Skip to content

Chapter 66

Chapter 66

Gimbiya Balaraba Book One Complete Hausa Novel 1,274 words 0 views Progress saved
Download Book

_Wannan yana da banbamci domin kuwa killatacce ne duk Wanda ke buk'ata se ya biyoni ta number kamar haka_ Whatsap numbar 07061553385 *Karku bari abaku labari* _*BISIMILHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿75* Cikin nutsuwa, tabi bayansa, Yana gaba tana baya zuciyarta sai wani d'ar-d'ar take, me Martaba yana bala'in yi mata kwarjini don haka suna had'a idoshi ta sunkuyar da kanta a k'asa,gami da zubewa k'asan k'afafun Mama Fulani tana gaishe shi. Cikin sakin fuska ya amsa yace"Sannu kinji ya k'okari,ya mukaji da rashin Moddibo kuma"? Cikin rawar murya tace"Alhamdulilahi" "Allah ya jik'an Yusuf" Me Martaba ya fad'a,da amin suka amsa. Sannan yayi shiru na minti biyu kana ya cigaba da cewa"Wato abunda yasa na kira ki, nan gurin shine, ina neman alfarma guda a gurin ki ina fatan zaki bani wannan alfarmar" A nutse tace"Ai babu abunda zaku nema a gurina in kasa yi muku shi,Allah ya taimake ka" Me martaba yaji dad'in lafazinta yace"Alhamdulilahi,Allah yayi miki albarka, ina son zan maye miki guribin Yusuf da Almustafa Sarki!kenan, ma'ana zan d'aura muku aure insha Allah rana ita yau, ina fatan ban shiga hakkin ki ba, ko idan ba kya sonsa ki fad'a kar ki rufe min,tamkar "yar cikina kike,domin bazan yi miki dole ba" Cikin fad'uwar gaba, tace"Duk rin hukuncin da ka yanke a kaina, bani da ja akai domin ka isa dani,saboda haka na amince da zab'in ka" Albarka me Martaba ya sa mata sosai sannan ya bata umarnin tafiya. Balaraba ta mik'e a nutse ta bar gurin kai tsaye d'akin da ta futo ta koma. Tana shiga ta zube kan daddumar da tayi sallah ta fara wani sabon kuka,tana tausayawa kanta,sam takasa cire Moddibo daga zuciyarta, yaya zatayi ta had'a soyyayarsa da ta kowa sam bata jin soyyayar Almustafa cikin zuciyarta,tana ganin bata da babban masoyi. Kamar Moddibo, kuka take sosai,da sosai. Ganin kukan da yayar tasu take ne yak'i k'arewa yasa Sadiya ta kama hannun Usuman suka futa suna kuka suma. Babu kowa a falo sai Sarki!dake kwance kan Sofa, yak'i komawa fada, saboda yana buk'atar hutu, sosai kwana biyu sam baya samun ishashan bacci,Moddibo na yawan fad'o masa a rai, mussaman idan ya tuna lokacin da ya had'a hannusa dana Balaraba yana fad'in, d'an uwana ga amana ta nan,wannan magana da Moddibo yayi masa tana tsaye a cikin ransa, Hangosu yayi sun futo suna share hawaye ya mik'e da sauri yana ware lumsassun idonsa, Sadiya ta k'araso kusa dashi cikin rawar murya tace"Magajin Sarki! ga yayarmu can tana kuka, kuma tak'i taci abunci tun safe take kuka, mu kam munci abunci mun k'oshi abunmu" Jin da yayi Sadiya tace"Tana kuka sai yayi tunanin maganar da me Martaba ya fad'a matane ta sanya ta kuka, wato tanaso ta nuna masa cewar bata sonsa,amma takasa fad'a gaban me Martaba, ranshi yaji ya b'aci kad'an, cikin zuciyarsa yace "Babu ruwuna da ko tana so ko bata so,insha Allah sai na cikawa d'an uwana burinshi. Mik'ewa yayi ya rik'e hannunwan su suka nufi d'akin da take ciki, tabbas bazai lamunci zama da yunwa ba Tana kwance kan daddumar har yanzu kuka take ya k'ofar d'akin ya shiga,da sallama ciki-ciki, sam batasan da shigowarsa ba, yazo ya tsaya kanta,yana k'are mata kallo, inuwar mutum dogo ta gani akanta, tayi sauri d'ago da fuskarta wacce taji jage-jage da hawaye, had'a ido sukayi, yana mata wani kallon kurulla. Da sauri ta mike zaune tana goge fuskarta da k'asan hijab dinta,hararasa take k'asa-k'asa ta takure jikinta cikin hijab tana sauke ajiyar zuciya. Yafi minti biyar a tsaye a kanta yana nazarinta, gyaran Murya yayi ya kira sunanta cikin yanayin muryar shi, sunkuyar da kai tayi bata amsa ba. Tsugunawa yayi kusa da ita ya d'ora gwiwarsa k'asa yana k'okarin d'ago fuskarta,da tafukan hannayensa,a zabure ta matsa gefe tana watsa masa harara,k'asa-k'asa, fuskarsa ya had'e sosai yace"Kukan me kike yi"? Shiru tayi masa gabanta na faduwa saboda kusancinsu da shi yayi tsanini Wanda har hucin futar nuffashinsa tanaji ga k'amshin turaransa duk ya baibayeta. Kaurara murya yayi yace"Wannan shine magana take da ta karshe mutuk'ar zan dunga yi miki magana kina raina min hankali, kinajin abunda nake cewa kinyi shiru ko"? D'ago kanta tayi tana kallansa,cikin dauriya tace"Me ya dame ka da kukana"? "Saboda ke amana ta ce" Cikin mamaki ta kalleshi jin abunda ya fad'a. "Anyway,nasan abunda yasa kike kuka saboda ance dake ki aure ni ne,shine dalili, ko"? Yafad'a cikin sigar tambaya. Shiru tayi tana takure jikinta,so take ya tashi daga kusa da ita duk a takure take. Wani murmushi yayi yana d'an girgiza kansa cikin damuwa abubuwan da suka da meshi yace" Tabbas kinyi rashin masoyi, mu kuma munyi rashin d'an uwa managarci hak'ika Moddibo ya taka muhimiyar rawa a rayuwar ki, tabbas duk abunda ya tafi ya bari a doran duniyar nan dole in d'ora daga inda ya tsaya, ko da me Martaba be yanke wannan hukuncin ba, ni ina da wannan kudirin na auranki araina saboda wasiyar da d'an uwana ya tafi da ita" Nuffashi ya sauke yayi shiru,gami da tsura mata ido, kana ya cigaba da cewa, mutuk'ar kikaga ba'ayi wannan auran ba,to sai dai in ke kika bujere,wa buk'atar mu,saboda haka, inason ki kwantar da hankalin ki a kaina ni ba,bak'on zafi bane duk irin zaman da kike so muyi ni dake haka zamuyi" Tsitt!! D'akin yayi bakajin komai sai k'arar AC da sautin nuffashinsu, da k'yar ta d'ago kanta tana kallonsa,bata tab'a tsammanin ya iya kyawawan lafazai irin wannan, wani irin kwarjini yayi mata,wanda yasa tayi saurin kauda da kanta daga kansa, muryarta na rawa tace" Ka matsa daga kusa dani" Girgiza kai yayi kawai yana sakin murmushi,yace"Sadiya tace"tun safe baki ci abunci ba,hakane"? D'akin take bi da kallo tana neman su Sadiya,basa nan, gabanta ya fad'i ta zaci suna d'akin a tunaninta ko Sarki!yayi niyyar yi mata wani abu ganinsu zai sa ya fasa. [17/08, 15:30] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 ^^^^^^^^^^^^^^^^^^ _*GIMBIYA BALARABA*_ ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ 👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻 _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIYAR*_ ```Nana Khadija``` ```Yaro Da kud'i``` ```Gimbiya Balaraba``` _*ZAMANI WRITERS*_ _*ASSOCIATION🤝🏻*_ ________________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur readers*_ ________________________ _*DIDEGATED*_ _*TO*_ ```RAHAMA ALIYU``` _*BISMILLAHI-RAHAMANI-RAHIM*_ *🅿76* Ganin yadda take rarraba ido yasa ya mik'e tsaye cikin nutsuwa yace"Ki futo falo kici abunci,ki sake da mutane, sannan ki cigaba da walwalarki,wannan zaman da kike cikin d'aki ke kad'ai duk bashi ne mafuta ba,a gareki, ita rayuwa ta duniyanan bata tabbata, ki sanya tawakkali a cikin zuciyarki, kisa a zuciyar ki cewa inda Moddibo ya tafi kema zaki tafi,domin can d'in shine tabbas,a garemu" Yana gama maganar sa ya futa daga d'akin,a nutse. Balaraba tayi mamakinsa mutuk'a sam bata tab'a tunanin mutum ne shi mai sauk'in kai haka ba,ga Ilimi da ikilashi,ta lura mutuwar Moddibo batasa ya furgice ba,duk da shak'uwarsu amma yana cikin nutsuwarshi, haka ake son mutum me tawakkali. Wannan Nasiha da Sarki!yayi mata ta k'arfafa mata jiki sosai tanaji a zuciyarta cewa itama hakane idon lokacinta yayi dole tatafi babu tsumi babu dabara. Allah kasa mu dace. A nutse ta furo falo, taga su Sadiya na zaune kan wata k'atuwar dadduma suna cin "yayan itatuwa shi kuma yana kwance kan Sofa kamar d'azu idansa a lumshe,da alama bacci yake ji, Babu kuzari a jikinta ta nufi wani keb'antaccan guri wanda aka tana da domin cin abunci ta

Table of Contents

Chapters

108 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108