayansa. Bayan sun dai-dai ta zamansu gaban me Martaba, ya kalli Balaraba sosai yana nazarin ta,a idonsa yake ganin kamar yasan fuskar, gyara murya yayi kalli Sallau da ya diririce a gurin duk alamun rashin gaskiya sun bayyana,a tare dashi,yace"Wannan itace yarinyar da kake magana akanta"? Sallau ya d'aga kai cikin tsaguwa Sam yaki kallon gefen da Balaraba take, lokacin k'ankani me Martaba ya fahimci Sallau bashi da gaskiya,girgiza kai kawai yayi ya mayar da idonsa kan Sarki!

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108