Chapter 105
Chapter 105
aka bawa umarni ta mike Zumbur! Kofar dakin taje tana murza wa, abun mamaki kofar ta bude, bata tsaya tunanin komai ba ta afka cikin dakin, abunda ta gani yayi mutukar gigita mata tunani,nan take sai kanta ya fara juyawa ta zube a gurin a sume.! ******* Tsaf! Ta shirya shi cikin wani parkinstan irin na maza sunyi masa kyau sosai kanshi sanye da hula irin ta Larabawa tsaf idan ya shiga cikinsu zai saje, turare ta d'auko tana fesa masa, ya rike hannunta yana murzawa, murmushi tayi tace." Ka bari in fesa maka fa kar Ku makara gasu Shatima na jiran ka." A kasalance yace." Kece duk kin gajiyar dani jikina duk ciwo yake." Hararsa tayi kad'an tace." Kana da Neman magana ko." Murmushi yayi tare da lakuce mata hanci yace." Gaskiya ne ai." While chair d'in ta kama tana k'okarin tura shi domin ta futa dashi farlo, yace." Bari ki gani da izinin Allah yanzu zan taka k'afafuna." Balaraba ta matsa gefe tana kallon ikon Allah, ya yunkura bakinsa d'auke da Addu'a sai gashi tsaye da kafafunsa, cikin mutukar farin ciki ta furta "Alhamdullahi ala kullu halin." Shima cikin farin ciki yace." Allah ne abun godiya." K'okarin futa take yi ya rike hannunta da sauri yana fad'in " INA zakije kece 'yar jagora ta fa." Cike da farin ciki tace." Wallahi duk na rasa ya zanyi saboda farin ciki,hak'ika ubangiji naji rokan bawansa ne." Yace." Hakane mutukar bawa zai mik'a lamarin shi ga ubangijinsa to babu shakka dukanin Matsalar sa ta kare." Rungume shi tayi sosai tana sauke ajiyar zuciya, cire ta yayi daga jikinsa yana Dan murmushi yace." In kika karya min alwala fa , zamuje massalaci yanzu in mun dawo kiyi min tanadi me kyau." Ta sinne kanta kafadar shi suka futa a haka Su Shahid na zaune suna jiran futowar sa,kawai suka ganshi ya futo da k'afafun sa,tare suka mike tsaye cikin mamaki ! Shatima yace." Alhmdullahi Alhmdullahi ala kulli halin, yaushe ka mike ka fara tafiya." Suka fada a tare. Balaraba tace." Yanzu ne kamar da wasa wallahi ya mike." Shahid ya zube gurin yana sujjadar godiya ga Allah,shiko Shatima waya ya futo da ita zai kira mutan gida, Yace." Ka bari tukkuna muje mu dawo ko meye sai ya biyo baya in ka kira mutane yanzu zasu hana mu ibada." Shahid yace." Hakane bari muje mu dawo kawai, tare suka futa har da Balaraba tana sanye da dogun hijabinta fari tass dashi mijinta ya rike mata hannu suka fara tayi,dake gidan da suke bashi da nisa da harami da kafa suka tafi, Bayan an idar da sallahr jama'a suka zauna massalaci suna add'a tare da karatun alkur'ani me girma. ********** Waziri Zayyanu kuwa yana futa fadawansa suka rufa masa baya tare da kareshi da lema saboda rana sai baza babbar riga sukeyi, kamar daga sama yaji wani irin ihu!! A kunnensa ,zabura! Yayi yana kalle-kalle, wani ihun yaji Wanda yafi na d'azu, can yaji gurnanin Mak'asudu sama-sama yaji muryar shi yana fad'in "Aiki ya lalaceee!!!!! Ka janyo min ka janyowa kanka, ihuuuuuuuu!! Shikadai yake jin wannan ihu,ya tsaya yana dira-dira Wani bafade yace." Gyara kimtsi daiiii!!! Allah yaja zamaninka ko kayi mantuwa ne." Waziri ya girgiza masa kai a mutukar tsorace!! Yake, tuni jikinsa ya fara tsiyayar da gumi! Ya juya zai goma gida, k'afafun sa suka sark'e suka lauye suka kwalmad'e ba tare da bata lokaci ba ya zube a gurin, yanda k'afafun sa sukayi haka hannuwan sa sukayi, bakinsa ya kar kace idonsa ya wurkile, hallitunsa suka sauya gaba ki daya. Fadawansa suka saka salati tare da d'aukar sa domin kai shi cikin gida. Ko da suka shiga dashi cikin gidan suka tarar da tashin hankali domin sauran 'yayan ne tsaye kan Mahaifiyar su suna k'okarin ceto rayuwar ta. ********* Shamsiyya ce cikin kuryan d'akinsa tunda ta tashi da safe take jin ciwon ciki tayi shiru bata fada ba,sai da taga wani abu me kama da jini yana zubawa daga gabanta shine fa ta kira mahaifiyar ta ta fada mata, Uwa ta kira Lantana hankali a tashe! Tasan haihuwa CE,nan suka fara bata taimako ganin yadda take yunk'urin da alama haihuwar a kusa take. ******** Tashin hankalin da iyalin Waziri suka shiga ba a fad'ar sa, ganin yadda hallitun ubansu ya sauya ya munana ya jirkita sai kace ba mutum ba, tuni wasu suka fara kuka mussaman mata, da k'yar aka samu Kattime ta dawo hayyacin ta, ta kallin mijinata da ya koma kamar tsumma! Lokaci guda ubangiji ya tagayarashi tace." Alhamdullahi Allah na gode maka da ya mayar da kai haka hak'ika mutuwar ita tafi amfani da RAYUWAR ka, ka cucu ni ka cuci 'yayanka saboda son zuciya irin taka, ka kashe rai Wanda bamu San adadi ba, hak'ika nayi nadamar auranka bana fatan ko a lahira ubangiji ya had'a fuskoinmu" Tana gama maganar ta fashe da kuka me cin rai! Nan fa fadawan da suka kawo shi suka dinga silalewa suna futa cike da kunya. ******** Cikin hukuncin ubangiji Shamsiyya ta haihu lafiya inda ta haifi d'anta namiji yaro lafiyyaye dashi me kama da ubansa sak!!! Kuka sosai take uwa na tayata wai yau itace zata Goya Dan shege rayuwa kenan, haka Lantana ta dafa ruwan zafi tayiwa jinjiri Wanka tas ta shirya shi cikin kaya,ta goyashi tana daure zuciyarta itama amma kukan zuciya kam kullum sai tayi shi. ****** To ranar bayan sun dawo daga massalaci Shatima ya kira wayar mama ya Sanar mata halin da ake ciki, murna sosai Mama tayi ta dinga godewa Allah da ya kawo wa yaron ta sauk'i cikin lokaci kankani lallai duk Wanda ya dogara ga Allah yayi dace duniya da lahira Me girma governor kuwa yana ganin kamar yafi kowa farin ciki, don haka nan take yasa mutanan sa afara shirye-shiryen nad'i domin a cewarsa me Martaba Sarki!Almansur na biyu na dawowa za'a fara shagalin nadin sarauta, aikuwa gari ya d'auka da murna,dama labarin halin da Waziri yake ciki ya karad'e ko ina cike da waje harda wajan gari ma kowa yaji wasu na turr dashi wasu kuma na tausaya masa halin da yake ciki. Yau Litinin Wanda yayi dai-dai da sati uku kenan da tafiyar su saudi'a a yau din ne kuma suke d'aura niyyar dawowa gida cikin farin ciki da samun nasara, Balaraba tayi wani fresh da ita kyallin ciki duk ya bayyana a tattare da ita, ta kara cika da kwarjini sosai duk Wanda yasan mace me ciki ya kalleta a lokacin sai ya gane, shiko uban tafiyar tamkar ba Wanda yaje jinya ba ya had'a wata kiba fatarshi tayi sumul-sumul sai shek'i take,shida Balaraba har nasara Wanda yafi wani kyau da gogewa ****** Can gida kuwa ya hautsine da shagali gami da kid'e-kid'e da busa ko INA ka kalla jama'a ne suke kai kawo kowa yana cike da farin cikin dawowar me Martaba cikin aminci da koshin lafiya. Halisa da Azima sai kintse-kintse sukeyi kowacce tana k'okarin tayi abunda zata fi 'yar uwarta dashi, Azima kokari kawai take tana ji ajikinta kamar asirinta zai tuno tunda dai gashi Waziri yana cikin wani hali shine dama ya yaudare ta, gashi yanzu tana mutukar son auranta addu'a kawai take Allah ya rufa mata asiri. Fili jirgi a cike da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108